Nazarin CGTN: Manufofin Haraji Na Amurka Sun Rage Kwarin Gwiwa Kan Kasuwar Hannayen Jari Ta Kasar
Published: 13th, March 2025 GMT
Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar.
Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya.
A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, “ba zai yuwu mu mayar da hankali sosai kan yanayin kasuwar hannayen jari ba.” A martaninsu, kaso 86.7 na wadanda suka bayar da amsa cikin nazarin, sun yi imanin cewa, wannan wani yunkuri na rage mummunan tasirin da manufofinsa na haraji suka haifar kan kasuwar hannayen jari ta kasar. Har ila yau ba da jimawa ba, shugaba Trump ya sanar da karin haraji kan kayayyakin karafa da gorar ruwa da kasar Canada ke kai wa Amurka, inda ya kara harajin zuwa kaso 50 bisa dari, lamarin da ya kara hargitsa kasuwar hannayen jarin. Don gane da hakan, kaso 86.8 na masu bayar da amsa sun yi ammana cewa, faduwar darajar hannayen jari da aka samu a baya bayan nan a Amurka, ta nuna rashin kwarin gwiwa mai tsanani dake akwai a kasuwar zuba jari a tattalin arzikin Amurka, inda ake kara damuwa cewa, durkushewar kasuwar hannayen jarin ka iya tasiri kan kasuwanni duniya da rage kwarin gwiwa a duniya baki daya.
Nazarin ya gudana ne a dandamalin kafar CGTN na harsunan Ingilishi da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 7,875 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasuwar hannayen jari ta kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp