Aminiya:
2025-04-14@16:50:46 GMT

Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano

Published: 17th, March 2025 GMT

Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu.

Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano.

Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Aminiya ta ruwaito cewa gabanin wannan sabon naɗin, Ibrahim Yakubu Adamu shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano KNUPDA.

Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da sabon Kwamishinan da aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano.

Da yake jawabi, Gwamnan ya yaba wa sabon kwamishinan wanda ya ba da shaida kan ƙwazo da kuma ƙwarewa haɗi da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban birnin na Dabo.

Gwamnan ya buga misali da yadda sabon kwamishinan ya jagoranci aikin tsarawa da kuma bunƙasa rukunin gidajen nan na Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo waɗanda aka gina a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 a zamanin gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sabon kwamshinan wanda ƙwararren mai zana gine-gine ne, Gwamnan ya hikaito yadda ya taka rawar gani wajen tsarawa da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan gine-gine a lokacin da yake Kwamishinan Ayyuka da Gidaje a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

A wani labarin mai nasaba da wannan, Gwamnan ya umarci duk waɗanda suka mallaki gida a rukunin gidaje na Kwankwasiyya ko Amana ko Bandirawo da su tabbatar sun tare nan da watanni uku ko kuma su sanya ’yan haya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ibrahim Yakubu Adamu Kwamishinan Bunƙasa Gidaje da sabon Kwamishinan

এছাড়াও পড়ুন:

Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari

Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.

 Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa  lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance  wajen asibiti.

Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.

Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.

 Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina
  • Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato 
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza
  • ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
  • HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji