Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu
Published: 9th, March 2025 GMT
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi.
Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa.
A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa Shugabannin Larabawa Sun Amince Da Tsarin Gina Gaza Da Zai Lakume Dala Biliyan 53Ya kara da cewa, “Sin za ta hada hannu da Nijeriya wajen kyautata aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa 10 dake tsakaninsu, ciki har da inganta musaya tsakanin mata da hada hannu wajen gina al’ummar Sin da Nijeriya mai makoma ta bai daya. Ya kara da cewa, ya yi imani mata da dama za su amfana tare da cimma burikansu da samar da kyakkyawar makoma ta hanyar ingantaccen hadin gwiwar Sin da Nijeriya, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.
A nasa jawabi, mukaddashin babban sakataren ma’aikatar raya al’adu da fasahohi da bude ido da tattalin arzikin bangaren, Oraeluno Rapheal, ya kara tabbatar da goyon bayan da gwamnatin kasar ke bayarwa ga ci gaban harkokin mata. Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da tabbatar da inganta kwarewar mata ta hanyar bayar da horo da musayar al’adu da sauran shirye-shiryen dake da zummar ba mata damar kara taka rawar gani. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da Nijeriya tabbatar da Da Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Saudiyya sun jaddada wajabcin kara karfafa dangantakasu
Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori.
Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a wannan Juma’a a gefen taron gaggawa karo na 20 na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah.
A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan matsayin dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma masarautar Saudiyya, tare da jaddada aniyar kasashen biyu na ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakaninsu.
Bangarorin biyu sun kuma yi nazari kan halin da ake ciki a kan batutuwa daban-daban da suka shafi yankin, da ma sauran batutuwa na kasa da kasa, tare da jaddada wajibcin yin hadin gwiwa a tsakanin dukkanin kasashen musulmi wajen tinkarar kalubale dangane da batun Palastinu da Isra’ila ta mamaye, da kuma hana aiwatar da makarkashiyar da ake shiryawa da nufin share batun Palastinu, ta hanyar tilastawa al’ummar Gaza yin gudun hijira daga yankinsu.