Leadership News Hausa:
2025-03-06@13:48:44 GMT

Lamine Yamal Ya Amince Da Sabon Kwantiragi A Barcelona

Published: 6th, March 2025 GMT

Lamine Yamal Ya Amince Da Sabon Kwantiragi A Barcelona

Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona.

Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba.

Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa.

Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Barcelona Kwantaragi Yamal

এছাড়াও পড়ুন:

Kasafin Kudin Bana Zai Samarda Tsarin Tattalin Arziki Da Cigaban Ƙasa: Ministan Labarai

 

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.

 

Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa, Abuja, a yau.

 

Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin kuɗin wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin daɗi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

 

“Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai wata takarda ta kuɗi ba ce; yana nuna tsari mai ƙarfi na daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa. Wannan kasafin ya maida hankali kan harkokin tsaro da ababen more rayuwa da ilimi da lafiya da ma’adinai da noma da wasu sassa masu matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa.”

 

“Wannan shekara ta 2025, shekara ce ta tabbatar da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar, domin a fara jin ɗadin su a zahiri. Tuni muna gani a fili cewa farashin kayan abinci yana raguwa a hankali, wanda ke kawo sauƙi ga ‘yan ƙasa,” in ji shi.

 

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata, tare da nuna gaskiya da riƙon amana wajen cimma burin shirin ”

 

“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen aiwatar da wannan kasafin kuɗi domin cimma cikakken tasirinsa a rayuwar al’ummar mu. Don haka, ina kira ga duk ‘yan ƙasa su mara wa waɗannan ƙoƙari baya, domin mu gina Najeriya,” in ji shi.

 

Ministan ya yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa jajircewarsu wajen kawo rahotanni kan taron, yana jaddada muhimmancinsu wajen yaɗa sahihan labarai da suka dace, ba tare da son rai ba, tare da mai da hankali kan ci gaban ƙasa.

 

Ya nanata cewa kafafen yaɗa labarai suna ba da gudunmuwa wajen tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na samun ingantattun bayanai kan manyan tsare-tsaren sauyi da gwamnati ke aiwatarwa.

 

Mohammed Idris ya bayyana cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar tattaunawa bisa sani, fahimtar juna, da haɗin gwiwa don cigaban ƙasa. Saboda haka, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da kiyaye ƙa’idodin daidaito, alhaki, da ƙwarewa a cikin rahotanninsu.

 

“A wannan zamani da labaran ƙarya da son rai ke iya rinjayar tunanin jama’a cikin sauƙi, sadaukarwarku ga gaskiya da adalci ya fi zama mai muhimmanci fiye da da. Dole ne mu yi aiki tare don tabbatar da cewa bayanan da ke tsara ra’ayoyin jama’a sun dace da ainihin gaskiyar yadda ake tafiyar da mulki, ba tare da son rai ko ƙayatarwa maras tushe ba,” in ji shi.

 

Taron Minista karo na uku ya kuma samu halartar Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ministan kasa, Sanata John Owan Enoh.

 

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Liverpool na farautar Kerkez, Real Madrid na son Konate
  • Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikata.
  • An Sanya Ranar Sake Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Ribas
  • Hukumar Leken Asirin Isra’ila Ta Amince Da Gazawarta Wajen Hana Harin Hamas
  • Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed Musa Damar Taka Leda A Super Eagles
  • ’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe
  • Kremlin: Putin Ya Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Amurka
  • Kasafin Kuɗin 2025 Taswira Ce Ta ƙarfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai
  • Kasafin Kudin Bana Zai Samarda Tsarin Tattalin Arziki Da Cigaban Ƙasa: Ministan Labarai