Aminiya:
2025-03-24@16:41:49 GMT

Mata sun ƙwace kasuwancin kayan lambu a Gombe

Published: 23rd, March 2025 GMT

Kallo ya koma sama bayan da mata suka karbe ragamar kasuwancin kayan lambu a a tsakiyar birnin Gombe, inda a baya kasuwancin kayan ya kasance a hannun maza kadai na tsawon lokaci.

Wannan sabon sauyi ya da ya taso a hankali ya faru ne a sakamakon matsalolin kudi da nauyin kula da kai da kuma iyali da suka tilasta matan aure da zawarawa da ma ’yan mata da dama, suka tsunduma harkar wadda a baya ake kallo a matsayin ta maza kadai a wasu yankunan Arewa.

Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi

Amma a halin yanzu a wani sashe na Babbar Kasuwar Gombe, mata sun samun damar kafa nasu kasuwancin, kuma yanzu sun fi maza yawa a ciki.

Rayuwar mata a Kasuwar Kayan Lambu

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa, mata suna zuwa kasuwa tun da misalin karfe 6 na safe domin fara kasuwanci.

Ga Hajara Adamu, wadda aka fi sani da Maman Nana, kasuwancin kayan lambu ya canza mata rayuwa. Tana da ’ya’ya tara, kuma mijinta na fama da rashin lafiya, hakan ya sa ita ce ke daukar nauyin iyalinta gaba daya.

Ta ce, “Muna bude kasuwa da karfe 6 na safe, sannan muna rufewa tsakanin 10:30 na safe zuwa 1:00 na rana.

“Haka nake samun abin da za mu ciyar da iyalinmu.” Kamar Hajara, mata da dama suna fuskantar mawuyacin hali.

“Wasunsu sun rabu da mazajensu kuma aka bar su da dawainiyar kula da ’ya’yansu su kadai, wasu kuma zawarawa ne da ba su samun wani tallafi daga gwamnati. Haka nan, akwai matasa mata da ke kokarin guje wa talauci.

Dole da kawo sauyin tunani

A baya dukansu sun kasance cikin matsin tattalin arziki, amma yanzu sun zama ginshikai wajen karfafa wa juna gwiwa da samun kyakkyawar fata, suna samun abin dogaro da kai kuma suna mamaye kasuwancin da a baya ya kasance na maza kawai.

“Dole ta sa muka canza tunani, domin wannan kasuwancin ne kawai mafitar rayuwarmu. Ba abu ne gama-gari ba a ga mata Musulmi ’yan Arewa suna sayar da kayan lambu a kasuwa, amma matsin tattalin arziki ya tilasta mana hakan.

“Ta hanyar wannan kasuwanci, muna iya ciyar da ’ya’yanmu da biyan kudin makaranta da kula da iyayenmu tsofaffi har ma da biyan kudin magani ga mazajenmu da ’ya’yanmu da ke fama da rashin lafiya. Dole ne mu gode wa Allah bisa wannan dama,” a cewar Hajara.

Yadda muka faro – Shugabar mata

A matsayinta na Shugabar Mata ’Yan Kasuwar Kayan Lambu, Hajara ta ce suna da kyakkyawar alaka da maza a kasuwar, kuma mazan sun karbe su hannu bibbiyu, har ma da tallafa musu don su samu shiga kasuwancin.

Ta ce, da farko mata da dama ba su da jari, don haka suka dogara da rance daga maza ’yan kasuwa, suna karbar kaya bashi su biya bayan sun sayar.

Amma bayan lokaci ya fara tafiya sai kasuwancinsu ya bunkasa, har ma ya kai yanzu maza sukan zo su sayi kaya daga wurinsu idan nasu ya kare.

“Maza a kasuwa suna ba mu goyon baya. Suna kare mu, kuma suna tabbatar da cewa ba a zalunce mu daga hannun kwastomomi,” in ji Hajara.

Wata mata da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce mijinta ya rabu da ita shekaru hudu da suka wuce, ya bar ta da ’ya’ya biyu.

Ta ce, “Rayuwa ta yi matukar wahala har sai da wata mata ta shigar da ni cikin wannan kasuwancin. Na fara ba tare da ko sisi ba, amma ana ba ni kayan lambu a bashi in sayar.

“Yanzu ina iya kula da ’ya’yana, har ma da taimakon wasu. Wannan kasuwanci ya dawo min da martabata.”

Matasan mata na kafa kansu

Da wannan sana’ar Malama Amina Haruna ’yar shekara 19 ta samu mafaka daga masu son cin zarafinta.

Amina, wacce ke sayar da albasa da tumatir da kabeji da karas, ta ce tana amfani da ribar da take samu wajen kula da iyayenta da ’yan uwanta da kuma bukatun kanta.

Matashiyar ta ce bayan kammala sakandare ba ta da kudin ci gaba da karatu, amma yanzu tana zuwa makarantar Islamiyya da safe kafin ta fito kasuwa.

“Ko ba komai gara in ci gaba da wannan kasuwancin fiye da dogaro da mutane da za su iya lalata rayuwata su janyo wa dangina abin kunya.

“Baya ga ciyarwa, ina sayen kaya da sabulu da sauran abubuwan bukata na gida,” in ji matashiyar. Sai dai ta ce wasu maza har yanzu na sukar irin kasuwancin da take yi da nufin su yin lalata da ita, amma “duk da haka, gara in ci gaba da kasuwancin fiye da dogaro da mutane da za su lalata rayuwata”.

Ta kara da cewa, “Ina bai wa ’yan mata shawara su nemi abin yi mai amfani da zai taimaka musu su magance matsalolinsu na kudi domin kar a ci zarafinsu.”

Haka nan, Malama Mabani Amina Abubakar, mai shekaru 22, tana taimaka wa mahaifiyarta, wacce bazawara ce, wajen kula da shagonsu.

Ta ce da farko mahaifiyarta ta ji tsoro saboda maganganun jama’a, amma daga baya ta shiga kasuwancin gadan-gadan wanda yanzu da shi suke ciyar da kansu.

“Mahaifiyata tana gida babu abin yi kuma tana fama da matsalar kudi, har sai da wata kawarta ta shawarce ta da ta shiga kasuwar kayan lambu.

“Alhamdulillah, yanzu muna samun abin dogaro da kanmu. Babbar matsalar ita ce saurin lalacewar kayan lambu,” in ji Mabani tana mai cewa dole su biya kudin kayan da suka karba kowace rana.

Nasarar mata a kasuwar

Wata uwa mai ’ya’ya biyar, Malama Balkisu Ahmed, ta ce rabuwa da mijinta ya jefa ta cikin rashin tabbas a bangaren kudi, amma a yanzu tana cikin nutsuwa kuma tana iya kula da kanta da ’ya’yanta.

Shugaban Dillalan Kayan Lambu a kasuwar, Alhaji Sani Waya, ya amince da cewa mata suna fuskantar matsaloli masu tsanani na kudi.

Ya ce, “A farko, maza ’yan kasuwa ne suka rika ba su kaya bashi, amma cikin dan lokaci da dama sun samu jarinsu da kansu.

“Yanzu ba kawai dogaro da kai suke yi ba, wasu daga cikinsu sun gina gidaje, sun sayi filaye, har ma sun sayi babura da keke mai kafa uku.

“Abin mamaki ne ganin mata sun mamaye wata sana’a ko kasuwanci a wannan kasuwa, domin ba a taba ganin haka ba a baya,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Maza dillalan kayan lambu da dama sun yarda cewa sauyin da aka samu a kasuwar ba abu ne da ba za a iya musantawa ba.

“Kasuwancin da a baya ke hannun maza kadai, yanzu yana ci gaba da bunkasa a karkashin jagorancin mata masu himma, wadanda suka tabbatar da cewa jajircewa da kokari na iya karya duk wani shinge na al’ada.

“Ina farin ciki da yadda wadannan mata suka samu ci-gaba bayan damar da muka ba su.

“Yawancinsu zawarawa ne ko kuma matan da mazajensu suka rasu, suna fama da matsin tattalin arziki,” in ji Alhaji Sani Waya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Gombe Kayan lambu wannan kasuwanci kasuwancin kayan wannan kasuwa kayan lambu a

এছাড়াও পড়ুন:

UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara.

“Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Sannan kuma jami’in  ya yi Allah wadai da tauye hakkin yara da ake yi da gangan a Gaza, ya kuma bukaci masu karfin fada a ji a duniya da su dauki mataki.

Ya kara da cewa an toshe alluran rigakafi 180,000 na rigakafin yara masu mahimmanci, da na’urorin saka jariran da ba su kai ga lokacin haihuwa ba, inda Isra’ila ta hana shigar da wadannan kayayyakia  cikin yankunan zirin gaza.

Babban jami’in na UNICEF ya ce, daukar irin wadannan matakana  kan yara yana a matsayin babban laifi wanda ka iya zama laifin yaki bisa dokoki na kasa d akasa.

A kan haka ya kara jaddada kiransa ga kasashe masu karfin fada a ji da su sauke nauyin da ya rataya a kansu kan batun Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba
  • Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba
  • NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
  • Gombe Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.1 Don Samar Da Fitilun Hanya Masu Aiki Da Hasken Rana
  • Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
  • Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai
  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  • Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
  • Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho