2025-03-24@16:51:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 396

«kayan lambu a»:

    Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun maka Shugaba Bola Tinubu a Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara. Gwamnonin sun garzaya kotun ne domin neman fatawa game da abin da sashe na 305 na kundin mulkin ƙasar ke nufi. Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha Juventus za ta sallami kocinta Thiago Motta Gwamnonin da ke kan gaba a shigar da ƙarar sun haɗa da na jihohin Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, Zamfara. Daga cikin abubuwan da suke nema akwai neman kotun ta ɗauki matsaya kan ko sashen na 305 na kudin mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa shugaban ƙasa dama ya dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakiyarsa da majalisar dokoki ta...
    Al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya na nufin makomar kowace al’umma da kowace kasa tana da nasaba da juna. Hakan na nufin ya kamata mu yi rayuwa tare duk rintsi duk wuya, muna more daukaka da wahala tare da kuma kokarin mayar da duniyarmu al’umma guda mai jituwa, inda za mu mai da burin mutane na samun ingantacciyar rayuwa ta zama gaskiya. Shekaru 12 da suka gabata, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki ta farko a matsayinsa na shugaban kasar Sin, ya gabatar da wannan ra’ayi mai cike da hangen nesa. Tun daga wannan lokacin, ra’ayin ko tunani ya bunkasa zuwa wani tsari na musamman da ake aiwatarwa, tare da samun kaso mafi girma...
    Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League. An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga....
    Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yari da ke garin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin. Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya Mista Fanwo ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere ɗin. Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin. Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne. “Dole...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen ɗantayin da ba nata ba, bayan an tilasta ta, ta mayar wa asalin iyayen jaririn ɗansu. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Krystena Murray, mazauniyar Jihar Georgia, ta ɗauki cikin ne bayan dashen ɗantayi na (IBF) da aka yi mata a asibitin masu neman haihuwa da ake kira Coastal Fertility Clinic,...
    4 – Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi kofa ce ta kowane sharri. 5 – Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa. 6 Ki nuna wa mijinki komai naki nasa ne komai nasa kuma nasa ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi. 7- Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa a jikinki in ya shigo gida, ina idonsa ke kallo a jikinki. Bayan kin yi kwalliya. sai a gyara masa su da kyau domin a dauke masa hankali. In kuma kin tabbatar duk lokacin...
    Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad Okhande-Zadeh ya na fadar haka a yau Lahadi: Ya kuma kara da cewa, kasashen da suka shigo da kayaki a kasar Afganistan a shekarar da ta gabata sun hada ta Iran, a gaba da ko wace kasa, sannan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Pakisatn, China da kuma Turkamanistan. Kakakin ma’aikatar kasuwancin ta kasar Afganisatn ya ce a dayan bangaren kuma kasar Afaganista ta fidda kayaki zuwa...
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar da lada na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tare da bayyana Haqqani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo. Kawo yanzu dai babu wani martani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka dangane da matakin. Haqqani shi ne shugaban kungiyar Haqqani, wata kungiya mai karfi a cikin kungiyar Taliban wacce ta shahara wajen ayyukanta da makamai. Duk da ayyana shi a baya a matsayin “dan ta’adda na...
    Kallo ya koma sama bayan da mata suka karbe ragamar kasuwancin kayan lambu a a tsakiyar birnin Gombe, inda a baya kasuwancin kayan ya kasance a hannun maza kadai na tsawon lokaci. Wannan sabon sauyi ya da ya taso a hankali ya faru ne a sakamakon matsalolin kudi da nauyin kula da kai da kuma iyali da suka tilasta matan aure da zawarawa da ma ’yan mata da dama, suka tsunduma harkar wadda a baya ake kallo a matsayin ta maza kadai a wasu yankunan Arewa. Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi Amma a halin yanzu a wani sashe na Babbar Kasuwar...
    Jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) na shiyyar Gombe, sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfarar Intanet a Jihar Bauchi. A cewar wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin, “An kama wadanda ake zargin ne ta hanyar samun sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfarar Intanet a yankin Kaure New Government Reservation Area, Bauchi da Awala, a titin Maiduguri, Jihar Bauchi. Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Rukunin Farko Na Taraktoci Dubu Biyu Daga Belarus Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi “Abubuwan da aka kwato daga hannunsu a wajen kama su sun hada da motoci kirar...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasa Switzerland Chen Xu ya yi jawabi a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 58 kan batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, inda ya yi bayani game da tunanin Sin kan kare hakkin dan Adam da kin amincewa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Chen Xu ya yi nuni da cewa, ana bukatar bin ra’ayin bangarori daban daban da tunanin kare hakkin dan Adam da yin hadin gwiwa mai amfani don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam. Wasu kasashe sun yi amfani da dalilin kare hakkin dan Adam wajen tsoma...
    Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labara da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka. Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.  Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa a cikin tsawon shekara daya da rabi. Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da...
    A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa  Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda  nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki. Wajibi ne mu zauna mu tattauna.” Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran. Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi. Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din...
    A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa. Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum. Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa. Ana zargin rundunar kai...
    Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan an kashe fararen hula 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a. An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun kashe fararen hular ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata. Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin inda ta...
    Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana. Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon hadiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram. Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Lokacin da ta fara amai,...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Fadar Shugaban Kasar Nijeriya, ta yi watsi da rahoton baya-bayan nan da kwamitin hulda da kasashen wajen Amurka ya fitar, wanda ya kafa hujja da amincewar majalisar dokokin kasar, na zargin kakaba wa wasu kiristoci takunkumi a kasar. Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Daniel Bwala, ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe da makama, yana mai jaddada cewa; tun bayan lokacin da Shugaba Tinubu ya dare kan kujerar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, al’amuran cin zarafi, musamman ta fuskar addini suka yi matukar ja da baya. Bwala, ya yi wannan furuci ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, wato na D; yana mai jaddada cewa,...
    Sojojin Sudan sun sanar a yau Juma’a cewa sun kwace iko da fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Khartum, bayan da su ka kori mayakan rundunar kai daukin gaggawa. Majiyar ta ce, sojojin na Sudan sun fara da kutsawa cikin fadar shugaban kasar ne, ta mashigar gabas,bayan da su ka kashe mayakan rundunar kai daukin gaggawa da dama,yayin da wasu da dama su ka gudu zuwa cikin kasuwar dake kusa. Bayanin da sojojin na Sudan su ka fitar ya kunshi cewa; Mun murkushe mayakan Duqlu, ‘yan ta’adda a tsakiyar birnin Khartum da kuma kasuwar Larabawa da ginin fadar shugaban kasa da sauran ma’aikatu.” Har ila yau majiyar sojan na Sudan ta ce,su kuma yi nasarar rusa makamai da motocin yakin...
    Jaridar “Yediot-Ahranot” ta buga wani rahoto da yake kunshe da gargadi daga jami’an sojan mamaya akan yadda ake samun koma baya na sojojin sa-kai saboda da dalilai mabanbanta. Daga cikin dalilan da jaridar ta bijiro da su da akwai gajiya da yaki na lokacin mai tsawo da HKI ta shiga, sai kuma matsaloli na tattalin arziki da  kashe kudade masu yawa wajen kula da su. Haka nan kuma manyan jami’an sojan mamayar sun bayyana yiyuwar rusa rundunar sojan sa-kai din saboda babu wadanda su ka dace su jagorance ta,  ga kuma tsadar tafiyar da rundunar kamar yadda jaridar ta “Ahranot” ta bayyana. Ita kuwa jaridar “Financial-Times” ta bijiro da tata majiyar da take cewa; Yakin da ba shi da ranar...
