2025-03-06@13:53:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 442

«Kwantaragi»:

    Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40. (Telegraph – subscription required)   West Ham na kokarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka. (Guardian)   Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a...
    Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo.   A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron...
    Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki.   Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa...
    An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki.   Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara.   Ya ce...
      Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara.   Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman...
    Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran...
    Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye. Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
    Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai  har...
    Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar  Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan...
    Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa. A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin...
    Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan...
    “A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna...
    Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira. Mijina bai hana ni...
    A cewar rahoton, za a samar tare da aiwatar da wani tsari mai wa’adin shekaru 3, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa bangaren ilimi. Haka kuma, kasar za ta inganta raya ilimin dole mai inganci kuma bisa daidaito, tare da kara bayar da damar shiga makarantun sakandare. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin...
    Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba. Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na...
    A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta...
    “Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”   Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green...
      Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.   Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
    Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida...
    Aikin titin Abuja zuwa Kano dai yana da matuƙar muhimmanci ga tafiye-tafiye da kasuwanci a Arewacin Najeriya, kuma jama’a sun daɗe suna ƙorafi kan jinkirin kammala shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi...
    A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za...
    Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari. Rahotanni sun bayyana...
    A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio. A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar...
    Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) za ta gudanar da taron shekara-shekara daga ranar 4 zuwa ta 10 ga Maris a nan birnin Beijing, a cewar wani kakaki a yau Litinin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin...
    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin...
    Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa  zuwa aiki. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin. A cewarsa,...
    Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa. NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C. Hakar ma’adanai: ILO ta horas...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne  na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya...
    Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qais Al-Khaz’ali ya na karyata wannan labarin, ya kuma bayyana haka ne a wani shiri a tashar talabijin ta Al-Irakiyya na kasar ta...
    Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba. Badr Abdul’adhy,  ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya. Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema...
    Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58...
    Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...