Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
Published: 14th, March 2025 GMT
Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+.
Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu.
Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.
Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk da takuntuman kasar Amurka, sai da karkashin shugaban kasar Amurka Donald Trump, na sabunta kokarinta.
Sauran Man na biyu na fitowa ne daga Nijeriya, inda yawan Man da take fitawa ya karu kuma yawan bukatarsa a cikin gida ta karu saboda samar da Matatar Mai ta Dangote.
Hakazalika, bincken na kafar Reuters, ya gano cewa, yawan Man da manyan kasasshe biyu da suke a cikin kungiyar OPEC wato Saudi Arabia da Irak, na su ya ragu, inda a yanzu suke hako kasa da wanda OPEC+ ta sanya masu su hako.
A cewar nazarin, man da kasashe mambobin kungiyar OPEC suka fitar a watan Fabrairun 2025 ya karu, inda Iran ke kan gaba, duk da kokarin da kasar Amurka ta yi na yunkurin dakile fitar da man.
To sai dai a ranar Litinin, ta yanke shawarar dakatar da shirin nata, inda take sa ran kara yawan man da take hakowa a watan Afrilu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yawan Man da
এছাড়াও পড়ুন:
Abubuwa Da Yawa Na Faruwa Ba Tare Da Sanin Tinubu Ba – Tsohon Ma’aikacin Aso Rock
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp