2025-04-17@18:22:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2370
«da Nijeriya»:
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...

Iran Tana Daukan Tattaunawarta Da Amurka Da Muhimmanci Don Neman Warware Takaddamar Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada muhimmanci game da tattaunawa da ita kuma a shirye take ta magance matsaloli da takaddamar da ake yi kan Shirin makamashin nukiliyarta Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Kazim Gharibabadi ya bayyana cewa: zagayen farko na tattaunawar da ba na kai tsaye ba da aka gudanar a birnin Muscat na kasar Oman tsakanin Iran da Amurka, ba a samu wani babban sabani ba, kuma an yi shi ne domin tantance muhimmancin bangarorin biyu da kuma bayyana matsayinsu. Gharibabadi ya kara da cewa: A wannan zagayen tattaunawan Iran ta nuna muhimmancin tattaunawar da kuma rashin son bata lokaci, yana mai cewa amincewa da shawarar da Amurka ta yi na gudanar da shawarwari ba wai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Wata Cibiyar Kare Hakkin Bil’Adama Ta Bukaci Kama Jami’in Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Kasar Birtaniya
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar...
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama. Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata...
Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici. Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan...
Bugu da kari, illar matakin na Amurka na iya gurgunta salon hada-hadar kudade, da kwadago, da kirkire-kirkire da kasuwannin kasa da kasa ke cin gajiyarsu. Bisa la’akari da tarihi, mun san cewa Sin da Amurka kasashe ne dake da banbance-banbance ta fuskar ci gaba, da yanayin gudanar masana’antu da karfin tafiyar da su, amma duk da haka ci gaban sassan biyu ya dunkule wuri guda, ta yadda illata sashe daya na iya haifar da koma baya ga dukkanin bangarorin biyu. Ga misali, yayin da gwamnatin Amurka ke ta yayata manufar karin harajin ramuwar gayya, kamata ya yi mu lura cewa, Amurka na shigo da tarin hajoji da aka kammala sarrafawa, da wadanda ake kara sarrafawa a cikin kasar...
Mazauna gundumar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna sun shiga cikin fargaba sakamakon jerin hare-haren ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar sace mutane biyar da kuma kwashe shanu 1,200 cikin kwanaki hudu. Babban Jami’in Gundumar, Mista Stephen Maikori, ya tabbatar da faruwar hare-haren a ranar Laraba. A cewarsa, lamari na farko ya faru ne a daren Talata, 8 ga Afrilu, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Mashigi Boka-Libere, wani matsugunin Fulani, da misalin karfe 10 na dare. Maikori ya ce maharan sun kwashe garken shanu guda 12, inda kowanne garke yake da kimanin shanu 100, wanda ya kai jimillar dabbobi 1,200. Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba Najeriya da gwamnatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A karo na biyu a cikin mako guda, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur. Daga ranar 16 ga Afrilu, 2025, farashin man fetur zai tashi daga N865 zuwa N835. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rage farashin a cikin mako guda yayin da matatar man Dangote a baya ta rage farashin daga N880 zuwa N865 kan kowacce lita. Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu Sai dai kuma, har ya zuwa ranar Laraba, farashin bai canja ba a galibin gidajen mai da suka haɗa da cibiyoyin sayar da man fetur na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL). Yayin da ’yan kasuwa ke...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin aikin hajjin na kananan hukumomi. Ya ce masu gudanar da aikin, an zabo su ne daga kowace karamar hukuma 27 na jihar domin gudanar da aikin hajjin mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce su kuma masu gudanar da aikin za su horas da maniyyatan a cibiyoyin da aka kebe a kananan hukumominsu na jihar. Ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin...
Farfesa Bello ya ce gwamnatin jihar ta dage wajen bai wa ’yan mata masu tasowa ingantaccen ilimi da tallafa musu domin su zama masu amfani ga iyalansu da al’ummominsu. Ya bayyana godiyarsa matuka bisa gudunmuwar da Bankin Duniya ke bayarwa, yana bayyana aikin AGILE a matsayin wani gagarumin sauyi wajen canja ra’ayin al’umma game da ilimin ’ya’ya mata. “Kalma ba za ta isa ta bayyana yadda muke jin wannan taimako daga Bankin Duniya ba, musamman game da aikin AGILE. Kungiyar aikin a jihar, karkashin jagorancin Maryam Sani Dangaji, ta yi kokari sosai wajen fadakar da iyaye cewa AGILE yana kokarin taimaka wa yarinya ta gane cikakken kwarewarta,” in ji shi. Farfesa Bello ya kara da cewa gwamnatin...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin aikin hajjin na kananan hukumomi. Ya ce masu gudanar da aikin, an zabo su ne daga kowace karamar hukuma 27 na jihar domin gudanar da aikin hajjin mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce su kuma masu gudanar da aikin za su horas da maniyyatan a cibiyoyin da aka kebe a kananan hukumominsu na jihar. Ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin...
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace...
Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20. Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya. Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama...
An tabbatar da cewa, tashin hankalin ya barke ne jim kadan bayan da alkalin wasa ya busa tashi daga wasan, kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a safiyar ranar Alhamis, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu raunika a yayin rikicin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An bukaci gwamnatocin jihohi da su kara samar da tsarin kula da kiwon lafiya na bai daya (UHC) ga ‘yan kasa domin tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya a kasar. Jami’ar Ayyuka, Kula da Lafiya ta Duniya ga Mata a Lafiya ta Duniya, Najeriya (WGH), Dokta Sienne Oluwatosin Orogun, ta yi wannan kiran a wani taro mai taken “Amfani da Dabaru da Tsarin Gida don Haɓaka Tsarin Kiwon Lafiyar Duniya” a Ilorin, jihar Kwara. A cewarta akwai tsare-tsare da aka tsara don samar da inshorar lafiya mai araha ga masu rauni a cikin al’umma, ta kara da cewa aiwatar da ingantaccen aiki ya kasance kalubale. Tun da farko a nata jawabin, kwamishiniyar lafiya ta jihar Kwara,...
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mayar da dan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar, Shamsudeen Hassan Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Arewa, bayan da ya nemi gafarar majalisar. Hakan ya fito ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Bello Madaro ya raba wa manema labarai a Gusau. A zaman da aka yi, Kakakin Majalisar, Alhaji Bilyaminu Ismail Moriki, ya karanta abin da ke cikin wasikar neman afuwar Basko, inda daga nan ne ya nemi shawarar majalisar ta gamayya inda ‘yan majalisar suka amince da dage dakatarwar. Shugaban majalisar ya jaddada bude kofar majalisar na karbar irin wasikun neman afuwa daga sauran ‘yan majalisar bakwai da aka dakatar, inda ya ce irin wadannan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad ’yar Arewacin Najeriya ce da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar fannin kimiyya duk da ƙalubalen da matan yankin suke fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala, wanda a mafi yawan lokuta, ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙaurace wa karatar sa. NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wajen kula da marasa lafiya a asibitoci. Domin sauke shirin, latsa nan
Sojojin HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankunan kudancin Lebanon da ya zama ruwan dare a cikin kwanakin bayan nan. A jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gari “Aytas-sha’ab. Haka nan kuma tankokin yakin ‘yan mamayar sun kai wasu hari a kan wasu gidaje a garin na Aytas-sha’ab. Haka nan kuma sojojin mamayar sun gina wata Katanga da ta raba tsakanin Ayta da Khillatul-wardi. Har yanzu sojojin na HKI suna ci gaba da zama a cikin wasu wurare biyar da ta ki ficewa daga cikinsu bayan zuwa karshen wa’adin kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki. Kamfanin dillancin labarun Lebanon ya bayyana cewa; Jirgin yakin HKI maras matuki ya kai hari akan gidajen tafi da gidanka da...
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da gwamnatin Najeriya. Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar. Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.” Takwaransa na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa nan gaba Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su gana da shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, a matsayin ci gaban wannan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da yin kira da a kawo karshe killace garin da aka yi da kuma bai wa fararen hula kariya. Mayakan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” dake fada da sojojin Sudan ta shimfida ikonta akan sansanin ‘yan hijira na “Zamzam’ bayan kwanaki na barkewar fada a kusa da birnin al-fasha. Daruruwan mutane ne su ka rasa rayukansu yayin da wani adadi mai yawa na ‘yan hijirar ya jikkata. Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran na nuna cikakken goyon bayan Sudan a matsayin dunkulalliyar kasa. A bisa kididdigar MDD a kalla mutane 300 aka kashe...
