Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule.

Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar.

Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su, domin tabbatar da sahihanci da ingancin aikin jarida.

Da yake ƙarin bayani, ya ce gwamnatin Abdullahi Sule ta kawo sauye-sauye masu amfani, musamman wajen inganta harkar haƙar ma’adinai a jihar.

Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ce ke kan gaba a Naieriya wajen samar da ma’adinan Lithium, wanda ke amfani ga ci gaban tattalin arziƙi.

A nasa jawabin, Shugaban ‘Yan Jarida na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya sabon Sakataren Gwamnatin Jihar murna bisa naɗin da aka yi masa.

Ya ce naɗin da aka yi wa Labaran Shuaibu Magaji ya dace da shi, kuma ‘yan jarida ba su yi mamaki ba duba da irin tarihin ayyukansa.

Haka kuma, ya roƙi Sakataren Gwamnatin da ya haɗa su cikin harkokin yaɗa labarai na gwamnati, musamman a ɓangaren tallafa wa ayyukansu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Jarida Nasarawa Sakataren gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto

Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

 

Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar
  • Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Wajen Inganta Noma, Sufuri Da Ma’adanai 
  • Wata Miyar Sai A Makwabta…
  • Gwamnatin Bahrain Ta Kara Kaimi Wajen Kama Yan Adawa Daga Ciki Har Da Yara Kanana
  • Gwamna Buni Ya Naɗa Matasa 200 A Matsayin Hadimansa
  • Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa
  • Araghchi: Gwamnatin Amurka ta haramta wa Irakawa samun wutar lantarki
  • Iran ta soki matakin Amurka na hana shigar da wutar lantarki Iraki
  • Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto