2025-03-12@20:47:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1314
«yan majalisa»:
Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025. Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta...
Ganin halin da fasinjojin ke ciki, sojojin suka yi kukan kura kan yan ta’addan, inda hakan ya tilasta suka saki fasinjojin da suke yunkurin garkuwa dasu tare da arcewa zuwa cikin daji. Hakan ya sanya Sojojin kutsa kai cikin dajin domin farautar yan ta’addan, al’amarin da ya basu nasarar halaka wasu yan ta’adda da kwato makamai da babura. Bugu da kari kuma, babu ko mutum daya a cikin ayarin da ya samu rauni ko kwalzani, amma daga bisani sun kubutar da fasinjojin guda 7. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi. Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%. Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa...
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci zafin rana mai tsanani a kwanaki masu zuwa, a wasu yankuna na Najeriya. A cewar NiMet, jihohin da za su fi fuskantar wannan yanayi sun haɗa da Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, Benuwai, Enugu, Anambra, Abiya, Ebonyi, Kuros Riba da Babban Birnin Tarayya. ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Sauran yankunan da ake tsammanin za su fuskanci zafi mai tsanani sun haɗa da Kudu Maso Yamma, Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna, Zamfara, da Sakkwato. Zafi mai tsanani na iya zama hatsari ga lafiyar jikin mutum, yana iya haifar...

Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Suka Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...

Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Sun Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967. Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus. Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon...
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike “Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar. Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka...
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita su 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya. Wannan tallafi na da nufin ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a yankunan. Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000. Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul. Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan...
Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar. Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar. A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara. A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar...
Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai. Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin. Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Malam Yunusa Alfazazi, dan kimanin shekara 35 kuma mazaunin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, ya kafa tarihi a duniyar fasaha da kirkire-kirkire, inda yake kera jiragen sama da bindigogi da sauran na’urori daga robobi da filastik. Allah Ya albarkaci Nijeriya da mutane masu fasaha da baiwar kera kayayyaki ba tare da samun horo na musamman ba. Misali, Malam Yahaya Makera da ya kafa tashar rediyo mai aiki a Kaduna da kayan aikin daba su taka kara sun karya ba. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Haka nan, Mansur Nuhu Bamalli ya samu nasarori a fannin injiniyanci duk da karancin kayan aiki da suke...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu. Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari. Wani ganau da ya buƙaci a sakaya...
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili. Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024. Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya. A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
Wannan umurni yana da tushen shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma yana da hikima da fa’ida da dama. Allah Ta’ala Ya umurci Musulumi da yin isti’aza kafin karanta Alƙur’ani kamar yadda Ya labarta mana haka a cikin Suratul Nahli a aya ta 98. Inda Ya ce:” To idan za ka karanta Alƙur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan korarre (daga rahamar Allah).” Wannan aya ta tabbatar da neman tsarin Allah kafin a fara karatun Alƙur’ani. Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1] CIYARWA [Falalarta Da Muhimmancinta] Na 1 Ma’anar Isti’aza: Isti’aza na nufin neman tsari da kariya da fake wa a wurin Allah Shi kaɗai ban da waninsa daga sharrin Shaiɗan. Domin ƙarin haske duba Ibnu Jarir; Jãmi’ul...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba. An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin...
Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna. A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fara aikin kyautata na’urorin aiki da kuma maye gurbin tsoffin kayayyaki da sabbabi a bara. A bana kuma, an habaka wannan aiki zuwa harkar noma, inda za a mai da hankali wajen gyara da kyautata tsoffin manyan rumfuna masu aiki da hasken rana, da rumfuna na roba, domin karfafa tsarin kiyaye tsaro, da kara yin amfani da gonaki. Haka kuma, bisa wannan shiri, za a...
Majalisar Wakilai ta bai wa Hukumar Sadarwa ta NCC umarnin rufe duk wasu shafukan intanet masu nuna batsa a Nijeriya. Majalisar ta ba da wannan umarni yayin zamanta na yau Talata, inda ta nemi hukumar sadarwar ta umarci duk kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa. Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Wannan umarni na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Dalhatu Shehu Tafoki, ya gabatar. Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Nijeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar...
Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris. Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin. Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu. Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba...
Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta tabbatar da hakan ba. Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin ba shi kariya. Janar Muhoozi Kainerugaba ya kuma ce: “ Za mu kare dukkanin kasar Sudan Ta Kudu, kamar yadda za mu kare kasarmu. A wurinmu Salva Kiir ne mu ka aminta da cewa halartaccen shugaban kasar Sudan Ta Kudu,don haka duk wanda zai shelanta yaki akansa, ya shelanta yaki ne akan Uganda.” Har ila yau janar din na Uganda ya kuma ce; “ Wadanda...
Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
Fim din na “Habibullah” wanda Adnan Zandi ya fitar da shi, ya sami kyautar ne a wurin bikin baje kolin fina-finai karo na 28 a Poland. Wannan bikin baje kolin na fina-finai mafi girma da ake yi a kasar Poland domin tsamo fina-finan masu kima ta fuskar fasaha. Labarin fim din na “Habibullah’ an gina shi ne akan wani mutum da ya manyanta, amma yake jajurcewa wajen
Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba. Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan ta’adda su ka yi a gabar ruwan Syria, masu mulki a Damascuss suna boye gawawwakin gabanin isar tawagar MDD zuwa yankin. Mafi yawancin mutanen da aka yi wa kisan gillar a yankin gabar ruwan Syria, fararen hula ne wadanda aka fito da su daga cikin gidajensu,yayin da wasu kuma aka yi musu kisan gilla a gaban iyalansu. Ya zuwa shekaran jiya ana maganar cewa an...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da sauran dangoginsa da sun kai ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata. Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Kwamishinan ya yi bayanin cewa ya zama wajibi duk wasu alamomi da aka gani a ɗauka a shiga da su ɗakin gwaje-gwaje a bincika domin a tabbatar ko ƙoshin lafiyar al’umma. Dakta Faruk Umar ya ce ma’aikatarsa za ta saka ido kan jami’an lafiya na gwamnati da masu...
Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi. Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin. Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Shi ma wani mazaunin yankin, Suleiman Abubakar wanda ya rasa ɗan uwansa ɗaya a dalilin harin, ya ce maharan sun auka wa ƙauyukan ne da yammaci bayan sallar Magariba. “Abin ba a cewa komai domin mun ga tashin hankali. Sun kashe mutane da dama sun ƙone mana ƙauyuka kuma...
Haka kuma, an bukaci su riƙa shan isasshen ruwa, amfani da fanka ko na’urar sanyaya ɗaki, da kuma zama a wurare masu inuwa don kaucewa illar zafi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar. Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong. Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi. Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da...
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.” Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi, tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa wasu. Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.” Jami’in...
An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana. ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ An hana tashe bana a Kano — Nalako Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana na gargaɗin cewa idan NNPC ta daina sayar wa matatar Dangote mai a naira, hakan na iya haifar da hauhawar farashin man fetur, maimakon rage farashin da ake tsammani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar ƙasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki waɗanda suke takun saƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke ƙullawa Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP. NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi DAGA LARABA:...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kwanan nan ne aka fitar da motar daukar mara lafiya ta farko mai ISO na ma’auni na kasa da kasa, wanda tawagar bincike karkashin jagorancin kwararrun Sinawa suka tsara, mai suna motar asibiti mai dakin kebance mara lafiya wato “Negative Pressure Ambulance Medical Cabin Technical Specifications”. Wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya suna da kayan aikin jinya masu muhimmanci, galibi ana amfani da su don kebe mara lafiya cikin aminci yayin da ake jigilarsu, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da cututtuka daban-daban na numfashi. Wannan ma’auni na kasa da kasa ya gabatar da bukatun fasaha a karon farko wanda ya kamata a samar a cikin irin wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya, kuma...

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...

Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas da kudurin rahoton aikin kwamitin dindindin na taron, da rahoton da kwamiti mai kula da kudurori ya gabatar game da bincike kan kudurorin da aka gabatarwa taron, kana da kudurin siyasa na taron da dai sauran muhimman takardu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da tsaron makarantunta, inda za a hada hannu da masu ruwa da tsaki don kara karfafa tsaro a yankunan da makarantu suke. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar da kuma horas da jami’an tsaron makarantu, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar. Gwamnan wanda kwamishinan Ilimi Alhaji Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki kudirin gwamnatinsa na bunkasa fannin ilimi a jihar. Ya ce yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubale wajen tabbatar da tsaro a makarantu, wannan shirin wani...
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi. Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba...
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba. Ya ce a matsayinsa na wanda aka kafa jam’iyyar APC da shi, zai ci gaba da tunawa da faɗi tashi da kuma kyakkyawar mu’amalar da ya yi da duk abokan hulɗarsa. Ya ce ya yi fatan cewa jam’iyyar APC wadda...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari. Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma fara horaswar da aka gudanar a Dutse. Alhaji Adamu Sabo ya ce, baya ga jajircewa, da juriya, da nasarorin da mata suke da, bikin ya yi duba kan irin rawar da mata suke takawa wajen dorewar muhalli da bunkasar tattalin arziki. Ya jaddada cewa ta hanyar shirin bola jari, watiWaste to Wealth Initiative, za su iya baiwa mata damar kare muhalli da kuma samar...
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba. Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka assasa ta tun fil-azal.” Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon...
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da a wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta. El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba. Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka assasa ta tun fil-azal.” Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar. A yanzu dai wannan...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai. Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na...
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta,...
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel. Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin...
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya. An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja. Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci Wata majiya daga iyalansa ta ce tsohon Mataimakin Gwamnan ya rasu ne cikin daren ranar Lahadi. Cif Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999. Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogin, ƙani ne ga tsohon Darekta Janar na Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai...
Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron...
Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 a cikin kwanaki biyu kacal. Wannan tashin hankalin, ya fi shafar yankin yammacin Syria, wanda ya kara ta’azzara halin da ake ciki. A baya dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa, an kashe akalla mutane 237 da suka hada da 142 wadanda ba mayakan ba ne a yankin gabar ruwan kasar ta Syria, tun bayan fara kazamin fada a ranar Alhamis din da ta gabata....
Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News. Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci. Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu Afrika ta...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi tsattsauran gargaɗi dangane da rahotannin da ke yawo kan cirar kuɗi daga albashin ma’aikatan gwamnati ko kuma ƙin biyan su gaba ɗaya. Ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin ma’aikata da cin amanar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba. Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Biyo bayan korafe-korafen da ma’aikata suka yi, na cewa wasu daga cikinsu sun shafe watanni ba tare da samun hakkokinsu ba, Gwamna Yusuf ya sha alwashin gano masu hannu a wannan ɗanyen aiki da kuma hukunta su. “Gwamnatin nan ba za ta...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa. Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran a matsayin tushen rashin tsaro a yankin. Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu iyalai baki daya a wannan tashin hankali, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin “mai matukar tayar da hankali”. Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan kisan kiyashin da masu dauke da makamai suka aikata, tare da hukunta wadanda suka aikata laifukan. Babban jami’in kare hakkin bil adama na MDD ya kara da cewa, “Muna samun rahotanni masu matukar tayar da hankali kan yadda ake kashe iyalai baki daya, da...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan fararen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...
Shehun malami al-Imam Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Alƙur’ani ya sauka shi ne kira ga bautar Allah da shiga cikin addininsa. Wannan magana tana da tushen ilimi mai zurfi wanda ke da nasaba da tauhidi da shari’a, da hikimar shiriya. 1. Tauhidi a Matsayin Asalin Kiran Alƙur’ani: Manufar farko da Alƙur’ani ya zo da ita; ita ce tabbatar da tauhidi, wato bautar Allah Shi kaɗai ba tare da sanya masa abokin tarayyaba. Wannan ita ce mafi girman sako da dukan annabawa suka zo da shi. Allah ya ce: “Kuma babu wani Manzo da Muka aiko a gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa: Lallai babu abin bautawa da gaskiya...

An Yi Cikakken Zama Na Uku Na Taron Shekara-Shekara Na Majalisar Bada Shawarwari Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin
An yi cikakken zama na uku na taron shekara shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin da safiyar yau Lahadi a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing, inda zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin, Wang Huning ya halarci taron, kana, membobin majalisar guda 14 ne suka gabatar da jawabai. A jawabinta, mambar majalisar Ge Huijun ta ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen babban taron murnar cika shekaru 75 da kafa majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, jawabin da ya kafa alkabila da samar da babban tushe ga ci gaban...
A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata su samu sana’a da za ta rage musu dogaro da wasu. PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025 An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba “Wannan tallafi yana da muhimmanci domin zai taimaka wa mata su kula da kansu da iyalansu ba tare da jira komai daga mazajensu ba. “Wannan kuma wani yunƙuri ne na taimakon jama’a kamar yadda maigidana, Hon....
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi. Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa. A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa...
Wani mutum wanda yake nuna kin amincewa da zaluncin da HKI yake yi wa mutanen Gaza, ya hau kan hausumiyar agogon “ Big-Bang” a birnin London dauke da tutar Falasdinu. An sami cunkuson motoci a yankin Westminster dake birnin London a jiya Asabar,yayin da masu ceto suke kokarin isa ga mutumin domin sauko da shi daga kan hausmiyar agogon. Jami’an ‘yan sandan sun sanar da samin rahoton abinda ya faru da misalin karfe 7 na safe,kuma sun fara aiki domin ganin an sauko da mutumin cikin lafiya. Jami’an tsaro sun sanar da cewa an rufe hanyar da take zuwa majalisar saboda abinda ya faru. Haka nan kuma gadar da take zuwa Wesminster da sauran hanyoyin da suke yankin duk an...
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a. Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin. A shekarar...
Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’. Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993. “Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a Jihar Gombe, Ali Isa JC, ya raba wa Musulmai da Kiristoci 2,000 kayan abinci don rage wahalar Azumin watan Ramadan da na Kiristoci. Ali JC ya bayyana cewa wannan tallafi yana da muhimmanci don sauƙaƙa wa jama’a gudanar da ibadarsu cikin sauƙi. An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta “Buƙatar kayan abinci tana ƙaruwar a irin wannan lokaci, kuma muna ƙoƙarin taimaka wa mutanen mazaɓarmu su samu sauƙin rayuwa,” in ji shi. Baya ga kayan abinci, ya kuma raba babura 10 da babura masu kafa uku guda 20 domin tallafa wa mutane 200 a Jihar Gombe, inda kashi 50 cikin 100 aka...
Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar adalci da zaman daidaito, kuma karin kasashe na rungumar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa na kara karfinsu, inda suka riga suka zama muhimmin karfin da ke kiyaye zaman lafiya da sa kaimin ci gaban duniya. Mutanen kasashen yamma su kan ce, “Moriya ta fi zumunta muhimmanci da dorewa”. Amma a ganin Sinawa, ya kamata abota...
A wajen Arteta, wasan na ranar Lahadi a gidan Manchester United ba kawai wasa ne na samun maki uku ba, har ma game da bikinshi na wasa 200 a matsayin kocin Arsenal a gasar Firimiya, kocin dan kasar Sifaniya zai shiga cikin jerin jiga-jigan masu horarwa da su ka samu wannan nasara, inda ya zama na 13 kacal da ya yi hakan da kulob guda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni sun bayyana cewa, ya kammala yunkurin komawa jam’iyyar SDP. Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na nan dan jam’iyyar PDP na gaskiya. Yayin da yake bayyana rahotannin a matsayin “karya”, ofishin yada labaran ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton sauya jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Isyaku Mahmud, makaho ne dan shekara 28 da ke sana’ar sayar da data a yankin Kudancin Kaduna. Ya shaida wa Aminiya cewa har sana’ar hada-hadar kudi ta POS yana yi a baya, amma yanzu ba shi da jari. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Aminiya ta ga yadda makahon yake sarrafa manhajojin WhatsApp is Fesbuk kuma yake sayar da data kai tsaye daga wayarsa ta hanyar amfani da tsarin Smart Cash tare da tura kudi da wayar tasa, kamar yadda ya gwadawa wakilinmu. Dan asalin garin Yalwa da ke Karamar Hukumar Tudun Wada (Dan Kadai) da ke Jihar Kano ne, ya kwashe shekaru kusan biyar yana zuwa yawon bara...
Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila. Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun. Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin...
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku. Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma kungiyoyin da suke kawance da su da suka da alaka da alkaida, sun kashe fararen hula 745 na Alawi a cikin kwanaki uku da suka gabata, wanda ya haura adadin da aka sanar a lokutan baya. Sai dai Fox News ta buga misali da wata ‘yar Alawiyya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne aka kiyasta an kashe...
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...