Kungiyar kasuwanci ta duniya ta bayyana cewa, za a sami raguwar hajar da za a yi kasuwancinta a duniya da kaso 0.2% saboda Karin kudin fito da Amurka ta yi. Rahoton kungiyar kasuwancin ta duniya wanda aka fitar da shi a ranar Litinin din da ta gabata ta gina shi ne akan yadda tafiyar kasuwanci za ta kasance daga 2025-2026, wanda aka tsammaci zai rika samun bunkasa, sai dai kuma Karin kudaden fito da Donald Trump ya yi, ya sa kungiyar ta sauya hasashen da ta yi a baya. Cinikayya ta kayayyaki zai ta yi baya da kaso 1.5% idan har Donald Trump din ya yi aiki da sabuwar siyasar tasa ta haraji. Shugaban na Amurka ya dakatar da aiki...
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da Gwmanatin Najeriya. Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar. Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary You Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah. Allah Ne Ya haɗa wannan zumunta ka, babu wanda ya isa ya raba ta.”
Bakori ya ce, makaman da ake zargin an dauko su ne daga jihar Filato, ana shirin kaddamar da wani mugun nufi ne acikin Kano da kuma jihohin da ke makwabtaka da ita. Ya kara da cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai samame a wata maboya da ke Kuntau da Gwale, inda suka bankado yadda kungiyar ke gudanar da muggan ayyukanta. A wani samame da jami’an ‘yansandan suka gudanar sun kama wata babbar mota makare da buhunan siminti amma kuma an boye kwalaye shida wanda ake zargin kwayar tramadol ce da kudinsu ya haura Naira miliyan 150. An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu akan safarar kwayar da aka dauko daga Sokoto...
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun ta Jihar Kano ta ce za ta yanke hukunci nan gaba a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat, da wasu mutane da kamfanoni shida. Gwamnatin Jihar Kano ta tuhumi waɗannan mutane da kamfanoni da laifuka guda takwas da suka haɗa da karɓar rashawa, yin amfani da kuɗin jama’a ta haramtacciyar hanya, da kuma satar kuɗin gwamnati. Ganduje ya yi gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023. Lauyan Ganduje ya roki kotu da ta ba shi karin lokaci a shari’ar amma lauyan gwamnati ya soke wannan roko kuma ya bukaci kotu da ta yi watsi da shi. Ka dawo...
Ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dawo gida nan take domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ke ƙara ƙamari. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a jihohin Filato, Zamfara, Borno da wasu sassan ƙasar. Shugaba Tinubu ya tafi Faransa a ranar 2 ga Afrilu don “tafiyar aiki” na makonni biyu. Daniel Bwala, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Manufofi, ya ce tafiyar na da nufin yin yin bitar tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da kuma sauye-sauyen, gabanin cikar shekaru biyu na gwamnatin. A cikin saƙonsa na ranar Laraba, Obi ya ce ya zama...
Wato na farko, dogaro da kai a bangare makamashi, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kafa wani tsarin tattalin arziki dake amfanar da dukkan kasashen Asiya da Afirka, sun kuma kara karfin kafa tsare-tsaren samar da kayayyaki na mabambantan bangarori a shiyyar ta hanyar kara tuntuba, da dunkulewar manyan ababen more rayuwa, da yin musayar fasahohi, wanda hakan ya sa kasashen ba sa dogaro da sana’ar fitar da makamashi kawai, matakin da ya kara musu kwarin gwiwar samun bunkasuwa da kansu. Na biyu, samun jari da kansu. Sabon bankin raya mambobin BRICS, da bankin zuba jari na Asiya da dai sauran hukumomi, sun baiwa kasashe masu tasowa wata hanyar samun jari na daban ban da kasashen yamma. Ya...
Kakakin ma’aikatar rundunar sojin kasar Sin Zhang Xiaogang, a yau Laraba ya yi Allah wadai da rahoton tantance barazana da Amurka ta fitar, wanda ke kunshe da kalaman rashin da’a da ta yi kan kasar Sin, yana mai cewa shafawa kasar Sin kashin kaji ba zai tamaika kawar da tambarin Amurka a matsayin daular kutsen intanet ba. Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da amsa ga taron manema labarai dangane da rahoton tantance barazana na 2025 da ofishin daraktan hukumar leken asiri na kasar Amurka ya fitar. Inda ya ce, kasar Amurka ta kan zargi wasu da ayyukan da ita kanta ta aikata ko kuma take kan aikatawa, lamarin da ba wai kawai ya kasance...
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu. Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa. Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida...
