2025-03-17@22:01:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1803
«Kwamishinan Bunƙasa Gidaje»:
“Dole ne mu ci gaba da bunkasa jiharmu, kuma an gina wadannan gidajen ne don habaka jiharmu. “Ga dukkan masu gidaje da ke wadannan jerin gidaje, ina sanar da su a fili, ko dai su koma wuraren da zama ko kuma a kwace,” in ji Gwamna Yusuf. Ya kuma bukaci wadanda ba za...
Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa. Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa. Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano Ana zargin...
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu. Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano. Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri...
Wasu manyan jami’an kasar Habasha sun bayyana cewa, layin dogon da ya sada tsakanin kasar Habasha da Djibouti da kasar Sin ta gina, yana kara inganta bangaren hada-hadar kayayyaki na kasar Habasha, kana ya zama wani muhimmin ginshiki da ke taimaka wa cinikayyar shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje a kasar....
Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a...
Al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin ganganmi a fadin kasar, inda suka lashi takobin tinkarar ta’addancin Amurka ta hanyar kara karfin soji, da hada karfi da karfe, da kuma abokan gaba shakat. Gangamin ya zo ne bayan da jagoran gwagwarmayar kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa kasar a shirye ta ke...
Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa. Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare...
Rundunar sojojin kasar Sudan (SAF) ta sanar da cewa, dakarunta sun samu ci gaba sosai a yakin da suke yi a babban birnin kasar Khartoum. Mai magana da yawun rundunar sojin ta SAF, Nabil Abdalla ne ya fito fili ya bayyana cewa “Dakarunmu sun samu ci gaba sosai a tsakiyar birnin Khartoum.” Sai dai kuma...
Iran ta bayyana anniyarta ta yin hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran “na maida hankali” wajen hada kai da hukumar ta IAEA. A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gharibabadi ya yaba da tattaunawa mai ma’ana” da...
“Za a lika sunayen tare da albashin ma’aikata a wurare masu mahimmanci a cikin harabar ma’aikatu, ofisoshin gwamnati da sakatariyar kananan hukumomi 44 na jihar don sauƙaƙe aikin,” in ji Faruk. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada....
Sai dai hukumar yankin Taiwan na ci gaba da kokarin yada karairayi, tare da tunasar da kowa kasancewarta. In ba haka ba, wadannan bayanai masu kunshe da kurakurai da muka ambata ba za su bayyana a kan wata jaridar Najeriya ba. Hakika, a shekarun nan, hukumar Taiwan ta yi ta kokarin takala da batun neman...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya...
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa. Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu. Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi A...
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin tuntuɓar takwaransa na Rasha Vladimir Putin da zummar tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine. Trump ya shaida wa manema labarai hakan a cikin jirgin shugaban ƙasa na Airforce One a kan hanyarsa ta zuwa Washington daga Florida cewa yana ƙoƙarin ganin cewa yaƙin ya zo ƙarshe. Madalla...
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Legas na jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya sanar da koma wa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sanarwar ta zo ne bayan kwanaki biyu kacal da ya fice daga jam’iyyar PDP. Jandor ya ba da sanarwar koma wa jam’iyyar APC ne a wani...
Wasa wasa dai Musulunci na dawowa gidansa wato Nijeriya ta Arewa ta hanyoyi iri-iri. Ba dai sai an nanata ba. Arewacin Nijeriya da ma sassa da dama a jamhuriyar Nijar da Ghana har ya zawa Senegal sassa ne na Musulunci inda ƴan mulkin mallaka na Ingila da Faransa suka yi iyakar ƙoƙarin su rusa shi....
A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili...
Kasar Yemen ta sanar da cewa Amurka da ta sake kai wasu hare-haren a gundumar Hudaidah akan wani kamfani na auduga. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar Ansarullah ta kasar Yemen din tana cewa; Sojojin na Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami har 18 akan jiragen ruwa na dakon jiragen...
A daren ranar Lahadi Barcelona ta buga wasa mafi kayatarwa a wannan kakar wasanni ta bana bayan ta doke abokiyar karawarta Athletico Madrid duk da cewar Athletico din ta jefa kwallaye biyu a ragar Barcelona a minti 70 na wasan. A kokarin da take yi na sake darewa kan teburin Laliga, Barcelona ta zura kwallaye...
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz...
Sojojin HKI sun ci gaba da keta hurumin yarjeniyan tsagaita budewa juna wata tsakaninta da Gaza inda a jiya Lahadi kadai ta kashe Falasdinwa 14 a wurare daban daban a yankin. Tashar talabijin ta Almayadden ta kasar Lebanon ta bayyana cewa yawan shahidai a kan tafarkin Kudus a Gaza ya kai 48,872 da kuma wadanda...
Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan...
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kukan rashin aikin yi da a ko da yaushe ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, waɗanda za su cike guraben ayyukan ne suka yi ƙaranci a Najeriya. Alƙaluma na ci gaba da bayyana dubban ‘yan...
Mataki na Uku: Kare kai daga shubuha; wato matakin tsantseni, shubuha na nufin abubuwan da ba a tabbatar da halacci ko haramcinsu ba. Akwai wani mataki da ya fi kauce wa haram, wato kauce wa abubuwan da ke da shakku. Annabi (SAW) ya ce: ” Lalle halal a bayyane take, kuma lalle haram a bayyane...
Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu. Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu. An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a...

Ministan Noma Na Gambiya: Hadin Kan Gambiya Da Sin A Fannin Aikin Gona Ya Haifar Da Sakamako Mai Kyau
Ministan noma na kasar Gambiya Demba Sabally ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona na Gambiya a shekarun baya-bayan nan. Ministan ya ce, yawan amfanin gona da kasar ta...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan...
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na kunshe cikin wata ’yar takaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool...
Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen...
Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama a daren jiya Asabar. Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai kan wasu unguwanni a Sanaa babban...
An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru...
An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru...

Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya
Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin mayar da Filin Idi na Ƙofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa don Harkokin Addinin Musulunci. Sabuwar cibiyar za ta zama wajen gudanar da taruka da karatuttukan addini maimakon barin filin ana amfani da shi sau biyu a shekara don Sallar Idi. HOTUNA: NDLEA...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta...
Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma...
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA Mahaifiyar...
Mai Martaba Sarkin Kauru dake Jihar Kaduna Alhaji Zakari Ya’u Usman ya bukaci samun hadin kai da aiki tare kana da hakuri da juna tare da ɗaukar banbance banbance dake tsakanin al’umma a matsayin wata baiwa. Alhaji Zakari Ya’u II yayi wannan horonne lokacin da aka taru a fadarsa dake Kauru domin shan ruwan...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa...
Gwamnatin da kuma mutanen kasar Somalia sun ki amincewa da shawarar shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa a Gaza zuwa kasar Somalia. Shafin yanar Gizo na ‘Africa News’ ya nakalto yan kasar Somalia da dama suna fadar cewa yan kasar da kuma gwamnati ba zasu amince da korar Falasdinawa a Gaza, zuwa kasar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na...

Ma’aikatar Harkokin Wajen JMI Ta Yi Allawadai Da Kungiyar G7 Wacce Ta Zargin Kasar Da Abubuwa Da Dama
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin...