Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar
Published: 6th, March 2025 GMT
Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia.
Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar.
Kafin haka dai masu fama da wannan cutar thalassemia 438 ne suka shigar da kara kan mutane 17 na gwamnatin Amurka wadanda suke da hannu wajen aiwatar da takunkuman tattalin arziki na magunguna a Amurka.
Kotun ta yanke hukuncin tarar ne a kan wadanda Jami’an gwamnatin Amurka, wadanda suka hada da wadanda cutar ta gurgunta, ko ta yi masu wata illa. Ko barna ga masu mafa da cutar. Magungunar cutar Thalassemia masu kyau dai ana samunsu a kasar Amurka ne. Rashin samunsu ya tilastawa wasu amfani da jabun magani daga wasu kasashen wanda hakan ya kara yawan kudaden da suke kashewa cutar.. Takunkuman tattalin arzikin sun gurgunta ko sun jawo mutuwar mutane da dama a kasar Iran don haka wannan tarar ta dace da irin wannan laifin
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnatin Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Soke Tsaftar Muhalli A Watan Afrilu Saboda Jarabawar JAMB
Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar.
Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp