Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Rukuni Na Farko Na Masu Tsaron Makarantu
Published: 13th, March 2025 GMT
Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da rukuni na farko na jami’an tsaro karkashin shirin Safe Schools Initiative na Jihar Jigawa.
Taron, wanda kuma ya kasance bikin kammala horo ga masu tsaron, an gudanar da shi ne a sansanin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Panisau, a Dutse.
Wannan shiri, wanda shi ne irin sa na farko a ƙasar, an kirkireshi ne domin kare makarantu, da asibitoci, da kotuna, da wuraren samar da ruwa a fadin jihar, inda aka dauki ma’aikata 9,974 don aiwatar da wannan aiki.
Za a tura Jami’an tsaron ne karkashin kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da aka rarraba zuwa mazabun yan majalisun dattawa.
Kamfanonin tsaron sun hada da Kare-Kallo a Jigawa ta Tsakiya, sai JIMAD a Jigawa ta Arewa maso Yamma, da Corporate Security a Jigawa ta Arewa maso Gabas.
Wadanda aka dauka sun fito daga sassan jihar daban-daban na jihar, kuma sun hada da masu shaidar karatu ta digiri, da NCE, da difloma, kuma za su yi aiki ne a yankunansu.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kare kayayyakin more rayuwa da tabbatar da dorewar su.
“Wannan shiri an kirkireshi ne domin kare jarin da aka zuba a wadannan gine-gine na jama’a. Mun sha ganin yadda barayi ke lalata wadannan gine-gine, suna satar tagogi, kujeru, da sauran kayayyaki masu muhimmanci. A matsayina na shugaba mai kishin al’umma, mun dauki matakan dakile wannan matsala,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa wannan shiri ba wai tsaro kadai yake bayarwa ba, har da samar da ayyukan yi.
“Baya ga kare kadarorin gwamnati, wannan shiri kuma wata dama ce ta samar da aikin yi ga matasa. Kowane daya daga cikin mutum 9,974 da aka dauka daga yankunansu zai tabbatar da tsaron gine-ginen da ke yankinsa.”
Ya bukaci al’ummar yankunan da su baiwa jami’an tsaron hadin kai, yana mai cewa:
“A hakika, yakamata al’ummomi su rika kula da tsaron wadannan gine-gine da kansu, amma wannan shiri yana samar da tsari mai kyau na tsaro da ya dogara da al’ummar da ke yankunan.”
Da yake yi wa sabbin jami’an tsaron jawabi, ya bukace su da su yi aiki da gaskiya da rikon amana, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da shirin inganta jin dadinsu.
“Kayan da kuke sawa alamar iko ne don kare al’umma, ba don tsoratar da su ba. Gwamnati ta ware sama da Naira biliyan 3.4 duk shekara domin aiwatar da wannan shiri, abin da ke nuna muhimmancinsa ga jihar.”
Ya bukaci kamfanonin tsaro da ke kula da jami’an da su kula da jin dadinsu, kuma ya roki shugabannin kananan hukumomi da su bada hadin kai don tabbatar da nasarar shirin.
“Muna da yarjejeniya kan albashi mai kyau da adalci ga jami’an tsaro. Muna bukatar a kula da su yadda ya kamata, a biya su akan lokaci, sannan a basu kulawa da horo da ya dace domin tabbatar da ingancin tsaro.”
Gwamna Namadi ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na karfafa matasa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Makarantu Jigawa jami an tsaro wannan shiri tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba —Ganduje
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta.
A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa.
“Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo ne don girmama tsohon shugaban kasa kuma mu sanar da shi nasarorin da babbar jam’iyyarmu ta samu tun bayan saukarsa daga mulki. Mun tabbatar masa da cewa za mu ci gaba da sanar da shi ina aka kwana akai-akai game da halin da ake ciki,” in ji Ganduje.
Game da ziyarar Atiku ga Buhari, wadda ake gani a matsayin yiwuwar haɗewarsu a siyasa, Ganduje ya yi watsi da ita a matsayin mara muhimmanci.
“Wannan ziyarar ba ta dame mu ba. Ƙoƙari ne maimaita tarihi amma abin da suke nema ba zai yiwu ba. Abin da suke kokarin ginawa ba shi da tushe. Wasu ɓangarorin ba za su taɓa iya haɗuwa ba,” in ji shi.
Ko da yake ya ki yin ƙarin bayani, Amma ya yi nuni da cewa a shirye APC take don dakile duk wani yunkurin ’yan adawa, ko da yake bai yi ƙarin bayani ba.
Ganduje ya ce, “Ba za mu bayyana shirinmu ba, amma mun riga mun shirya musu. Nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu yana ƙara karfafa jam’iyyar,” in ji shi.
Ganduje ya kuma jaddada burin APC na karɓe fiye da jihohi 21 da take mulki a halin yanzu, yana mai bayyana ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar za ta samu karin jihohi ta hanyar sauya sheka ko zaɓe mai zuwa.
“Wasu gwamnoni za su iya dawowa cikinmu, ko kuma mu kayar da su a zaɓe. Ko ma mene ne dai, muna faɗaɗa mulkinmu. Muna gamsu da inda muke, amma ba za mu tsaya a iya nan ba.”
Da yake tsokaci kan sauya shekar da wasu kusoshin APC suka yi a kwanan nan da kuma rikicin cikin gida na jam’iyyar, Ganduje ya tabbatar da cewa tafiyarsu ba ta da wani tasiri mai yawa.
“Manyan mutane daga wasu jam’iyyu suna dawowa APC. ’Yan ƙalilan da suka tafi kuma babu wata illa ta a-zo-a-gani da za sai yi,” in ji shi.
Dangane da sukar da ake yi kan zargin gwmanatin Tinubu da nuna bangaranci a rabon muƙamai, Ganduje ya dage cewa ana raba mukamai daidai kuma jam’iyyar na tattara bayanai don tabbatar da adalci.
Ya ce, “Muna tara alƙaluman nadin mukamai don nuna cewa babu nuna bambanci a nadin mukaman shugaban kasa,” in ji shi.
Kalaman Ganduje na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da cukumurdar siyasa gabanin babban zaben 2027, inda jam’iyyun masu mulki da na adawa ke neman karfafa kawance da kuma sake dabaru.