Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai
Published: 9th, March 2025 GMT
Idan ana maganar masana’antu a Arewacin Nijeriya a shekarun baya a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Bauchi da sauransu, sai ka rantse cewa jihohin Arewa su ne ginshikin ci-gaban tattalin arzikin kasar nan.
Sai dai sannu a hankali duk irin wadannan tarin masana’antu da Allah Ya albarkaci yankiin da su, a yanzu sun koma kufai in banda ’yan kalilan da ke yin aiki.
A Jihar Kano kaɗai akwai daruruwan masana’antu waɗanda suke rukunin masana’antu na Sharada da na Bompai da na Challawa da sauransu.
Hakazalika Jihar Kaduna ma ta kasance cibiyar masana’antu a can baya, amma kamar yadda masana’antun Kano suka durkushe, su ma na Kaduna haka lamarin yake, lamarin da ya jefa dubban jama’a cikin halin talauci da kunci.
Bauchi daya ce daga cikin jihohin Arewa maso Gabashin kasar nan da ke fama da matsalar durkushewar masana’antu kimanin 15, wanda hakan na daga cikin manyan kalubalen tattalin arzikin jihar.
A baya Bauchi na daga cikin jihohin da suke samar da abubuwa da dama ta fuskar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, gami da bayar da gudunmmawa wajen habaka tattalin arzikin kasa baki daya.
Da zarar an ambaci sunan jihar, babban abin da ke fara zuwa ran mutum shi ne shahararren gandun daji da shakatawa da yawon bude ido na Yankari, wanda ke jan hankalin maziyarta daga sassan kasar nan da ma kasashen ketare.
Waɗanda suka durkushe a BauchiA shekarun baya, a bangaren gandun daji, bayan Yankari akwai gandun dajin Lame Burra, kuma duk suna samar da kudaden shiga ga Gwamnatin Jihar Bauchi daga masu yawon bude ido, amma durkushewar ko kuma nuna halin ko’in kula da su, ya sa ko dai sun mutu ko kuma suna cikin halin magagin mutuwar.
Daga cikin masana’antun da ake jihar akwai Kamfanin Steyr Nigeria Ltd, da suke hada manyan motoci da babura (Hero Punch) da turaktocin noma.
Ga kuma kamfanin yin kwanukan rufi na Asbestos da kamfanin yin kayan karau da ke Misau da ake kira Arewa Ceramics.
Sai kamfanin fulawa na Zaki Flour Mills, da Kamfanin Bauchi Furnitures masu yin gadaje da kujeru.
Sauran sun hada da Kobi Cola da kamfani wutar lantarki na Alind Nigeria da Kamfanin Taki na Bauchi, da Masana’antar sarrafa nama ta Bauchi, wanda Firayi Minista na farko Sa Abubakar Tafawa Balewa ya kafa, da dai sauran masana’antu.
Ya kawo koma-bayan kuɗaɗen shigaBinciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa durkushewar wadannan masana’antu ya taimaka kwarai da gaske wajen kawo koma-baya da karancin kudaden shiga da jihar ke samu.
Ko da yake gwamnatocin da sukayi mulki a jihar sun sha yin alkawuran farfado da wasu daga cikin wadannan masana’antu, a lokuta daban-daban.
Wasu cikin kamfanonin sun mutu murus kamar na Kobi Cola, da Zaki Flour da Guarana da Kamfanin Yankari Natural Water da na yin ruwa na Wikki da dai sauransu.
Waɗanda a yanzu ba a ganin su kuma wasu ko inda kamfanin yake babu alamarsa, wasu kuma koda an ga alamar ginin arurrushe yake kuma ya lalace da wuya ka sami wani kayan aiki da ke cikin hayyacinsa.
Shi kuwa Kamfanin Steyr ya mutu murus, duk da cewa ana kan shari’a a kotu saboda rahin biyan ma’aikatanasa hakkokinsu.
Hasalima wadanda suka sayi kamfanin suma sun gaza farfado da shi.
Daga shanu 250 an koma yanka 3A lokacin mulkin tsohon Gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda an yi kokarin farfado da kamfanin sarrafa nama na Bauchi, kuma har dambun nama ake yi da za a kai wa sojoji da suke fagen yaki.
A baya can da aka kafa kamfanin ana yanka shanu 250 a kullum, kuma har kasar Morocco ana kai mana baya ga jihohin cikin gida irin s u Lages da Inugu da Binuwai Filato da Nasarawa da sauran wurare.
Sai dai a yau ba a iya yanka shanu biyu ko uku, sannan injunan da ke sarrafa naman duk sun daina aiki sai abin da ba a rasa ba.
Gandun Dajin Yankari da kuma gandun kiwon dabbobi da yawon shakatawa da gwamnatin Jihar Bauchi ta samar duk sun mutu.
Amma dai gwamnati mai ci a yanzu na kokarin yin ayyuka da nufin sake farfado da martabarsu.
Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a kokarinta na farfado da masana’antun a zangon farko na mulkinsa ta yi niyyar sayarwa ko bayar da hayar wasu daga cikinsu da suka hada da masana’antar sarrafa nama ta Bauchi, Kamfanin Furniture na Bauchi, Kamfanin Taki da Otal na Zaranda, da wajen yawon shakatawa na Wikki da kuma wajen habaka kiwon dabbobi na Gallambi Cattle Ranch, da nufin ganin sun dawo suna yin aiki kuma ana samun riba.
Duk kokarin da Aminiya ta yi na jin ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu na Jihar Bauchi Alhaji Muhammad Salis Gamawa ya ci tura, saboda ya yi tafiya kuma bai dawo ba a lokacin da muke hada wannan rahoto.
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed a lokuta da dama ya sha alwashin farfado da wadannan masanaantu da nufin habaka hanyoyin samar da ayyukan yi, da kuma tattalin arzikin jihar.
Haka irin wannan lamari yake a Jihar Katsina, wadda duk da cewa ba jihar da ake bugun gaba da ita a harkokin kasuwanci, kamar irin su Kano ko Legas, amma duk da haka, tana da nata irin masana’antun da take takama da su.
Misali, akwai masaka da ke Funtuwa da kamfanin sarrafa farar kasa a yankin Kankara da kamfanin yin kusa da ke Kankiya sai kuma kamfanin mulmula karafa na Katsina Rolling Steal da kamfanin yin fenti da ke cikin garin Katsina.
Baya ga wadannan manyan kamfanonin, akwai kuma irin wadanda za a ce matsakaita ne irin na masu yin walda da kafintoci da sauran irin su.
Amma yanzu kusan duk wadancan masana’antu da aka ambata da ma wadanda ba a ambata ba, a yanzu wasu daga cikinsu na neman zama tarihi, saboda sun durkushe yayin da wasu ma babu su gaba daya sun bace.
Masana’antar da ake sarrafa farar kasa da ke yankin Kankara yanzu ta zama abin da ta zama saboda ko gwangwani guda ba a fitarwa daga wajenta.
Dalilin durkushewarsuTo mene ne dalili ko dalilan durkushewa ko ma mutuwar wasu masana’antun?
Kusan a iya cewa babbar matsalar ba za ta rasa nasaba da karancin wutar lantarki ba, kamar yadda wani da ya yi aiki a masana’antar mulmula karafa ya shaida wa wakilinmu.
“A lokacin da muke aiki karkashin kulawar DANA, sai a kawo bil na biyan kudin wutar lantarki har Naira milyan guda a wata.
“Amma sai ya zamo duk ranar da wutar ta yi awa uku cikakku, sai a yi ta murna domin an yi aiki mai yawa.
“Ka ga babban wuri ne, injinan da ake amfani da su ba karamin kudin mai ake kashewa ba.
“Akwai batun biyan ma’aikata da sauran su. Da aka duba sai aka ga cewa, maimamkon riba sai faduwa.
“Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya masana’antar da dauki hanyar durkushewa kafin daga baya a rufe kamfanin baki daya,” in ji shi.
Ita kuwa masana’antar sarrafa farar kasa da ke Kankara, wani mazaunin yankin ya aza alhakin durkushewarta a kan gwamnati.
Malam Sani ya ce, “lokacin da gwamnati ke kula da wurin, komai na tafiya sosai kamar yadda ake sarrafa auduga.
“Amma halin ko-inkula da aka fara nunawa ya janyo komai ya tsaya cik.”
Shi kuwa Malam Kabir Kankiya cewa, ya yi, “ita wannan masana’antar kusoshi babu mai iya cewa, ga dalilin da ya sa aka rufe ta.
“Mafi yawan bayanan da muka rika samu shi ne, za a yi gyare-gyare da kuma kawo sababbin injina wanda har zuwa yau ba mu ga komai ba sama da shekara 10 ko fiye da haka.”
Alhaji Sani Ado na daga cikin manyan masu sana’ar walda kuma shugaban kungiyar masu walda na Jihar Katsina, ya ce, “Farko wutar lantarki ita ce babbar matsalar da ke kawo mana koma baya ga wannan kamfani namu.
“Ga babu wadatar wutar ga kuma kudin da muke biya sun yi yawa sannan ga babu aikin kamar da.
“Har’ila yau, batun mai shi ma wata barazanar ce ta durkushewarmu. Idan muka duba yadda farashin litar gas yadda take tare da dubar yanayin janaretocin da muke amfani da su in an dauke wuta, dole muke samun inuwa mu zauna domin babu abin da za mu iya yi.
“Sannan shi kansa falankin karfen da muke sarrafawa da rodin da muke amfani da shi duk wani abu ne wanda za a ce farashin ya wuce tunanin mutum saboda tsada.
“Sannan ga shi babu wata hanya ta tallafi da gwamnati ke yi koda ta samo kayan ne ta sayar mana da sauki.”
A kan batun wutar lantarkin da aka fi kuka da ita, wata majiya mai tushe ta shaida mana cewar, a halin yanzu wutar da jihohin Katsina da Kano da Jigawa ta yi musu kadan.
Masakar Funtua kadai ke aikiDaga cikin manyan masana’antu ake da su a fadin jihar, masakar Funtuwa ce ke aiki har yanzu.
Ita ma can baya an kusa rufe ta amma saboda zama da suka yi da hukumar bayar da hasken wutar lantarki suka daidaita, shi ya sa har yanzu take aiki. Kuma ita ce masaka ta uku da ke aiki a yanzu a duk fadin Najeriya.
Binciken ya nuna cewar babban abin da ya haifar da durkushewar masana’antu a Jihar ta Katsina ita matsalar wutar lantarki da tsadar man fetur da gas.
Sai kuma rashin kulawar gwamnati musamman ga masana’antun da yake hakkinsu ke kanta. Kazalika, hauhawar farashin wasu kayayyakin masana’antu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi Jihar Kano Jihar Katsina tattalin arzikin wutar lantarki a masana antar sarrafa nama Jihar Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Ban Ji Dadin Zaman PSG Ba, Messi
Haka kuma an dakatar da shi, saboda zuwa Saudi Arabia ba tare da izinin mahukuntan PSG ba da ta kai bai samu halartar atisaye ba. Dan wasan tawagar Argentina, wanda ya koma Inter Miami, bayan ta yi mai tsoka daga manyan kungiyoyi ya ce ya koma Amurka ne domin ya taimakawa gasar kasar ta kara bunkasa a duniya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp