2025-03-13@01:06:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1947

«a dakatar da»:

    Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya. Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba. A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa,...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd yayin da suke ƙasar Sin.   Tang Zhangwei, ya jagoranci wasu kamfanoni zuwa jihar Zamfara, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a sassa masu muhimmanci, domin bunƙasa tattalin arziki.   A nasa jawabin, gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin da kamfanonin ƙasar Sin ke yi na tabbatar da nasarar haɗin gwiwarsu.   “Ina so in yi muku barka da zuwa Jihar Zamfara. Muna maraba da ku. A watan Fabrairu, na jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Sin don ganawa da kamfanoni a sassa daban-daban da kuma gano...
    Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025. Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta...
    Ganin halin da fasinjojin ke ciki, sojojin suka yi kukan kura kan yan ta’addan, inda hakan ya tilasta suka saki fasinjojin da suke yunkurin garkuwa dasu tare da arcewa zuwa cikin daji.   Hakan ya sanya Sojojin kutsa kai cikin dajin domin farautar yan ta’addan, al’amarin da ya basu nasarar halaka wasu yan ta’adda da kwato makamai da babura.   Bugu da kari kuma, babu ko mutum daya a cikin ayarin da ya samu rauni ko kwalzani, amma daga bisani sun kubutar da fasinjojin guda 7. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi. Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%. Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci zafin rana mai tsanani a kwanaki masu zuwa, a wasu yankuna na Najeriya. A cewar NiMet, jihohin da za su fi fuskantar wannan yanayi sun haɗa da Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, Benuwai, Enugu, Anambra, Abiya, Ebonyi, Kuros Riba da Babban Birnin Tarayya. ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Sauran yankunan da ake tsammanin za su fuskanci zafi mai tsanani sun haɗa da Kudu Maso Yamma, Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna, Zamfara, da Sakkwato. Zafi mai tsanani na iya zama hatsari ga lafiyar jikin mutum, yana iya haifar...
    Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...
    Wani jami’an gwamnatin kasar UAE ne zai isar da sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghani ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara na kasar UAE Anwar Gargash yana kan hanyarsa ta zuwa Tehran dauke da wasikar, don isar da ita ga  jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei. Labarin ya kara da cewa Gargash zai hadu da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da farko bayan isarsa birnin Tehran. Kafin haka dai Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran siyasa, wanda ya je kasar UEA...
    Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara. Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya. Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba. Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma...
    Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967. Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani  shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus. Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon...
    “Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.   “Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an kwato dabbobin da suka sace.   “Kwamishanan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an da suka nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikin ceto, ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike “Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar. Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka...
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
    Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta fitar da sunayen kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar Alhazan bana. Bayanin ya ƙunshi sunayen jiragen da kuma adadin mahajjatan da aka ware wa kowannensu. Kamfanin Fly Nas zai yi jigilar Alhazai 22,893, kashi 32.12 bisa dari kenan na maniyyatan Najeriya a bana, yayin da Kamfanin Air peace ya sami Alhazai  9,145 , kashi 12.83. Sauran su ne Max Air Ltd da aka warewa Alhazai 23,343, kashin 32.75 kenan bisa dari, sai kamfanin Umza Air Ltd an ware  da ya sami 15,893 wato kashi 22.30 bisa 100, wanda ya kawo adadin maniyyata 71,274 da ake sa ran za su sauke farali a bana. Hukumar ta NAHCON ta ce za a fara jigilar...
    Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa, sun shiga falakin da ake so cikin nasara, kamar yadda hukumar kula da kimiyya da fasahar sararin sama ta kasar Sin (CASC) ta bayyana. Hukumar ta kara da cewa, taurarin za su kasance rukunin taurarin dan’adam na kaddamar da ayyukan intanet na kasuwanci na kasar Sin. Wannan aiki na bincike da aka kaddamar na farko daga sashe mai lamba ta 1 na tashar harba kumbon,...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
    Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
    Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar. HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga. Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon...
    Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar. Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025. Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da shi. Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci  ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
    Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
    Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Rundunar sojan Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a babban birnin Sudan ta Kudu bisa bukatar Juba, a daidai lokacin da ake fargabar sake barkewar yakin basasa, musamman a halin da ake ciki tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da mataimakinsa na farko. A wannan Talata rundunar sojin Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Juba, babban birnin Sudan ta Kudu. Kakakin rundunar sojin Uganda Felix Kulayigye ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, batun tura sojojin na zuwa ne bisa bukatar gwamnatin Sudan ta Kudu. An kara samun tashin hankali a ‘yan kwanakin nan a kasar Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur, bayan da gwamnatin shugaba Salva Kiir ta kame...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar. Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar. A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara. A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar...
    Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare,  duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya yi nuni da lamari na baya-bayan...
    Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai. Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin. Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu. Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari. Wani ganau da ya buƙaci a sakaya...
    Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili. Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha...
    Kasar Yemen ta sanar da cewa za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan Isra’ila a wasu muhimman yankunan teku da ke gabar tekun kasar bayan cikar wa’adin da ta gindaya wa Isra’ila na ta sake bude mashigar zirin Gaza tare da bayar da damar kai agaji cikin yankunan Falasdinawa da yaki ya daidaita. Rundunar sojin Yaman ta fitar da sanarwar a cikin daren jiya, inda ta ce za a ci gaba da kai hare-hare kan duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ISra’ila kamar yadda Abdul-Malik al-Houthi shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar ya bada umurni. Tunda farko Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bai wa gwamnatin Isra’ila kwanaki hudu ta bude hanyoyin kai kayan agaji Gaza...
    Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa. Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin. Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
    Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
    Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024. Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya. A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba. An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin...
    Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna. A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fara aikin kyautata na’urorin aiki da kuma maye gurbin tsoffin kayayyaki da sabbabi a bara. A bana kuma, an habaka wannan aiki zuwa harkar noma, inda za a mai da hankali wajen gyara da kyautata tsoffin manyan rumfuna masu aiki da hasken rana, da rumfuna na roba, domin karfafa tsarin kiyaye tsaro, da kara yin amfani da gonaki. Haka kuma, bisa wannan shiri, za a...
    Da wannan nasarar ne Barcelona ta samu nasarar zamowa kungiya ta farko da ta tsallaka zuwa matakin kwata fainal a sabon jadawalin gasar Zakarun Turai da aka fara amfani da shi bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Wakilai ta bai wa Hukumar Sadarwa ta NCC umarnin rufe duk wasu shafukan intanet masu nuna batsa a Nijeriya. Majalisar ta ba da wannan umarni yayin zamanta na yau Talata, inda ta nemi hukumar sadarwar ta umarci duk kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa. Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Wannan umarni na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Dalhatu Shehu Tafoki, ya gabatar. Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Nijeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Atisayen sojojin ruwa mai taken (“damarar tsaro na shekara ta 2025”) wandake ke gudana a nan Iran. Wanda ni tahir amin zan karanta. ////.. A ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasashen China, Rasha da kuma Iran suka fara atisayen sojojin ruwa na hadin giwan kasashen uku, wanda suka sanya masa suna :damarar tsaro na shekara ta 2025″ wanda kuma ke gudana a halin yanzu a arewacin tekun Indiya da ke kudu maso gabacin kasar Iran da tekun farisa da kuma tekun Omman. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa atisayen wanda zai dauki kwanaki uku cur ana gudanar da shi, zai...
    Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris. Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin. Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu. Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba...
    Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta  tabbatar da hakan ba.  Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin ba shi kariya. Janar Muhoozi Kainerugaba ya kuma ce: “ Za mu kare dukkanin kasar Sudan  Ta Kudu, kamar yadda za mu kare kasarmu. A wurinmu Salva Kiir ne mu ka aminta da cewa halartaccen shugaban kasar Sudan  Ta Kudu,don haka duk wanda zai shelanta yaki akansa, ya shelanta yaki ne akan Uganda.” Har ila yau janar din na Uganda ya kuma ce; “  Wadanda...
    Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba.   Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci.   Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda...
    Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow  Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da  sauran dangoginsa da sun kai  ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta  EFCC ta bayyana cewa,  ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar  “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke. Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu. Ya...
    Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 wadda ita ce majalisar dokokin kasar Sin ta gudanar da taron rufe zaman babban taronta a yau Talata. Shugaba Xi Jinping tare da sauran jagororin gwamnatin kasar sun halarci taron a katafaren zauren jama’ar kasar Sin, watau Great Hall of the People, da ke birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata. Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Kwamishinan ya yi bayanin cewa ya zama wajibi duk wasu alamomi da aka gani a ɗauka a shiga da su ɗakin gwaje-gwaje a bincika domin a tabbatar ko ƙoshin lafiyar al’umma. Dakta Faruk Umar ya ce ma’aikatarsa za ta saka ido kan jami’an lafiya na gwamnati da masu...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi. Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin. Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Shi ma wani mazaunin yankin, Suleiman Abubakar wanda ya rasa ɗan uwansa ɗaya a dalilin harin, ya ce maharan sun auka wa ƙauyukan ne da yammaci bayan sallar Magariba. “Abin ba a cewa komai domin mun ga tashin hankali. Sun kashe mutane da dama sun ƙone mana ƙauyuka kuma...
    Duk da haka, kungiyar za ta ci gaba da amfani da Old Trafford har sai an kammala sabon filin wasan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar. Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong. Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi. Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa  al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa. “Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba,” in ji Araghchi a wani sakon da ya wallafa a shafin X. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani babban jami’an makamashi  a kasar Iraki yana cewa, a halin yanzu Iraki ba ta da wasu hanyoyin da za su maye gurbin makamashin da ake shigowa dashi  daga kasar Iran, lamarin da zai haifar da babban kalubale wajen biyan bukatar wutar...
    Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
    UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza. Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen  zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka. “Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin...
    Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.” Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi,  tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa  wasu. Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.” Jami’in...
    Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko. Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa ranar Litinin 10 ga watan Maris, kungiyar ta ce Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu na kawo cikas ga aiwatar da yarjejeniyar saboda wasu dalilai na rajin kansa da kuma na siyasa kawai. Hamas ta kuma kara jaddada aniyar ta na aiwatar da yarjejeniyar, inda ta bayyana aniyar ta na kaddamar da shirin tsagaita wuta a mataki na biyu ba tare da bata lokaci ba. Har ila yau kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran. Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.” Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki samun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, musamman gabanin watanni masu zafi na wannan shekara.” Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Iraki. Ya kara da cewa Iran ta tsaya tsayin daka kan kudurin ta ga gwamnatin Iraki na dakile ayyukan Amurka da suka sabawa doka. Kalaman Araghchi sun zo ne bayan da Amurka ta sanar da...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
    Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da ɗaukar salo iri-iri yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasaƙe suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ɗiga mata ɗanba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar ƙasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki waɗanda suke takun saƙa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suke ƙullawa Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP. NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi DAGA LARABA:...
    Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sha nanata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare fiye da kima, kuma Amurka na neman yin ciniki bisa adalci da daidaito. Sai dai kuma, da yake mayar da martani a yau Litinin 10 ga watan Maris, yayin wani taron manema labaru na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta yi nuni da cewa, maganar da ake yi a kullum kan “rasa madafa” da neman cikakken daidaiton cinikayya ta saba wa ilimin tattalin arziki na asali, da yin watsi da hukunci da muradun kamfanoni da masu sayayya na Amurka. Mao Ning ta ce, halin da ake...
    Mayar da hankali kan taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) da kuma taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar (CPPCC), muhimmin abu ne ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin. Zuwa karshen shekara ta 2024, adadin kamfanonin da baki ’yan kasashen waje suka zuba jari don kafa su a kasar Sin, ya zarce miliyan 1.239. A matsayinsu na wadanda ke gane wa idanunsu, da wadanda ke bayar da gudummawa, gami da wadanda ke cin moriya, daga harkokin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, kamfanonin jarin waje sun riga sun bada hadin-kai tare da samun ci gaba tare da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. A...
    Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC Aminiya ta ruwaito cewa, Ibrahim Yakubu Adamu wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA. Falgore ya ce nan gaba kaɗan za su aika masa goron gayyata domin tabbatar da buƙatar gwamnan. Kazalika, majalisar ta kuma tabbatar da dokar...
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
    Kirkira ita ce kashin bayan ci gaba, kuma hazaka ita ce ginshikin kirkira. A zamanin yau, fannoni masu tasowa musamman na fasahar zamani kamar kirkirarriyar basira (AI) da sauransu suna bunkasa, kuma akwai bukatu na matukar gaggawa ga sabbin hazaka. Hakan ya sanya kasar Sin ta maida hankali kan raya hazaka tun wuri-wuri, da kara zuba jari a fannin ilimi, da dasa iri na kirkire-kirkire don ya tsira a cikin zukatan matasa ta hanyar “zuba jari kan gina mutane”. Matakan da aka ambata a cikin rahoton aikin gwamnati a taruka biyu na bana, kamar bayar da tallafin tarbiyyar yara da karfafa tsare-tsaren tabbatar da kowane yaro ya samu ilimi ala tilas, ayyuka ne masu haske ga wannan manufa ta “zuba...
    Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki. Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu. Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Ya ƙara da cewar, wannan sana’a ta ɗinki sana’a ce da ke da matuƙar albarka idan ka sa juriya a ciki domin kuwa ba sana’a ce da za ka tara kuɗi akai-akai ba nan take. “Sai dai kuma muddin ka tsayar da gaskiya tare da cika alƙawari to lalle za ka samu babban rufin asirin...
    A kwanan nan ne aka fitar da motar daukar mara lafiya ta farko mai ISO na ma’auni na kasa da kasa, wanda tawagar bincike karkashin jagorancin kwararrun Sinawa suka tsara, mai suna motar asibiti mai dakin kebance mara lafiya wato “Negative Pressure Ambulance Medical Cabin Technical Specifications”. Wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya suna da kayan aikin jinya masu muhimmanci, galibi ana amfani da su don kebe mara lafiya cikin aminci yayin da ake jigilarsu, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen kula da cututtuka daban-daban na numfashi. Wannan ma’auni na kasa da kasa ya gabatar da bukatun fasaha a karon farko wanda ya kamata a samar a cikin irin wadannan motocin asibiti masu dakin kebance mara lafiya, kuma...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie  ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba.  Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba  tattaunawa sai dai tursasawa. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...
    Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran. A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
    Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas da kudurin rahoton aikin kwamitin dindindin na taron, da rahoton da kwamiti mai kula da kudurori ya gabatar game da bincike kan kudurorin da aka gabatarwa taron, kana da kudurin siyasa na taron da dai sauran muhimman takardu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Shugaban karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, Alhaji Sani Aliyu, ya tabbatar da harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai a yankin, inda suka kashe mutane kimanin 15 tare da kona kauyuka 7. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan rediyon Najeriya da ke jihar Kebbi, shugaban karamar hukumar ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewar wata majiya mai tushe, Malam Umar, maharan sun kara kona akalla wasu kauyuka bakwai da ke kusa da Birnin Dede, duk a cikin karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbin. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Malam Umar ya bayyana cewa, an kai harin ne domin ramuwar gayya kan kisan da jami’an tsaro...
    Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da tsaron makarantunta, inda za a hada hannu da masu ruwa da tsaki  don kara karfafa tsaro a yankunan da makarantu suke. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar  da kuma horas da jami’an tsaron makarantu, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar. Gwamnan wanda kwamishinan Ilimi Alhaji Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki  kudirin gwamnatinsa na bunkasa fannin ilimi a jihar. Ya ce yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubale wajen tabbatar da tsaro a makarantu, wannan shirin wani...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
    Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi. Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba...