Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa
Published: 8th, March 2025 GMT
Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar.
A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar.
“An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne laifinta babu daɗi babu ragi.”
Sanarwar ta ce da a ce Sanata Natasha ta yi aiki da dokoki da ƙa’idojin majalisar, da majalisar za ta karɓi ƙorafinta, kamar yadda doka ta tanada.
“Amma ba ta bi ƙa’ida da dokokin da suka kafa majalisar da take aiki a cikinta ba.”
Sanata Bamidele ya ce majalisar ta ɗauki matakin dakatar da Sanata Natasha ne bisa shawarar kwamitin ɗa’a, wanda ya same ta da laifin saɓa wa sashe na 6.1 da sashe na 6.2 na dokokin majalisar.
Sanarwar ta kuma zayyano wasu laifuka biyar da ta ce Sanata Natasha ta aikata, ciki har da ƙin zama a kujerar da aka sauya mata a lokacin zaman majalisar na ranar 25 ga watan Fabrairu, da yin magana ba tare da amincewar jagoran zaman majalisar ba, da yin kalaman zagi da rashin girmamawa da shugabancin majalisar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan har na tsawon wattani shida a kan laifin saɓa wa dokokin majalisar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa dakatar da Sanata Natasha majalisar da a majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
Wani babban jami’in Diblomasiyya na kasar Iran ya bada sanarwan cewa zagaye na biyu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka za’a gudanar da shi ne a kasashen Turai a ranar 19 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin waje na JMI kan al-amuran da suka shafi siysa Majid Takht-Ravabchi yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake gabatarwa Majalisar dokokin kasar Iran rahoto kan taron tawagar Amurka da kuma JMI a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Jami’in diblomasiyyar ya kara da cewa, a tattaunawar da ba kai tsaye ba tsakanin kasashen biyu a ranar Asabar da ta gabata yayin kokarin gano, wuri guda wanda zasu iya tsayawa a kansa don gina tattaunawar a kansa. Takht-Ravanchi ya nakalto tawagar gwamnatin Amurka na cewa da gaske suke a tattaunawar, kuma basa neman yaki da kasar Iran, banda haka a shirye suke su saurari korafe korafe gwamnatin JMI. A ranar Asabar da ta gabace ministan harkokin wajen kasar Amurka da wakilin kasar Amurka a harkokin gabas ta tsakiya Steve Witkoff suka gudanar da zagaye na farko a tsakanin kasashen biyu a birnin Mascat na kasar Omman. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kasar Lebanon ta nakalto shafin yanar gizo na larabarai na Axion na fadar cewa taro nag aba zai kasance a birni Roma na kasar Italiya.