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yin garambawul a fannin kiwon lafiya ta hanyar sanya tubalin gina sabbin cibiyoyin lafiya guda uku, da suka hada da Cibiyar Gwaji ta zamani, da Cibiyar kula da lafiyar Zuciya, da cibiyar samar da iskar numfashi (Cryo-Oxygen Plant) a Fanisau, da ke Dutse, babban birnin jihar. Wadannan ayyuka, wadanda za su ci biliyoyin nairori, wani bangare ne na hangen nesan gwamnatin na mayar da Dutse cibiyar yawon bude ido kan kiwon lafiya a yankin. A yayin bikin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana ta shiga kundin tarihi a ci gaban jihar. Ya bayyana cewa an tsara wadannan cibiyoyin ne domin kara karfin jihar wajen samar da ingantaccen...
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cika hannu da wani matashi da aka gani a wani yanayi mai kamanceceniya da baɗala da wata Akuya, lamarin da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta. Matashin, Shamsu Yakubu mai shekaru 24 da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Kano, ya shiga hannu ne bayan ɓullar wani bidiyonsa a dandalan sada zumunta musamman TikTok yana tsotsar farjin wata Akuya. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya A cikin bidiyon da wani yake ɗaukarsa wanda ya yaɗu sosai a soshiyal midiya, an hasko matashin a wannan yanayin mai kama da baɗala tare da Akuyar. Sai dai yayin da yake amsa...
An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori. An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani Ɗan banga na yankin ya mutu bayan da wani bam ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaron yankin. A cewarsa, motar ‘yansandan da ke sintiri ta ofishin ‘yansanda...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al’ummar duniya da su ba da himma wajen shiga wani gangami na tsawon mako guda domin ganin an kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, Hamas ta yi kira ga “kasashen Larabawa da na musulmi da kuma ‘yantattun mutane” na duniya da su halarci gangamin na ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi (18, 19 da 20 ga Afrilu). Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta ayyana wadannan ranaku a matsayin “ranakun nuna fushin duniya dangane da mamaya.” Hamas ta sake nanata bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don kawo karshen “ci gaba...
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar. Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023. Juyin mulkin da sojojin sukayi a Nijar ya haifar da takaddamar diflomasiyya sosai tsakanin Nijar da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta a wannan karon. Batun mayar da hambararen shugaban Nijar Bazoum da kin lamuncewa juyin mulkin daga gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar ta ECOWAS, shi ne a sahun gaba a...
Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar. Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur. Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.” Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan. Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu...
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba 16 ga wata cewa, mizanin hada-hadar tattalin arziki da aka fi sani da GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara a cikin rubu’in farko na shekarar 2025. A tsakanin wannan lokacin, alkaluman hukumar sun kuma bayyana cewa, mizanin ya nuna hada-hadar tattalin arzikin kasar ta kai yawan adadin kudin Sin yuan tiriliyan 31, da biliyan 875 da miliyan 800, kwatankwacin dala tiriliyan 4. 42. Har ila yau, kamar yadda alkaluman mahukuntan suka nuna, karuwar darajar kayayyakin da masana’antu suka samar ta kai kaso 6.5 bisa dari duk dai a rubu’in farkon na bana. An samu wannan bunkasa ce...
An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki. Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami. Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar. Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta. Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani...
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
Sun roƙi a dakatar da duk wani nau’in tashin hankali da ake yi a jihar. Ƙungiyar ta kuma yi addu’arsamun rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata. Ta kuma yi kira ga kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya da tattaunawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Waɗannan cibiyoyi ba iya Jigawa za su yi wa amfani ba, har ma da maƙwabta. “Tare da sabbin na’urorin gwaje-gwaje irin su MRI da mammography, ba sai an je wasu jihohi domin samun irin waɗannan ayyuka ba,” in ji shi. Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na ci gaba da inganta harkar kiwon lafiya a jihar, ta hanyar samar da sabbin ayyuka daidai da zamani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya jaddada cewa dole ne a gyara jam’iyyar PDP kafin a fara tunanin neman wani muƙami. Ya ƙara da cewa ko da siyasarsa ta tsaya a matsayin gwamna, zai kasance cikin farin ciki da gamsuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi, Umar Auwal, mai shekaru 20 da ya yi iƙirarin kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano. Matashin mai inkiyar ‘Abba Dujal’ ya ce ya miƙa kansa ga mahukunta ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a bayan nan. Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon murya da kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook. Da yake amsa tambayoyi, Abba Dujal ya yi iƙirarin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da kisan kai, fashi da makami da kuma satar babur...
