Gwamnatin Kebbi Ta Sha Alwashin Kawar Da Matsalar Abinci A Jihar
Published: 7th, March 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kaddamar da rabon kayayyakin noman rani da kayan abinci na watan Ramadan ga manoma da al’ummar jihar, inda ta umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana sayar da kayan abinci da na aikin noma.
A jawabinsa yayin kaddamar da rabon, gwamnan jihar, Kwamared Nasir Idris ya bayyana cewa, matsakaitan manoma 200,000 a fadin kananan hukumomin jihar 21 ne za su ci gajiyar shirin.
Gwamnan ya bayyana cewa, samar da kayan aikin gona ga manoma zai taimaka wajen bunkasa samar da abinci a jihar.
Ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da kuma jami’an gwamnati da ke da alhakin rabon kayayyakin, da su tabbatar da an yi adalcin wajen rabon kayayyakin.
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya ce shugaba Bola Tinubu, yana bakin kokarinsa wajen inganta harkar noma, ta hanyar karfafa gwiwar kowane bangare na al’umma da su ba da muhimmanci ga shirin noma na gwamnati.
Ya ce, rabon kayayyakin amfanin gona ga manoma a jihar Kebbi shi ne don bunkasa ayyukan noman rani a shekarar 2025, domin kara yawan kayan abinci a jihar da kuma dakile matsalar karancin abinci.
Kwamishinan noma na jihar Alhaji Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta kayan noma da kuma dakile matsalar karancin abinci.
Ya ce, matakin da gwamnati ta dauka shi ne rage wa manoma wahalhalu a lokacin noman rani tare da rage radadin da talakawa ke fuskanta a cikin watan Ramadan.
Kayayyakin da aka bayar sun hada da injinan wutar lantarki guda 3000, da famfo mai amfani da hasken rana guda 10,000, da famfunan ruwa na LPG guda 5000, da injin feshin maganin kwari guda 10,000 da dai sauransu.
Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Noman Rani rabon kayayyakin
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Jinjinawa Gwamnatin Jigawa Bisa Wanzar Da Zaman Lafiya
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar.
Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar Jigawa.
AIG Ammani ya yaba da dimbin tallafin da Gwamna Namadi ke bai wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
Ya bayyana jihar Jigawa a matsayin daya daga cikin jihohin kasar nan masu zaman lafiya.
A cewarsa, tun da ya samu mukamin AIG mai kula da shiyya ta 1, bai taba samun rahoton manyan laifuka daga rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ba, yana mai alakanta hakan da kokarin da gwamnan ke yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Hakazalika AIG ya yi amfani da damar wajen jajantawa gwamnan bisa rasuwar mahaifiyarsa da dansa, inda ya yi addu’ar Allah Yamusu rahma.
Usman Muhammad Zaria