Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi
Published: 22nd, March 2025 GMT
Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa, daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yin jana’iza.
Kakakin ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna samun labarin lamarin, jami’ansu suka fara bincike, musamman a wajen POS da ke kusa da inda aka nemi a biya kuɗin fansar.
A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka, wanda lambar wayarsa aka yi amfani da ita wajen kira mahaifin yaron.
Sun kuma gano asusun bankin da aka bayar don a biya kuɗin fansar.
Da aka tambayi Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozoichikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yin garkuwa da yaron.
Sannan ya ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi) mai shekara 25 da Musa Usman (Kala) mai shekara 30, dukkaninsu daga ƙauyen Leka.
A halin yanzu, ‘yansanda sun tsare waɗanda ake zargi, kuma ana zurfafa bincike a sashen manyan laifuka (SCID).
Kwamishinan ‘yansandan Bauchi ya tabbatar da cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an yi adalci.
Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai da kuma sanar da ‘yansanda duk wani abu da suke zargi a layin gaggawa na 112 ko Police Control Room a lamba 08156814656.
Rundunar ‘yansandan Bauchi ta jaddada cewa tana nan daram domin kare rayuka da dukiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yansanda Garkuwa Yaro mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Karin Sinawa Suna Son Kashe Kudi
A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da biliyan 373 da miliyan 100, karuwar da ta zarce zaton da aka yi.
Me ya sa karin Sinawa suke son kashe kudi? Farfesa Wang Xiaosong na kwalejin ilmin tattalin arziki na jami’ar Renmin ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, tun daga shekarar bara, tattalin arzikin Sin ya samu karuwa, kudin shiga na jama’ar kasar shi ma ya karu, lamarin da ya zama silan karuwar kudi da ake kashewa. Kana gwamnatin kasar Sin ta gabatar da jerin matakan tallafi don sa kaimi ga fadada kashe kudi a kasar.
Kasar Sin tana da mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 400, tana daya daga cikin manyan kasuwanni na duniya. Kamfanin McKinsey ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2030, mazaunan biranen kasar Sin za su sa kaimi ga karuwar kashe kudi ta duniya da kashi 91 cikin dari, biranen kasar Sin 700 za su samar da gudummawa ga karuwar kashe kudi na biranen duniya da dala triliyan 7, wanda ya kai kashi 30 cikin dari. Kashe kudi ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, ana kara kashe kudi a kasar Sin, babu shakka za a samu sabon karfin raya tattalin arzikin duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp