2025-03-14@17:16:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 21
«yawan Man da»:
Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+. Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu. Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.30, wannan ya kai daidai na alkaluman watan Satumba, wanda ya haura tun a 2018. Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk...
Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya. Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba. Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma...
Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna: Muhimmancin sadaka na da yawa baya ga kariya da take yi, sadaka tana hana bambancin da ake yi tsakanin mai kudi da kuma talaka, sadaka tana hada kan al’umma musulmi guri daya, tana taimakawa marayu, masu takaba da manya wadanda suka manyanta wajen nuna musu cewar suma suna da gata, tana kuma kusanto mutum da Allah ta’alla. Wadanda ya kamata a bawa sadaka; Marayu, iyalai masu karamin karfi, masu takaba, ‘yan gudun hijra, dalibai da sauransu. Hanyoyin bada sadaka na da dumbin yawa kamar; bada sadaka ta hanyar bada kudi, yinta ta hanyar dauke abu daga kan hanya wanda zai cutar da dan’Adam, hada kungiya ko kirkirar kungiya ko bada gudunmawa a kungiyar...
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu. Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris. NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa SP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47. Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da...
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma. Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar. Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau. Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran masu bukata ta...
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...
A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC + za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna cewa kungiyar OPEC + bata kara yawan man da take haka ba na lokaci mai tsawo, amma a halin yanzu zata kara kamar yadda aka sanar. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana rage ganga miliyon 5.85 wanda kuma shi ne kashi 5.7% na yawan man da ake haka a duniya, wannan kuma ya yi dai dai da shawarar da OPEC + suka dauka tun shekara...
Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana sayar da kwando daya na tumatir a kan Naira 3,500, yayin da ake sayar da babban kwando a kan Naira 10,000. 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda Wani manomin tumatir, Isah Bello Abba ya bayyana cewa, wannan yanayi ya sa manoma cikin fargaba saboda sun kashe kudade masu...

Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka. An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata ya zarce dala miliyan 7, inda fim din ya zama mafi shahara a matakin koli da Sin ta gabatar a karshen makon a Amurka. An ce, an fara nuna wannan fim a gidajen sinima 770 dake arewacin Amurka daga ranar 14 ga watan nan da muke ciki, a matsayin fim din da Sin ta gabatar, kana yawan kudin da...
Shekara guda bayan da Hukumar Zabe (INEC) ta dakatar da sake zaben mazabar Tsanyawa da Kunci a Majalisar Dokokin Jihar Kano, yankin ya ci gaba da zama babu zaɓaɓɓen wakili da yake wakiltar su a Majalisar Dokokin jihar. Hukumar Zabe ta Ƙasa ta dakatar da sake zaɓen ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2024, bayan da wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ce suka tarwatsa sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe da dama a kananan hukumomin biyu. Yadda za a yaƙi talauci a Arewa maso Gabas — Shettima Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 a Borno A shekarar 2023 ce Kotun Daukaka kara ta soke zaben dan Majalisar Dokoki na Jam’iyyar APC mai wakiltar...

Kasuwannin Kayayyakin Da Ake Yawan Sayen Su A Lokacin Bikin Bazara Goma Sun Inganta Kashe Kudi Sama Da Yuan Biliyan 1.6
Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6. An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don...
Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare. Kimiyya ba ta da iyaka. Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin...
An bayyana cewa Iran ce kasar ta 10 a duniya wajen samar da wutar lantarki, da yawan megawati dubu 94 da 846. Manajan da yake kula da tsara manyan ayyuka a ma’aikatar makamashi ta Iran, Behruz Muradi ya bayyana cewa, shekru 46 da su ka gabata, wato a lokacin juyin juya halin musulunci, yawan megawatin da Iran take samarwa ya yi kasa da wanda ake da shi a yanzu har sau hudu. Manajan ya kuma kara da cewa wutar lantarki da ake da ita a Iran da karfin tsarin da take da shi, tana taka rawa mai muhimmanci wajen gina tattalin arzikin kasar. Haka nan kuma ya ce, da akwai kyakkyawan tsarin da ake da shi ya samar da cigaba...
Amurka Ta Tasa Keyar Indiyawa Kusan 100 Zuwa Gida
Babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Burgediya Janar Hussain Salami ya bayyana cewa a dai dai lokacinda manya-manyan kasashen duniya suke amfani da takunkuman tattalin arziki, mafi muni a kan wasu kasashe, a lokacin ne kuma, dakarun IRGC suke yunkuri don kare kammu daga makiya. Sannan samar da ci gaban da muke bukata don kawukammiu daga cikin gida. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Salami yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, JMI ta na samun ci gaba duk tare da matsin lambar da ta take ciki. Kuma zata kara karfin sojojinta, don kare kanta daga duk wata kasa wacce teka barazana ga cibiyoyon Nukliyar kasar ko kuma tana son ta maida...
Bisa bayanan da aka samu daga wani dandali na shafin intanet, ya zuwa yau Talata, jimillar kudaden shiga da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a gidajen sinima a shekarar 2025 ta zarce kudin Sin yuan biliyan 11, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.5. Bugu da kari, adadin masu kallo a lokacin bikin bazara na shekarar 2025 ya zarce miliyan 170, wanda ya karya tarihin baya na yawan masu kallo da aka taba samu lokacin bikin bazara, a tarihin fina-finan kasar Sin. Har ila yau, bisa la’akari da yawan tikitin da aka sayar a shekarar 2025, yawan kallon fina-finan kasar Sin ya zarce na Arewacin Amurka, inda a halin yanzu ya zama na daya a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza...
Masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta kafa wani sabon tarihi a hutun bikin bazarar 2025, inda daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga Fabrairu, kudaden da aka samu daga kallon fina-finai ya kai biliyan 5.75 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 802, wanda ya zarce mafi yawan kudin da aka samu a baya na yuan biliyan 5.73 a shekarar 2021. Wannan adadi shi ne mafi yawan kudi da aka samu daga kallon fina-finai a lokacin bikin bazara a tarihin sinima ta kasar, kuma ya tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa jagora wajen samun mafi yawan kudade daga kallon fina-finai wato box office a shekarar 2025, wanda ya zarce Arewacin Amurka. Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji...
Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.55, shekaru 8 a jere ke nan ana samun wannan ci gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta kori wani jami’in sa-kai, Ado Abba, bisa zargin gudanar da bincike ba bisa ƙa’ida ba da kuma karɓar kudin haram daga jama’a. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ake ganin korarren jami’in tsaye a gefensa domin tabbatar da an san shi. SP Kiyawa ya ce bayan ƙorafin da aka samu, bincike ya tabbatar da laifin jami’in, don haka an kore shi daga aiki kuma ba shi da wata alaka da rundunar. Zargin Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Bankawa Keken Adaidaita Sahu Wuta A Kano Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti Ya kara da cewa...
Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya sanar da cewa yanzu haka sojojin ƙasar ne ke iko da mafi yawan unguwannin birnin Goma, da ke gabashin ƙasar. Muhingo Nzangi, wanda shi ne ɗan majalisa mai wakiltar yankin ya shaida wa ƴan jarida cewa sojojin sun yi maganin ƴan tawayen M23 waɗanda MDD ta ce na samun goyon bayan Rwanda. Sai dai har yanzu ƴan tawayen na iƙirarin cewa suna iko da birnin. Wakiliyar BBC ta ce M23 na ikirarin cewa tana kokarin kare tsirarun ƴan ƙabilar Hutu ne waɗanda ake ci wa zarafi, kuma wannan lamari ne da Rwanda take goyon baya, sai dai ta ce ba ta tsoma hannu kai-tsaye cikin rikicin ba duk kuwa da cewa Majalisar...