Aminiya:
2025-03-12@20:23:45 GMT

Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike

Published: 12th, March 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi.

Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki.

Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas

Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha.

“Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in ji Wike.

“Ba zan yarda cewa a cikin wannan ƙasa, mutane na tunanin ‘yan majalisa uku za su zauna su yi doka, sannan su ce suna shirin zuwa Kotun Ƙoli.

“Shin har yanzu muna buƙatar yin aiki?” ya tambaya.

Rigimar siyasa a Jihar Ribas ta tsananta bayan da Kotun Ƙoli ta amince da sahihancin ‘yan majalisa 27 da ke goyon bayan Wike tare da soke zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a watan Oktoban 2024.

Har ila yau, Wike ya jinjina wa waɗanda suka ƙalubalanci abin da ya kira rashin bin doka, inda ya bayyana cewa dole ne a mutunta zaɓaɓɓun shugabanni.

“Shugabannin majalisa da ‘yan majalisa ba yara ba ne; an zaɓe su ne, kuma ba yaran kowa ba ne.

“Ya kamata a zauna da su, a gina dangantaka da su,” in ji shi.

Alaƙa dai na ci gaba da zafi tsakanin Wike da yaronsa Fubara, tun bayan da bar mulkin Jihar Ribas.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fubara Siminalayi Fubara Siyasa yan majalisa

এছাড়াও পড়ুন:

Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi

Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi.

Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke.

Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi

A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu.

Ya ce an buɗe sansanonin keɓe waɗanda suka kamu, yayin da gwamnatin jihar ta soma ɗaukar matakan daƙile cutar ciki har da neman alluran rigakafin.

Kwamishinan ya gargaɗi jama’a game da shan magunguna da kansu, inda ya ce mutane su gaggauta zuwa asibiti mafi kusa domin yin gwaji a duk lokacin da ba su da lafiya don tabbatar da halin da suke ciki.

“Ya kamata mutane su guji yin barci a cikin ɗaki mai cunkoso. Su riƙa wanke hannayensu akai-akai bayan sun shiga bayan gida.

“Ya kamata su daina ziyartar sansanonin da aka keɓe marasa lafiyar kuma su tabbatar sun wanke ’ya’yan itatuwa da sauran kayan abinci kafin su ci don guje wa kamuwa da cutar Sanƙarau,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris ya bayar da naira miliyan 30 domin siyan magunguna da sauran kayayyaki domin ɗaukar matakan daƙile cutar.

Sanƙarau wata cuta dai da ke janyo kumburi a wani rukuni na ƙwaƙwalwa ta kuma karya garkuwar ƙashin baya.

Alamomin cutar sun haɗa da sanƙarewar wuya, zazzaɓi mai zafi, rashin son haske, ruɗewa, ciwon kai da amai.

A bayan nan ne hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.

Cikin jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa har da Kebbi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike
  • HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
  • Kungiyar Tarayyar Turai ta yi barazanar sake kakaba wa Syria takunkumi
  • Fiye da Falasdinawa 130 ne Isra’ila ta kashe tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Hamas : matakin Isra’ila na hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza ”laifi na yaki”ne
  • Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi
  • Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC
  • Ranar Mata: UNICEF Da Jihar Jigawa Sun Horar Sa Mata 600 Shirin Jari Bola
  • Isra’ila ta katse wutar lantarki a zirin Gaza