’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3
Published: 14th, March 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai hari tare da tarwatsa mazauna ƙauyuka biyar da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sonudazuwa, Tsauni Dodo, da Dandauka.
Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — ObasanjoWani jagoran al’umma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki sansanin Fulani da ke Kubuwo, inda suka sace matasan makiyaya uku.
Sun kai harin ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 6 na yamma.
Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar sun isa ƙauyukan suna harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.
“’Yan bindigar sun shigo suna harbi ta ko ina. Mutane suka riƙa gudu don tsira da rayukansu,” in ji wani jagora.
“Sannan sun sace matasa uku a sansanin Fulani, suka tafi da su cikin daji.”
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tserewa wani farmaki da sojoji suka kai musu a dajin Kurutu-Azara, wanda ke iyaka da Ƙaramar Hukumar Kagarko.
Ya ce a kan hanyarsu ta tserewa ne, suka farmaki ƙauyukan da ke hanyarsu.
A yayin harin, ’yan bindigar sun ƙone mota da babur a Unguwan Tauka.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, “An ƙone wa wani mutum mota sabuwa da ya sayo a Kaduna. Yana kan hanyar shigowa garin ne sai ya hango ’yan bindigar.
“Nan take ya fice daga motar ya tsere, suna ganin motar suma cinna mata wuta suka ƙone motar da wani babur.”
Wani ɗan banga daga cikin ƙauyukan da aka kai wa harin ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bin sahun ’yan bindigar.
Rundunar ’yan sandan yankin ta tabbatar da harin, amma ta ce za a tuntuɓi hedikwatar ’yan sandan m Kaduna don ƙarin bayani.
Sai dai kakakin rundunar, ASP Hassan Mansur, bai samu damar yin tsokaci kan harin ba lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa hari Ƙauyuka Ƙonewa yan bindigar sun bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin.
Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike“Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar.
Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna, sannan suka yi musayar wuta da su.
DSP Sadiq, ya ce babu wanda ya ji rauni daga cikin waɗanda aka kuɓutar, kuma jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da wasu dabbobin da maharan suka sace.