MDD, ta la’anci Isra’ila kan katse wutar lantarki a Gaza
Published: 11th, March 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin.
Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin.
Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila suka mabato cewa ministan makamashi da ababen more rayuwa na gwamnatin Isra’ila Eli Cohen ya umarci Kamfanin Lantarki na Isra’ila da ya katse wutar lantarki zuwa Gaza “nan take.”
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza tun a ranar 7 ga Oktoba, 2023 bayan harin ba zata na kungiyar Hamas, kuma tun lokacin ta kashe Falasdinawa sama da 48,400, baya ga lalata duk wasu cibiyoyi masu mahimmanci na Zirin kama daga asibitoci, sansanonin ‘yan gudun hijira, makarantu gidajen jama’a da dai saurensu tare da goyan bayan Amurka, lamarin da gwamnatocin kasashen duniya dama suka danganta da yunkurin share wata al’umma daga doron kasa.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta fitar a bara da sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Galant, bisa zarginsu da aikata laifukan yaki a Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp