Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM
Published: 12th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM.
Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.
Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala.
Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta ATM daga Naira 65 zuwa Naira 35, don sauƙaƙa wa al’umma.
Sabon tsarin na CBN ya tanadi cewa, idan kwastoma ya cire kuɗi daga ATM na bankinsa, ba za a caje shi komai ba; amma idan ya cire daga ATM na wani banki daban, za a caje shi Naira 100 kan kowace Naira 20,000 da ya cire.
Majalisar ta nuna damuwa cewa wannan ƙarin caji zai ƙara matsin lamba ga ‘yan Najeriya, musamman ma masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalolin tattalin arziƙi.
Saboda haka, ta umarci CBN da ya dakatar da aiwatar da wannan sabon tsari har sai an gudanar da cikakken nazari tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun mafita mai ɗorewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai Sabon Tsari a dakatar da
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki.
Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu.
Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati.
NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan RamadanaShirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin ƙarfi suke samu yayin da suke azumi.
Domin sauke shirin, latsa nan