2025-03-25@15:02:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 521
«yaro»:

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berry ya bayyana cewa HKI tanason jawosu cikin tattaunawar diblomasiyya wanda zai kai kasar ga samar da huldar jakadanci da ita, amma mu bama tare da wannan ra’ayin. Nabih Berry ya bayyana haka ne a lokacinda yake zantawa da jaridar ‘Sharqul Awsad’ ya kuma kara da cewa a halin...
Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa...
Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su. Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai...
Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a...
Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood....
Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti...
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus ta maye gurbin Thiago Motta da tsohon...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus na shirin raba gari da mai horas da ’yan wasanta, Thiago Motta, yayin da ko kaka ɗaya bai cika ba a kwantaragin da ya ƙulla da ƙungiyar ta Italiya. A cewar Jaridar wasanni ta La Gazzetta dello da Gidan Talabijin na Sky Sport, Juventus na shirin maye gurbin Thiago Motta...
Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin. Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya Mista Fanwo...
Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake...
Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin...
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga...
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar...
Ana sa ran, za a yi jana’izarta yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin 4 na yamma (4pm) a garin Radda, ƙaramar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina. Hajiya Radda, jigo ce da za a rika tunawa da ita bisa hikima da juriya wanda hakan ya...
Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga...
Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a...
Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar...

Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa
A kwanan nan ne sakatare janar na kungiyar ASEAN Kao Kim Hourn ya bayyana a wata hirar da ya yi da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, nasarorin da Sin ta samu ta fuskar ci gaba ba sakamakon ‘siddabaru’ ba ne, illa sakamakon aiki tukuru kuma mai dorewa. Kao...
Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma. Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a...
Kamfanin dillancin labarun “Anatoli” na Turkiya ya ambato cewa; Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar Mohamed Toumba ne ya bayar da labarin cewa, mutane da dama sun kwanta dama sanadiyyar harin da su ka kai wa masu masu salla a garin Fonbita dake gundumar Kokorou. Rahotannin sun tabbatar da cewa adadin masu sallar da...
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta...
Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa. Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin...
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar...
An kuma sanar da ma’aikata masu zaman kansu da ‘yan kwangila na kasa da kasa kan dakatar da ba da tallafi. A lokaci guda kuma, an daina ba da tallafi na tarayya ga gidajen Rediyon ‘Free Asia da Rediyo Free Europe/Radio Liberty’. Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce shi da kusan dukkan ma’aikatansa 1,300...

Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama
Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kungiyar abokantaka ta inganta hakkin bil’adama, da tattaunawa da hadin gwiwa da sauransu, yayin taron MDD karo na 58 da ya gudana a jiya Alhamis. A cikin...
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci...

Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar...
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gabaci da kuma kudancin kasar Lebanon wanda yak eta yarjeniyar zaman lafiyan da HKI ta cimma da kungiyar Hizbullah mai lamba 1701 ta shekara ta 2006. Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon na cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace. Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB)...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin...
Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki. A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da ya mayar da hankali kan karfafa samar da ci gaba mai inganci, da warware tarnakin tafakkuri, da aiwatar da gyare-gyare da kirkire-kirkire, da kokarin ci gaba da azama, da daukar matakai masu inganci, da kuma kafa sabon...
Dokta Saleh ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar, yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya. Har ila yau, a buƙaci a samu haɗin gwiwa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a...
’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin...
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu. Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.” A cewarsa, hanyar da ta...
Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara...
Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a hanyar Karu zuwa Nyanya dake birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da wata mummunar gobara da ta rutsa da motoci da dama, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yammacin ranar Laraba. Har zuwa yanzu dai ba a...
Kasashen Nijar da Burkina Faso da kuma Mali kowannensu sun sanar da ficewa daga kungiyar kasashe renon faransa ta (OIF). Nijar ta sanar da ficewa daga kungiyar a ranar Litini, yayin da Mali ta bi sahu a ranar Talata, aa daidai lokacin da ake raya makon kungiyar. Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar Laouali Labo,...
Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki. A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu...