2025-04-14@17:23:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1033
«Jami an Tsaro Makarantu»:
Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar...
’Yan bindiga sun kashe mutane arba’in a wani hari suka kai a ƙauyen Zike, a yankin Kwall da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Wani shugaban al’ummar Kwall, Wakili Tongwe, ya ce maharan sun shiga ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Litinin suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna...
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an...
Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar. Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan. A wata zantawar da aya...
Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi. Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa. Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar...

Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake...

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu...
Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano,...
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas. “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20. “Taron mai...
Gwamnatin Amurka ta sanar da janye sabon harajin da ta ƙaƙaba wa kayayyakin laturoni irin su wayoyin salula, kwamfutoci da sauran na’urorin da ake shigo mata daga ƙetare. Ana sa ran matakin ya rage raɗaɗin tashin farashin kayayyakin da zai faru a Amurka bayan da a kwanaki Shugaba Donald Trump ya lafta wa ƙasashe ciki...

Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan...
Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International” ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan...
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya...
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin...
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh...
Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar. Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar. An kashe ƙasurgumin...
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin...
Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar...
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar sakandare a fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse. A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar...
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana...
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda...

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji. Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu. Da...
Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin...
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon...
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan. Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis. Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala...
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar. Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar...
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya...

Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu. Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a...
Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta. An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar. Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar. ...
Sama da gidaje dari biyu da arba’in ne aka lalata a daren Talatar da ta gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana yi a unguwar Garin Kestu Atuwo dake karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi. Da yake jajantawa wadanda abin ya shafa, Gwamna Nasir Idris ya shawarci gidajen da...
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan...
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
Wani muhimmin abun lura ma shi ne ita kanta Amurka ba za ta tsira daga mummunan tasirin wannan yaki na cinikayya da take rura wutarsa ba. Ko shakka babu matakin zai haifarwa Amurka matukar koma bayan tattalin arziki, da hauhawar farashi a cikin gida, da dakile guraben ayyukan yi da sauransu. Tuni ma kasuwannin Amurkan...
Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar. Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar. Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji...
Ƙungiyar Ƙwadago a Jihar Sakkwato (NLC), ta musanta iƙirarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), Ali Kankara, ya yi cewa gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba. Shugaban NLC na jihar, Kwamared Aliyu Abdullahi, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa Gwamnatin Sakkwato...
Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin...
Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu. Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan...
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke...
A sa’i daya kuma, mambobin kungiyar WTO sun jaddada cewa, za su nuna goyon bayansu ga kungiyar WTO don ta ba da gudummawa kamar yadda ake fatan gani, kana suka yi kira ga dukkanin mambobi da su warware sabanin dake tsakaninsu bisa ka’idojin kungiyar ta WTO. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta...
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...