HKI tana ci gaba da kai wa yankunan Gaza mabanbanta hare-hare da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai a yau Laraba. Tun da safiyar yau Laraba ne HKI ta kai hari akan wani gida dake unguwar “al-Tuffah” dake cikin birnin Gaza da hakan ya sa mutane 6 su ka yi shahada. A yankin Jabaliya kuwa jiragen yakin HKI sun kai hari akan wani gida da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3. A wani labarin kungiyar ” Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba” ta bayyana cewa; Isra’ila ta mayar da yankin Gaza zuwa Makabarta. Kungiyar ta bayyana cewa; Yadda Isra’ila take fadada wuraren da take kai wa hare-hare ta sama, kasa da ruwa a yankin Gaza , tana korar mazauna yankin...
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere. “Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI. Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi nuna kiyayya ne, da keta hurumin masallacin kudus. Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa; Abinda ;yan sahayoniyar suke yi, ya isa bakantawa musulmi al’ummunsu da gwmanatocinsu, ya kuma sa su yunkurawa domin hana ci gaba da abinda yake faruwa. Hizbullah ta kuma ce; Al’ummarmu ta larabawa da musulmi tana da cikakkiyar masaniya akan bukatar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba. Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan...
An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila. Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta. Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan...
An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila. Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta. Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan...
Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Wata majiyar HKI, yahudawa ta fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Ynetnews’ kan cewa sojojin sama na HKI su na dakon isowar boma-bomai har 3000 daga kasar Amurka a cikin yan makonni masu zuwa. Labarin ya kara da cewa rundunar ta na son ta gudanar da ayyukan soje mai fadin gaske a kan Falasdinwa wanda ya zai kawo karshen Hamas ya kuma kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Labarin ya kara...
Ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram bisa ƙudirinsa na “Renewed Hope Agenda” domin inganta rayuwar ’yan ƙasa da bunƙasa ƙasa baki ɗaya. Ministan ya ƙara da cewa bukukuwan Esta na ba da damar yin nazari da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin dangi da al’umma. Gwamnati ta buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin lumana da kwanciyar hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Hamas Ta Fadawa Iyalan Yahudawan Da Take Tsare Dasu A Gaza Kan Cewa ‘Ya’yansu Zasu Koma A Cikin Akwatunan Gawaki
Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani mai magana da yawan dakarun yana fadar haka a wani fai-fai bidiyo da rundunar ta watsa a yanar gizo a jiya talata. Dakarun suna kira ga iyalan yahudawan da su yi shirin karban gawakin yayansu a cikin akwatunan gawaki, wannan kuma saboda yadda jiragen yakin HKI suke kai hare-hare babu kakkautawa kan gaza ba tare da bambanta tsakanin yara da mata da sauransu ba. Sakon Bidiyon yana...
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ƙiris ya rage madugun jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu ta APC. Gamduje ya bayyana hakan ne yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta mutu murus, kuma jana’izarta kaɗai suke jira a gudanar a nan kusa. Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ziyarar da wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu (TSG) ta kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja. Ganduje ya ce APC a kodayaushe tana cikin shirin karɓar jiga-jigan ‘yan siyasa ciki har da Kwankwaso “idan...

Kakakin Sojojin Kasa Na Dakarun IRGC Ya Ce Butun Tsaron Kasar Iran Da Karfin Sojojin Kasar Ba Abinda Tattaunawa Da Makiya Bane
A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI, Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne, haka ma, karfin sojojin kasar. Janar Naeini ya ka ra da cewa, rawar dajin da sojojin IRGC suka yi a baya-bayan nan ya na tabbatar da hakan. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, Burgediya Janar Naeini yana maida martani ne ga gwamnatin Amurka wace ta fara maganar cewa, zata tattauna da kasar ta Iran ne a kan shirinta na makamai masu linzami, da kuma shirin ta...
Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
Jami’an diblomasiyya daga kasashen duniya da dama, da kuma wakilan kungiyoyin agaji daban-daban sun hadu a birnin London na kasar Burtania don tattauna batun yakin da ke faruwa a kasar Sudan wanda a halin yanzu yake cika shekaru 2 ke nan. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika New” ya bayyana cewa, taron na kwana guda ya tattara wakilai daga kasashen Faransa, Burtaniya, Jamus da kuma kungiyar tarayyar Turai, har’ila yau da kasashen da suke makobtaka da kasar ta Sudan. Labarin ya kara da cewa, yakin na Sudan wanda yake cika shekaru biyu, ya zuwa yanzu ya lakume rayukan mutane akalla 20,000, sannan ya yi sanadiyar kauracewar mutane kimani miliyon 14 zuwa cikin kasar da kuma kasashe makobta, sannan wasu da...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 18, da kuma Litinin, 21 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Easter a faɗin ƙasar. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo A jawabin da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida , Dokta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai. Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan lokaci, Mista Tunji yana kuma kira...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa. Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin...

Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka zai kasance ne a birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman. Baghaei ya yi watsi da rade-radin da ake yi kan inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce, “Bayan tuntubar juna, an yanke shawarar cewa birnin Muscat ne zai karbi bakwancin zagaye na biyu na shawarwarin, wanda za a yi a ranar Asabar mai...

Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...

Firaministan Malaysia: Xi Jinping Babban Jagora Ne Mai Matukar Mayar Da Hankali Kan Abubuwan Dake Shafar Zaman Rayuwar Jama’a
Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu. Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...

Rasha Ta Sanar Da Kashe Manyan Kwamandojin Sojin Ukraine Fiye Da 60 A Birnin Sumy Na Kasar Ta Ukraine
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...

Ina Dalilin Da Ya Sa Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin Ke Samun Bunkasuwa Mai Dorewa Ba Tare Da Tangarda Ba?
A kwanakin nan da suka gabata kuma, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 5, da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice wato Canton Fair karo na 137 a nan kasar Sin, inda yawan kamfanonin da suka halarce su suka kai matsayin koli a tarihi. Shugabar kwalejin nazarin tattalin arzikin Sin bisa salon kirkire-kirkire ta kasar Brazil madam Claudia Jannuzzi, ta ce Sin na matukar bude kofarta ga sauran sassa, tare da ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya. Cinikin shige da ficen Sin na samun bunkasuwa mai dorewa a gabanin duk wani kalubale. Ba shakka duniya za ta ga hakikanin halin da ake ciki, wato babu mafita a aiwatar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...

An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar. A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in. Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa a wani taronta karo na bakwai da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda ya gudana a birnin Maiduguri, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin ƙarfafa tsaro da haɓaka ci gaban yankin.
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu. EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan. Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da...
Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar moriyar kai, gami da neman tabbatar da adalci a duniya. Da ma shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gabatar da jerin zafafan matakan tattalin arziki ne don neman daidaita matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta. Sai dai ra’ayinsa na dora “Amurka ta zama gaba da komai” na tarnake masa damar samun biyan bukata. Raymond Thomas Dalio, shahararren mai kula da sha’anin hada-hadar...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, ta gaza tabbatar da zargin wulaƙanta takardar Naira da take yi wa fitacciyar ’yar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya. A bayan nan ne EFCC ta gurfanar da Murja a gaban kotu kan zargin cewa ta ci karo da wani bidiyonta tana rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400. A ƙunshin ƙarar da EFCC ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ta ce laifin da take tuhumar Murja tanadi na Kundin Dokokin Babban Bankin Nijeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris. OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata. Sabon rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin ya ce yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairu. A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce Algeria da...
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...

Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda. Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba Bola Tinubu, da nufin kawo masu zuba jari na kimanin Dala biliyan guda a ɓangaren sukari a Najeriya. Daga cikin yarjejeniyar, Kamfanin SINOMACH zai kafa masana’antar sukari da kuma gonar rake da za su fara da samar da metrik ton 100,000 na sukari a duk shekara. Kamfanin zai kuma taimaka da kwarewarsa da kayayyakin aikinsa wajen zartar da abubuwan da suka danganci gine-gine sayayyan kayan...
Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis. Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi da ke Khan birnin Younis da ke Gabashin Gaza. Mai magana da yawun asibitin, Saber Mohammed, ya bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da marasa lafiya da kuma jami’an kiwon lafiya. Isra’ila ba ta uffan a game da harin ba a halin yanzu, amma wasu rahotanni sun nuna jami’an tsaronta sun yi awon gaba da wasu Palasdinawa 14 a yankin Yamamcin...
Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini, inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara. Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu.. Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma...
Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci, har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano. Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda ya hana shi kuɗin kashewa. ’Yan sanda sun gurfanar da matashin ne a kan laifin ɗura ashariya da barazanar kisa da kuma ɗaukar makami ba bisa ka’ida ba. Bayan karanta masa takardar tuhumar, matashin ya amsa laifin, inda Alƙali Nasir Ahmad ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da tarar Naira dubu 20, da kuma karin ɗaurin wata shida tare da bulala 40.
Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa. Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya dauki labarin ya ambaci cewa,an gano gawawwaki 51 daga cikin wadanda aka kashe din, kuma wani adadi mai yawa na mutanen kauyukan sun jikkata. Ita kuwa kungiyar “Amnesty International” ta ambaci cewa maharan sun kuma rusa gidaje, tare da wawashe kayan da suke cikinsu. Kungiyar ta zargi jami’an tsaron kasar da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro. Jahar Filato ta dade...
Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Samson Zakhom, ya bayyana cewa an ceto mutanen ne da misalin ƙarfe 9 na dare bayan sun tsinci motar a daji babu kowa a ciki. Ya ce ganin haka ne sojojin rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar suka yi zargin sace fasinjojin cikinta aka yi. An yi garkuwa da masu ibada a Kogi Yadda kisan mutum...
Kasashe da dama sun bi sahu a wannan karnin, inda Saudiyya ta zama ta baya-bayan nan, wajen ba mata ‘yancin kada kuri’a a kananan zabukan kasar a shekarar 2015. (Ba su yin zaben shugaban kasa a Saudiyya.) A cewar Majalisar Dinkin Duniya, wannan ya sa yanzu mata a kowace kasa suna da ‘yancin yin zabe. Sai dai Afghanistan a karkashin mulkin Taliban, ta mayar da hannun agogo baya wajen kwace wa mata hakkin zabe. “Matan Afghanistan sun samu damar kada kuri’a ne kimanin shekaru 100 da suka gabata, amma yanzu a karkashin mulkin Taliban, an cire a tsarin dimokuradiya,” in ji tsagin mata na Majalisar Dinkin Duniya, sashen da aka ware domin karfafa gwiwar mata. Zuwa tsakiyar karni na 19,...
A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya. A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla. Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a...
Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48. Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno Rotayo,tare da cewa za ta mayar masa da martanin da ya dace. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Aljeriya ta bayyana cewa; A matsayinta na kasa mai cikakken shugabanci, tana daukar ma’aikatan ofishin jakadanci Faransa 12 a matsayin wadanda ba a maraba da su, sannan kuma ana bukatar da su fice daga kasar a cikin sa’oi 48.” Aljeriya din ta dauki wannan matakin ne a matsayin...
’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba. Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su. Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yankin Egbola, a kan hanyar Agabja a Ƙaramar Hukumar Lokoja. Shaidu sun bayyana cewa ’yan bangan gwmanatin jihar sun yi nasarar ceto wata mata daga cikin masu ibadan, bayan sun samu rahoton aukuwar lamarin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura Wani ɗan banga daga cikin waɗanda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwarsu. Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16978635-dalilan-rikice-rikice-a-jihar-filato.mp3?download=true
“Abin takaici ne cewa, a maimakon yin amfani da gagarumin goyon baya da yunƙurin da ƴan ƙasa ke ginawa, Onanuga ya zaɓi fitar da wata sanarwa mai takurawa. Fahimtar da ya yi wa dokar zabe yana da tsauri fiye da kima kuma ya kasa gane bambanci tsakanin yakin neman zabe ba bisa ka’ida ba da kuma furuci na siyasa na gaske na ‘yan kasa. “Ƙungiyar gamayyar matasan Arewa ta yi watsi da wannan mataki. Goyon baya ga Shugaba Tinubu na halitta ne kuma a duk faɗin ƙasar, Ginin siyasa ba laifi ba ne. “Don haka, muna kira da a gaggauta maye gurbin Bayo Onanuga, mai bayar da shawara kan harkokin siyasa da kuma mai bayar da shawara ga...
Dadin dadawa, Sin za ta ci gaba da shimfida yanayin ciniki mai inganci, da samarwa kamfanonin ingantattun hidimomi. Sin na maraba da masu zuba jari na sassan duniya da su gudanar da hada-hadarsu a kasar musamman ma wannan tasha ta ciniki maras shinge da more zarafin ci gaban Sin tare. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...