2025-03-13@17:14:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1449

«Sakataren gwamnati»:

    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau , shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano. Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar. Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu —...
    Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin...
    Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce galibin ’yan Najeriya suna sha’awar yin amfani da muƙaman gwamnati ne kawai don arzuta kansu da abokan hulɗarsu su durƙusar da ƙasar fiye da yadda suka same ta. Tsohon Shugaban ƙasar ya ce waɗannan mutane suna karɓar rancen biliyoyin Nairori, suna ganin cewa biyan kuɗaɗen gwamnati bayan an...
    Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kulla haɗin gwiwa mai muhimmanci da Jami’ar Azman domin faɗaɗa damar ilimi da inganta ci gaban al’ummar jihar. An bayyana hakan ne lokacin da shugabannin Jami’ar Azman, karkashin jagorancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Fatima Batul Mukhtar, suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a Fadar Gwamnati da ke Dutse....
    Babban Rajistara na Sashen kula da lafiyar Koda a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga, ya yi kira ga jama’a da su kula da lafiyarsu domin kaucewa kamuwa da cututtukan koda. Ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe yayin bikin Ranar Koda ta Duniya. Dr. Fidelis Linga ya jaddada...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya...
    Yara mata kimanin 74,452 ne suka amfana da tallafin kudi karkashin shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) a kananan hukumomi 19 na jihar Kano, wanda ya kunshi rukuni na farko da na biyu. AGILE wani shiri ne na Bankin Duniya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wanda aka kirkira don...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu. Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin...
    Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da rukuni na farko na jami’an tsaro karkashin shirin Safe Schools Initiative na Jihar Jigawa. Taron, wanda kuma ya kasance  bikin kammala horo ga masu tsaron, an gudanar da shi ne a sansanin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Panisau, a Dutse. Wannan...
    Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule. Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar. Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su,...
    Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi. Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari. El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan...
    ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon shinkafa da sauran kayayyaki ga gidaje sama da 30,000 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar.   Da yake kaddamar da rabon a Sokoto, Sanata Tambuwal ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake ganin watan Azumin Ramadan tare da tabbatar...
    Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma.   Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi.   Guguwar ruwan sama ta yi...
    Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi.   A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da...
    Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan.   Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya...
    Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha.     A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara.   Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar.   A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.   A wata sanarwa da mai magana da yawun...
    Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa.   Gwamnan, ya ba da umarnin...
    Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki. Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU:...
    Wannan magana tana nuni da cewa idan mutum ya nemi kariya a wurin Allah da zuciya ɗaya, to Allah zai amsa roƙonsa kuma zai kare shi daga duk wani abu mai cutarwa. Wannan yana da asali a cikin koyarwar Musulunci, inda ake koyar da Musulumi su nemi tsari wurin Allah kaɗai daga sharrin Shaiɗanun aljanu...
    Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd yayin da suke ƙasar Sin.   Tang Zhangwei, ya jagoranci wasu kamfanoni zuwa jihar Zamfara, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu...
    Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton...
    Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan...
    Ganin halin da fasinjojin ke ciki, sojojin suka yi kukan kura kan yan ta’addan, inda hakan ya tilasta suka saki fasinjojin da suke yunkurin garkuwa dasu tare da arcewa zuwa cikin daji.   Hakan ya sanya Sojojin kutsa kai cikin dajin domin farautar yan ta’addan, al’amarin da ya basu nasarar halaka wasu yan ta’adda da...
    Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda...
    Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci zafin rana mai tsanani a kwanaki masu zuwa, a wasu yankuna na Najeriya. A cewar NiMet, jihohin da za su fi fuskantar wannan yanayi sun haɗa da Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, Benuwai, Enugu, Anambra, Abiya, Ebonyi, Kuros Riba da Babban...
    Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro...
    Wani jami’an gwamnatin kasar UAE ne zai isar da sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghani ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara na kasar UAE Anwar...
    Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy...
    Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara...
    Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967. Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto...
    “Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.   “Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari. A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin....
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani...
    Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa,...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya,...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen...
    Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa...
    Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da...