2025-04-15@04:22:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 25
«kasuwar hannayen jari ta kasar»:
Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga ɓangaren zantarwa na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri Hakan dai ya ci karo da yadda aka yi hasashe a lokacin da aka kaddamar da ’yan majalisar su sama da 460 domin fara aikinsu na wakilcin ’yan Nijeriya sama da miliyan 230 a...
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta. Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa. Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa Jannatul Firdaus, ta zama makoma ga Galadima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace. Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi. Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi. Shugaban...
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
A gun taron manema labarai na musamman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Talata, jami’ai masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, yayin da manufofi da matakai daban daban na fadada kashe kudi ke ci gaba da yin tasiri a bana, kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin baki daya, sun ci gaba da nuna yanayin bunkasa bisa daidaito. Jami’an sun kuma ce ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta inganta ayyuka na musamman don bunkasa kashe kudi, da gudanar da ayyuka a fannoni hudu, wato inganta yadda ake amfani da kayayyaki, da fadada amfani da hidimomi, da samar da gajiya daga sabbin kayayyaki, da kuma kirkirar sabbin yanayin cimma gajiya. Ma’aikatar kasuwancin ta kuma bayyana cewa,...

Fashewar Tankar Man Fetur: Rundunar ‘Yansanda Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 6, Motoci 14 Sun Kone A Abuja.
Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, rundunar ta yi matukar jimamin hatsarin motar da ya afku a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin karfe 6:58 na yamma kafin gadar Nyanya. Ta kuma ce, ofishin hukumar na Karu ya samu...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya. Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba. A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa,...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...

Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Da CGTN Ta Gudanar Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Diflomasiyyar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar da take yaki da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya zagon kasa, ta yi wa tsohuwar ministar harkokin mata Uju Kennedy,tambayoyi masu alaka da zargin da ake yi mata akan aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da wasu kudade da sun kai Naira miliyan 138.4 a karkashin kasafin kudin ma’aikatar tata a 2023. Da safiyar jiya Alhamis da misali 11: na safe ne tsohuwar ministar ta isa babbar shalkwarar hukumar ta EFCC dake birnin Abuja,inda ta amsa tambayoyin da aka yi mata. Majiyar hukumar ta EFCC ta ce da akwai wasu kudade da aka bai wa ma’aikatar a karkashin shirin nan na p-Bat cares, amma sai aka karkata su zuwa asusun tsohuwar ministar. Uju tana cikin minsitocin da ...
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai muka tuna da fim dinsu na Badakala (wanda wani jarumi Bashir Mudi Yakasai ya shirya), inda suka yi fim mai dauke da rawa da waka na farko a cikin fina-finan Hausa,wato a shekarar 1997 wannan fim ya daga abinda yanzu ake kira Hausa Afropop, domin shi ne wakar fina-finan Hausa ta farko da aka kai wa Rabi’u BK a kasuwar Kofar Wambai domin sayar da...
“A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56. Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949). Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960). Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021). Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...