2025-03-07@00:56:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«rabon kayayyakin»:
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kaddamar da rabon kayayyakin noman rani da kayan abinci na watan Ramadan ga manoma da al’ummar jihar, inda ta umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana sayar da kayan abinci da na aikin noma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon, gwamnan jihar, Kwamared Nasir Idris ya bayyana cewa, matsakaitan manoma 200,000 a fadin kananan hukumomin jihar 21 ne za su ci gajiyar shirin. Gwamnan ya bayyana cewa, samar da kayan aikin gona ga manoma zai taimaka wajen bunkasa samar da abinci a jihar. Ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da kuma jami’an gwamnati da ke da alhakin rabon kayayyakin, da su tabbatar da an yi adalcin wajen rabon kayayyakin....
Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo. Basaraken ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta. Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba. “Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun fara raba kayayyakin tallafi ga mutum 507 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a 2024. An gudanar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a a Ƙananan Hukumomin Kibiya da Madobi, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa kayayyakin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin. Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ne, ya wakilci gwamnan. Gwamnan, ya gode wa NEMA bisa goyon bayan da ta ke bai wa jihar, tare da yaba wa SEMA saboda jajircewarta wajen...
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
“Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.” Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya kafa, suka kama tare da kwato kayayyakin more rayuwa da aka lalata. Disu ya yaba wa mazauna yankin bisa ci gaba da ba su goyon baya, ya kuma bukace su da su kasance cikin taka tsan-tsan, yana mai jaddada cewa kare kadarorin jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyansu....
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki. Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani gida. A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....