2025-03-06@13:10:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1394
«gwamnatin Amurka»:
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
Daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Jihar Binuwai sun kubuta. Daliban sun lubauta ne bayan shafe kwanaki takwas a hannun ’yan ta’addan.
Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya. An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati. Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon...
Kamfanin dillancin Labarun “Resuters” ya nakalto cewa jami’an tsaro sun killace gidan mataimakin shugaban kasa da wasu manyan jami’an soja da fararen hula. Baya ga mataimakin shugaban kasa Riek Machar da sojoji su ka yi wa daurin talala a cikin gidansa, an kuma kama mataimakin hafsan hafsoshin sojan kasar Jamar Gabriel Doup Lam, sai kuma ministan man fetur Pout Kang Chol, haka nan kuma iyalansa da masu gadinsa. Har ila yau a jiya Laraba an ga jami’an tsaro masu yawa sun killace ofishin mataimakin shugaban kasar, sai dai kuma wata majiyar ta ce, an gan shi ya isa wajen aikin nashi da safiyar jiya Laraba. Wadannan matakan na tsaro dai sun biyo bayan fada mai tsanani da aka yi ne ...
Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya. Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida. Tun bayan da aka yi cacar baki a...
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba. Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40. (Telegraph – subscription required) West Ham na kokarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka. (Guardian) Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a Burnley, James Trafford mai shekara 22 ko kuma Joan Garcia mai shekara 23 daga Sifaniya, domin maye gurbin Andre Onana mai shekara 28 na Kamaru. (Teamtalk) Real Madrid na son ɗan wasan Liverpool mai shekara 25 daga Faransa, Ibrahima Konate. (Mail – subscription required) Real ta kuma nuna matsuwa kan ɗan wasan Bournemouth mai shekara 19 daga Sifaniya, Dean Huijsen, wanda cikin yarjejeniyarsa...
Jami’ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih – Mahaifar shugaba Zelensky. Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine. Wannan hari na zuwa ne sa’o’i bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta daina musayar bayanan sirri da Ukraine — wanda haka zai kasance ƙalubale matuƙa ga Ukraine wajen iya daƙile hare-haren Rasha. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce masu aikin sa kai daga wata ƙungiyar bayar da agaji daga Amurka da Birtaniya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya. Hakazalika, an kai wasu hare-haren...
Shugaban kungiyar marubuta wasanni ta kasa SWAN, Kwamared Isaiah Benjamin, ya bukaci sabon kwamitin hadin gwiwar SWAN da aka kaddamar da su farfado da kungiyar ta hanyar jawo masu zuba jari don tallafa wa marubutan wasanni a fadin kasar nan. Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin kwamred Isaiah Benjamin ya jaddada mahimmancin karfafa kudi ga ‘yan jaridun wasanni, yana mai baiwa kwamitin ‘yancin gudanar da aiki yadda ya kamata. “Aikin da ke gaba yana da girma, amma ina da yakinin iya karfin ku na karfafa tattalin arzikin marubutan wasanni a Najeriya ta hanyar hadin kai. Kuna da cikakken goyon bayanmu, ”in ji shi. Ya bayyana cewa zaben ‘yan kwamitin wanda shugaban kungiyar SWAN na jihar Nasarawa,...
A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba. Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta...
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo. A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron karin haske kan ayyukan gudanar da aiki, nasarori, kalubale, da hasashen da za a yi a nan gaba, inda ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu wajen yaki da rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata. Ya yi nuni da cewa al’amuran satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami, da kuma rikicin kabilanci ya ragu matuka saboda jajircewar sojojin. A...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar. Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni. “Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya...
Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki. Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi. ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su. Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki. Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara. Ya ce a lokacin azumi da ake tsananin zafi a hankali ruwan jiki yana raguwa. A cewarsa karuwar cin ‘ya’yan itatuwa daban-daban zai yi matukar amfani ga musulmi mai azumi. Farfesa Afolabi ya bayyana cewa a lokacin azumin watan Ramadan musulmi sun kaurace wa abinci da abin sha, tare da hana jikinsu cin abinci da suka saba. Ya ba da shawarar a kara amfani...
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka haɗe a ƙarƙashin Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS. Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin ƙungiyar da ƙasashen AES, domin har yanzu ana ci gaba da hulɗa tsakanin al’ummomin yankin. Hakazalika, ECOWAS ta bayyana cewa ƙofarta a bude ta ke ga ƙasashen idan har sun shirya komawa cikin ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe. Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin jihar kan rashin amincewa da rawar da gwamnatin tarayya ta taka, wanda hakan ya sanya ake yaudarar jama’a wajen ganin cewa tallafin na jiha ne kawai. Jam’iyyar adawa ta ba da shawarar cewa yin shiru ya sa ayar tambaya game da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kayayyakin agaji. Ta kuma yi zargin cewa sukar da Gwamnan ya yi a...
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara. Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman Ahmad Tudu. A cewar sanarwar, Haidar ya gaji Ahmad Liman, wanda ya yi ritaya a ranar 28 ga Fabrairu, 2025. Haidar, wanda ya kammala karatunsa na kimiyyar siyasa a shekarar 1989 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, an nada shi Babban Sakatare a shekarar 2012, kuma ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi gwamnati da dai sauransu. Gwamna Lawal ya bayyana...
An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna. Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe. Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata. Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024. An kama korarren jami’in tsaro da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda. Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari. Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur...
Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hegseth yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake hira da shirin labarai na tashar talabijin ta Foxnews na Amurka. Seketarin tsaron tsaron ya kara da cewa dok wanda yake son zaman lafiya to ya shiryawa yaki. Don haka kasar Amurka, inji Hegseth dole ta tabbatar da tana da sojojin masu karfi da makamai masu inganci don shiriwa ko ta kwana, saboda...
Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya. Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika...
Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye. Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya aiki Adam Boehler mutumin da yake wakiltansa a al-amuran fursinonin Amurka a waje, zuwa kasashen yankin kudancin Asiya don tattauna batun Amurkawa da suke hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza. Leavitt ta kara da cewa Amurkawa sun cancanci a shiga tattaunawa ko kuma a bi duk hanyoyin da suka dace don ganin, an kubutar da Amurka wadanda suka shiga hanun makiyansu a ko ina suke...

Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar
Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia. Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar. Kafin haka dai masu fama da...
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa. Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na...
Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Wannan mataki ya zo ne saboda yadda ayyukan hukumar ke jan hankali, inda sau da yawa ake samun saɓani tsakaninta da wasu. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala ne, ya bayyana cewa an yi wannan dokar gyara ne don daidaita harkokin ɗaukar fina-finai da kare addini da al’adu. Ya ce daga yanzu...
A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14. Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban kasar Sin, musamman ma a fannin sa kaimi ga inganta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da dunkulewar masana’antu, da sa kaimi ga inganta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, da shigewa gaba wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na ci gaban kasar, da kuma ba da misali a fannin samar da wadata ga jama’a baki daya. (Safiyah Ma) Daga...
Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan. Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka: Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata 1. Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar abin da zai rage lada ko karya azumi. 2. Sallah: Ya fi dacewa a dage da Sallar Taraweeh da Tahajjud, tare da yin sallolin farilla a cikin jam’i da nafiloli da ake yi kafin ko bayan su. 3....
Hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila (Shin Bet) ta amince da gazawarta wajen hana harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su. Ya ce, da hukumar ta Shin Bet ta yi wani abu daban a cikin shekarun da suka gabata kafin harin da kuma a daren da aka kai harin… da an kaucewa hakan. “A matsayina na shugaban hukumar, zan...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York. Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.” Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda ba na son rai. A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta kan kaddamar da kiraye-kirayen bayar da tallafi don tara kudade da biyan Diya, ta yadda za a saki fursunonin da ake yanke musu hukunci bisa aikata laifukan da ba da gangan ba. Taron dai ya hada jami’ai da masu ba da agaji a Tehran babban birnin kasar da kuma garuruwa daban-daban na kasar duk shekara. Diya wani hakki ne da ake biya ga wanda aka...
Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi. Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5. “Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da...
Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi A ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba. Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci. Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu,...
Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar. Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.” Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta. Martanin Akpabio Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa. A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata. Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru. Abin da Sanata Natasha...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani matashi Safiyanu Dalhatu, mai shekara 20, kan zargin kashe mahaifiyarsa har lahira a unguwar Abujan Kwata. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ’yan Kwamitin Tsaro na Unguwar ne suka kai rahoton lamarin ofishin rundunar na ‘A’ Division da ke Bauchi. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau Bincike ya nuna cewar mahaifiyar matashin, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta samu karaya a hannayenta biyu sakamakon dukan da ya mata bayan sun samu saɓani. Bayan samun rahoto, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Abdullahi Muazu, sun garzaya wajen da lamarin ya faru. Sun kai Salama Asibitin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na siyasa ya samo asali ne daga yanayi da ya fi ƙarfinsu gaba ɗaya. “Gaskiya ni na yi imanin cewa ni da Kwankwaso ba mu da wata matsala ta zama tare a ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya. A duk abubuwan da suka faru, da ni da shi duk babu mai laifi,” inji shi. Da yake tsokaci kan lokacin da suka...
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne. Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ya yi watsi da bukatar HKI na kwance damarar dakarun kungiyan a matsayin sharadi na ci gaba da aiwatar da yarjeniyar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025. Kungiyar ta kara da cewa, kwance damara dakarun kungiyar jar layi ne a wajenta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI tana bukatar ta raba kungiyar da makamanta, kafin ta ci gaba da aiwatar da yarjeniyar ta watan Jeneru. Wannan bukatar dai ta sa tababa a cikin yiyuwar tsagaita wuta tsakanin HKI da Hamas ya dore. Yarjeniya ta yanzu dai, wacce ta faraaiki a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025, kuma an tsara shi bisa marhaloli 3. Daga...
“A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.” Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai...
Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza. Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba. Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci...
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700. EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa. ’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan...
Tunin Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya umarci babban baturen ɗansanda a C Division da ya jagoranci tawaga ta musamman da za su gudanar da bincike kan lamarin a tsanake. A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, yunkurinsu a halin yanzu ya kai ga kama Fatima Mohammed, kishiya ga mamaciyar wacce a halin yanzu take tsare a hannunsu. “Bincike na farko ya nuna cewa, akwai zargin Fatima Mohammed na da hannu a mutuwar Hajara. A yayin da ake yi mata tambayoyi, an ce ta amince ta shaƙe ta har lahira, sannan ta yi yunƙurin ɓoye laifin ta hanyar zuba mata tafasasshen ruwa tare da ƙona jikinta da buhun da ke narkewa,” in ji CSP Wakil A...
’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe. An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin. Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa. Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba...
Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. “Ma’aikatan jihar za su je aiki karfe 9 na safe sannan su tashi da karfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis maimakon zuwa karfe 5 da ake kai wa a baya, sai ranar Juma’a ma’aikatan za su je aiki da karfe 9 na safe su tashi da karfe 1 na rana kamar yadda aka saba”. Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, an yi wannan karimci ne da nufin samarwa ma’aikatan...
Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira. Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta riƙa laƙume kaya da kadarori kafin ’yan kwana-kwana su iso wurin. Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa...
Rundunar ‘yansanda ta Durumi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da tattara bayanai, sannan ta mika gawar zuwa Asibitin kasa domin ci gaba da gudanar da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fa’iza Muhammad wacce aka fi sani da Fa’iza Badawa, daya ce daga cikin mawakan Kannwood. Ita ta yi wakar fim din Oga Abuja, daya daga cikin finafinan suka yi tashe, ya kuma fito da basirar mawakiyar. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu Kasancewar ta yi aure, mutane sun ɗauka ta daina harkar waƙa baki ɗaya. Sai a hirarta da wakilinmu Ibrahim Musa Giginyu, Fa’iza ta ce ba haka ba ne. Yaushe kika yi aure? Na yi aure ne a ranar 8 watan Afrilun shekar 2017, kuma ina zaune lafiya da mijina da kuma haihuwa daay da Allah Ya bamu, kuma aure ne na so ada kauna da kuma kyakkyawar kulawa. Kuma yana...
Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba. A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za...
A cewar rahoton, za a samar tare da aiwatar da wani tsari mai wa’adin shekaru 3, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa bangaren ilimi. Haka kuma, kasar za ta inganta raya ilimin dole mai inganci kuma bisa daidaito, tare da kara bayar da damar shiga makarantun sakandare. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta inganta hada ilimin sana’o’i da ilimi na gama gari, tare da hada hannu da masana’antu da makarantu ta yadda ilimin sana’o’i zai kara dacewa da tsarin ilimi. Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin za ta aiwatar da gyare-gyare a makarantun gaba da sakandare cikin rukunoni, tare da daukar matakai masu kwari wajen fadada ingancin karatu da gaggauta samar da jami’o’i da bangarorin...
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ina mana lale barka da zuwan masoyi watan Ramadan. Da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan alheran da ke cikinsa kuma Ya sa mu zama daga cikin ’yantattun bayinsa, amin. Ramadan: Alherai goma ga Ma’aurata. 1. Gyaran aure: Ramadan lokaci ne na ibada da kyautata ibada. Aure da zamantakewar aure yana ɗaya daga cikin manyan ibadojin Addinin Musulunci. A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Yace, Aure rabin Addini ne. Don haka kamar yadda muke dagewa wajen ayyukan addini da gyaran alakar mu da Allah, to ya kamata ma’aurata suyi amfani...
Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila. Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban. Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da shirin na...
Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”. Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran. Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana...
Wasa ya koma kuka bayan da wani mai wasan barkwanci manne laɓɓansa ba sa buɗewa bayan da ya shafa musu gam din sufa-gilu a yayin da yake yin bidiyo kai-tsaye domin ƙayatar da masu bibiyarsa. Mutumin ya shafa gilu ne, inda ya manne laɓɓansa, wanda cikin dakika kaɗan, mannewar ta kama fatar laɓɓan kamar yadda ya so, inda hakan ya sa yabar laɓɓansa a rufe sosai. Fasinjoji 16 sun ƙone ƙurmus a Ogun DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana A zamanin da ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani, mutane sukan yi iyakacin ƙoƙarinsu don samun mabiya da sakonsu zai kai gare su a intanet. Raye-rayen zuwa abubuwan barkwanci, suna yin tasiri a shafukan sada...
Aƙalla fasinjoji 16 suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Talata a Jihar Ogun. Aminiya ta ruwaito cewa hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya kacal ya afku ne a gidan Buhari da ke kan titin Abeokuta zuwa Shagamu. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’ An bayyana cewa, hatsarin dai ya rutsa da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba KJA 949 YJ, da misalin ƙarfe 1:00 na rana. Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar. Ta ce ba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba. Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. Domin sauke shirin, latsa nan
A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta kara dora muhimmanci kan matakan shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, kana take ta karfafa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi, da zurfafa hadin kai da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Amurka, wajen shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da sinadaran da ake samar da shi daga gare su, inda kuma aka cimma manyan...
“Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.” Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma. Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa. Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar...
A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje. Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS). Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...

A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja. Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar. Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi. Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda...
A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga a dama da ita, kuma za ta kasance mai bayar da shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Da yake tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, Lou ya ce, daukar matakin da Amurka ta yi bisa radin kai ya saba wa ka’idojin kungiyar...
Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin, take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
Iran Tayi Tir Da Shirin Shugaban Amurka Na Sake Tsugunar Da Al’ummar Gaza Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu wurare, kuma ta biyyana shi a matsayin ci gaba da siyasar kisan kare dangi kan alumma falasdinu, Shugaban na Amurka Donald trump yayi wannan bayanin ne a taron manema labarai da yayi a fadar white hause da fira ministan isra’ila binjamin natanyaho a watan jiya, inda ya nuna aniyarsa ta kwashe alumma yankin gasa zuwa wasu kasashen larabawa. Tare da gina wajen shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa a wajen. Shuwagabannin kasashen laraba wa da na musulmi sun jadda mastayinsu na amincewa da yancin falasdinawa tare...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin. Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi...
Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green Horizon, Farfesa Muhammed Sabiu (SAN) ne ya jagoranci taron wanda shirin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta shirya. Tun da farko a jawabinsa na bude taron, Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Sarkin Fulani Hamceta Alhaji Aminu Lawal Bagiwa ya wakilta, ya ja hankalin mahalarta da su tsaya domin sanin abin da za a ilmantar da su kasancewarsu na shugabannin al’umma kuma na farko da ake kawo...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis. Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa. Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa, Abuja, a yau. Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin kuɗin wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin daɗi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. “Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai wata takarda ta kuɗi ba...
Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu. “Farawa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe kuma su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis, raguwar awanni biyu daga tsohon lokacin rufewa na karfe 5:00 na yamma. A ranakun Juma’a kuwa, ma’aikata za su fara aiki da karfe 9:00 na safe su kuma tashi da karfe 1:00 na rana, kamar yadda aka saba.” A...
Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa sojojin HKI sun sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’. Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba, a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa; “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83. Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.” Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara...
Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin. Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida wa kotun cewa mutumin ya yi yunƙurin aika-aikan ne bisa zargin matarsa da kama kuruwar ɗansu da ya jima yana fama da rashin lafiya. Magidancin da ke zaune a ƙauyen Gawo da iyalin nasa ya musanta tuhumar da ake masa, don haka, Alƙali Nura Ahmad ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari. Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a...
Aikin titin Abuja zuwa Kano dai yana da matuƙar muhimmanci ga tafiye-tafiye da kasuwanci a Arewacin Najeriya, kuma jama’a sun daɗe suna ƙorafi kan jinkirin kammala shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi wannan kiran ne bayan wata maganan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya yi dangane da kasar Iran. Labarin ya kara da cewa, Hakan Fiddan ya bayyana cewa shirye-shiryen JMI a kasar Siriya masu rusa kasar ne, kafin juyin mulkin da Turkiyan ta dauki nauyinsa a baya-bayan nan a kasar Siriya. Ya ce: Fidan yana magana kan gagarumin taron Jana’izar Shahid Sayyid Hassan...
Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC. Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.
A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC + za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna cewa kungiyar OPEC + bata kara yawan man da take haka ba na lokaci mai tsawo, amma a halin yanzu zata kara kamar yadda aka sanar. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana rage ganga miliyon 5.85 wanda kuma shi ne kashi 5.7% na yawan man da ake haka a duniya, wannan kuma ya yi dai dai da shawarar da OPEC + suka dauka tun shekara...

Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD Ta Ce Sauye-Sauyen Da Ke Faruwa A Amurka Zai Shafi Al-Amura Da Dama A Majalisar
Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen duniya. Volker Turk ya ce al-amura da suka shafi nuna wariya ne, mai yuwa su zama akasin haka nan gaba, bayan wadannan sauye sauye sun fara aiki. Wannan dai shi ne jawabi mai muhimmancin da wani jami'an MDD ya gabatar dangane da abubuwan da ke faruwa a sabuwar gwamnatin Amurka. Turk ya kuma...
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar. ’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne. Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su. Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok...
Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari. Rahotanni sun bayyana cewa faɗuwar tankar man ke da wuya, jami’an tsaron suka isa wurin, inda suka killace wurin domin hana mutane kaiwa inda man yake. Daga nan ɗauke tankar man da babbar motar ɗauko, aka mayar wata motar sannan aka tafi da ita. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin (CPPCC) da za a fara ranar 4 ga watan Maris, da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da za a fara ranar 5 ga watan Maris, su kasance manyan taruka biyu na kasar Sin inda ake gangamin siyasa domin nazartar baya da kuma hangen gaba. Wadannan hukumomi biyu suna karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda ke karkashin jagorancin babban sakataren Xi Jinping. Kwamitin CPPCC na kasa, mai mambobi 2,169, yana aiki ne a matsayin babbar hukumar da ke tafiyar da tsarin dunkulewar sassan kasar ta fuskar siyasa, wanda ke hada kungiyoyin zamantakewa daban daban mashawarta jam’iyyar. Ita kuma, majalisar NPC mai wakilai 2,977, tana aiki ne a...