    Kwamishinan ‘Yansandan ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Kano. Dukkanin waɗanda ake zargi suna cikin bincike a sashen binciken laifuka na CID, kuma za gurfanar da su gaban shari’a bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kazalika, a wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Fabrairun 2025 ya tsaya da kashi 1.67 cikin dari, idan aka kwatanta da watan Janairun 2025, an samu raguwar matsakaicin farashin kayan abinci kamar su dawa, dankali, wake, masara da garin masara da rogo. Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne tun bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafi mai da sauyi da ya kawo kan musayar canjin kudade bayan da ya aka rantsar da shi a 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Kotun Ƙoli ta yanke hukunci tare da tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin halastaccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa. Anyanwu, wanda na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya shafe lokaci yana takun-saƙa da Sunday Ude-Okoye kan wannan matsayi. Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas Ude-Okoye ya samu goyon bayan wasu ɓangarori na jam’iyyar PDP bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu ta tabbatar da naɗinsa, biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tsige Anyanwu. Sai dai, a ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalan Kotun Ƙoli guda biyar, ya yanke hukunci cewa rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya al’amari ne na...
    Dubban dubatan mutane masu goyon bayan magajin garin Istambul a kasar Turkiya ne suka fito kan titunan birnin inda suke bukatar gwamnatin Urdugan ta sake shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mutane suna ganin Ekrem Imamoglu, dan takarar shugaban kasa ne a zaben shugaban kasa mai zuwa kuma mai yuwa ya kara shugaban Urdugan a zaben, saboda yawan magoya bayansa a kasar, musamman a birnin Istambul. Labarin ya kara da cewa Imamoglu mutum ne wanda yake da karbuwa a cikin mutanen kasar, wanda kuma ana ganin mai yuwa ya kada shugaba Urdugan a zaben shugaban kasa mai zuwa. Don haka ana ganin gwamnatin Urdugan ta sa aka kamashi, tare da zargin cin hanci da rashawa,...
    Gwamnatin Isra’ila ta sanar da korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gidan kasar Ronen Bar, wanda Firaministan kassar Benjamin Netanyahu ya ce bai gamsu da kwarewarsa ba hasali ma ba’a yarda da shi.  “Gwamnati baki daya ta amince da shawarar Firaminista Benjamin Netanyahu na kawo karshen wa’adin” Ronen Bar, wanda zai bar ofis idan aka nada magajinsa ye zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, in ji ofishin Firayim Minista a cikin wata sanarwa. Rashin gamsuwa da aikin na kokaren shugaban hukumar ta Shin-bet, ta fito fili a baya bayan bayan bayannan da suke fitowa game da harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Ronen Bar, wanda aka nada a watan Oktoba 2021 na wa’adin shekaru biyar,...
    Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa. Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci. Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai...
    Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno. Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi. ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe Yayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All… Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967. Inda yahudawan suka mamaye har da gabacin birnin Qudus sannan sun ginawa yahudawa...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako. Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin. “Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe. “Sun tilasta Shugaban Kasuwa...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ta yi kakkausar suka ga sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai bayyana su a matsayin “ci gaba da kisan kiyashi da share wata al’umma a yankin da aka yi wa kawanya. Baghaei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i bayan harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara. Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ke da alhakin kashe-kashen da ake yi a Gaza, yana mai cewa, ana kai hare-haren na Isra’ila ne da tare da goyan bayan Washington. Baghaei ya kuma yi kira ga...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma  “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network. Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar. ‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’ Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya...
    Daga ƙarshe, jam’iyyar ta ce kiran da El-Rufai ke yi ga ‘yan adawa da su shiga SDP ba komai ba ne illa ƙoƙarin biyan buƙatun kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan. Idan ana batu na kirkira da amfani da fasahar zamani a duniya, to kowa ya san cewa kasar Sin ta yi zarra a wannan bangare. Haka kuma kowa ya san duk wani ci gaban da Sin take nema ko ta samu, tana yi ne domin jama’arta su kasance cikin walwala, shi ya sa ci gaban Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, ya game kowane bangare na...
    Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar. Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya. Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar. Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria...
    Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar. Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya  Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma...
    Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dan Mahadi Karubi, wanda  yana  ya jagoranci boren 2009 bayan zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa an daukewa mahaifin nashi daurin talalar da aka yi masa bisa umarnin ma’aikatar sharia. Shi dai Mahadi Karubi an yi masa daurin zaman gidan ne bayan hargitsin da ya jagoranta bayan zaben shugaban kasar da aka yi a 2009. Husain Karubi ya fada wa kamfanin dillancin labarun “IRNA” cewa; An fada wa mahaifina cewa, Daga nan zuwa watan Aprilu zai iya gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da kaidi ba, amma daga yanzu zuwa lokacin zai iya sanar da jami’an tsaro inda yake son zuwa gabanin  kwana daya. Harigitsin day a biyo bayan zaben 2009 a Iran wanda ‘yan takara uku...
    A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku. Kungiyar ta Tahrirush-sham ta yi amfani da makamai rokoki da atalare  wajen kai hari daga kan iyaka. Tuni dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta karyata zargin na kungiyar Tahrirus-sham. Ofishin da yake kula da watsa labaru na Hizbullah ya bayyana cewa; Babu gaskiya a cikin labaran da ake watsawa na cewa Hizbullah tana da hannu a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili da kuma abinda wasikar tasa ta kunsa. Dr. Baka’i ya kuma kara da cewa; Bayan yin nazarin wasikar da abinda ta kunsa za mu bayar da jawabi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kore cewa ziyarar da ministan ma’aikatar tasu Abbas Arakci ya kai zuwa kasar Oman yana da alaka da bayar da jawabin wannan wasikar ta shugaban kasar Amurka. Da yake mayar...
    A daren ranar Lahadi Barcelona ta buga wasa mafi kayatarwa a wannan kakar wasanni ta bana bayan ta doke abokiyar karawarta Athletico Madrid duk da cewar Athletico din ta jefa kwallaye biyu a ragar Barcelona a minti 70 na wasan. A kokarin da take yi na sake darewa kan teburin Laliga, Barcelona ta zura kwallaye 4 a cikin minti 20 domin komawa gida da maki uku, Lewondowski, Ferran Torres da Lamine Yamal ne su ka jefawa Barcelona kwallayenta. Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu Julian Alvarez na Athletico Madrid ya fara bude kasuwa a...
    Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar  nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Wata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, a cewar Gidan Rediyon Freedom da ke Kano. Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin...
    An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim. An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama. Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”...
    Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke karkashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba. Haka kuma tuni Trump din ya soma daukar wasu matakai wadanda suka...
    Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibinta Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta. Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza. A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a...
    Barkan mu da sake haɗuwa a zauren girke-girke na watan Ramadana. Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo wa uwargida wani girkin shuwa daga Jihar Borno, wato ‘Kamoniya’ domin yin buda baki. A sha ruwa lafiya. Abubuwan da za ki bukata: · Hanta · Tumbi · Huhu · Albasa 3 · Lemun tsami · Attaruhu · Man gyada · Curry da thyme · Maggi da gishiri Yadda ake hadin: A wanke kayan ciki (banda hanji), sai a yanka su kanana. A zuba man gyada a cikin tukunya, sai a dora a kan wuta. Sannan sai a yanka albasa a zuba man gyadan kadan a cikin tukunyar. Bayan haka, sai a zuba curry da thyme da gishiri...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta  Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
    An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa An kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023, a cewar ’yan sandan Riverbank. Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016. Haka kuma a cewar shafinta na...
    Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi ta jinjina wa wani sojan kasar a matsayin jarumi saboda ci gaba da fafatawa a yankin Kursk tsawon mako guda bayan harbin da aka yi masa a ka. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ruwaito cewa yana cikin Brigade na 155 na Marine na Rukunin Pacific Fleet na Rasha, ya ci gaba fafatawa da sojojin Ukraine a Kursk lokacin da aka harbe shi. Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa A lokacin an harbi hular kansa, amma yana tunanin tabbas harsashin ya huda cikinta. Ya samu kumburi a saman idonsa, wanda daga ƙarshe ya sa...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata. ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Kudin hatsi irin su shinkafa da...
    Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.   Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.”   Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba.   “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed...
    A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace. Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala. A ‘yan kwanakin nan, magoya bayan Manchester United sun ci gaba da nuna fushinsu kan iyalan Glazer, masu mallakar sama da kashi 70 na kulob ɗin. Har ila yau, Ratcliffe bai samu cikakken goyon baya daga ma’aikatan ƙungiyar ba tun bayan zuwansa a shekarar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar. Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro. Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023. Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa...
    Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
    Gwamnatin kasar Amurka ta ce bata bukatar samuwar jkadan kasar Afrika ta kudu Ebrahim Rasool a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa Rasool mutum ne wanda yake nuna wariya, yake kuma kin Amurkawa. Don haka bama da abinda zamu tattauna da shi, kawai bama son ganinsa a cikin kasar babba. Rubio bai bayyana dalilan daukar wannan matakin a kan jakadan ba, amma hakan ya faru ne bayan da Jakadan Rasool ya wata cibiyar bincike na Afrika ta kudu inda a jawabin da ya gabatar ya zargi shugaban kasar Amurka Donal Trump da, da samar...
    Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
    Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Arewa domin inganta tsaro. Ya yi wannan roƙo ne bayan ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira a Kangiwa, bayan harin da wasu da ake zargin Lakurawa ne suka kai musu. Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 Harin da aka kai a ranar 9 ga watan Maris ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da ƙone ƙauyuka bakwai. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro, da Garin Rugga. “Sansanin soji a yankin zai taimaka...
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.   A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.   Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.   “A wannan karon,...
    Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi akan cewa; Wata sabuwar yunwa za ta  bulla a Gaza saboda yadda HKI take ci gaba da killace yankin da hana shigar da kayan agaji hatta a cikin watan Ramadan. Kakakin kungiyar ta Hamas Abdullatif al-Qa’uni wanda ya fitar da wani bayani ya ce; Falasdinawa a yankin Gaza an killace su, makonni biyu a jere, kuma sojojin mamaya sun hana a shigar da kayan abinci,magunguna, da makamashi, wanda hakan yake a matsayin amfani da yunwa a matsayin makamin. Qa’ani ya kara da cewa; Abinda ‘yan mamaya suke yi, shi ne jefa Falasdinawa cikin yunwa. Haka nan kuma ya ce;  A nan gaba kadan kayakin da ake da su na bukatun yau da...
    Amurkawa masu goyon bayan Falasdinu sun gudanar da gangami a unguwar manhatan na birnin Nuyork don neman sakin Mahmoud Khalil daya daga cikin masu gwagwarmaya kan tafarkin samun yencin Falasdinawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kama Mahmoud Khalila da kuma tsareshi ya ingiza matasa da dama a Amurka suka nuna goyon bayansu a gareshi, wasu kuma suka fito zanga-zangar neman a sake shi. Mahmoud Khalil dai, ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Colombia na birnin News na kasar Amurka. Sannan ya shahara da goyon baya ga al-ummar Falasdinu. Banda haka yana da ‘Green Card wanda ya bashi damar zama a kasar Amurka na dindin din. Amma a rahotannin da suke fitowa gwamnatin kasar tan son...
      Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi.   Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce ci gaban, suna nuna cewa gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu na yin tasiri.   Ya amince da wahalhalun da ‘yan Najeriya suka sha amma ya tabbatar da cewa hakan ya fara wucewa.   Mohamed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya tana nan daram wajen daidaita tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.   A jawabinsa, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce kudaden da aka...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Ministan harklokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce kasarsa na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar farko ta Iran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi. Mista Lavrov ya jaddada goyon bayan Moscow ga sake farfado da muhimmiyar yarjejeniya da Iran da manyan kasashen duniya suka rattabawa hannu a shekarar 2015. “Mun tattauna halin da ake ciki a yankin Tekun Fasha da kuma shirin hadin gwiwa,” in ji Lavrov a wata hira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Tass, yayin da yake amsa tambaya kan ko batun Iran na cikin tattaunawar da ake yi tsakanin Rasha da Amurka. Rasha ta tattauna halin da ake ciki dangane da yarjejeniyar da Iran ta kulla da Amurka yayin da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki. Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha. “Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in...
    Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
    Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
    Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare,  duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya yi nuni da lamari na baya-bayan...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
    Kasar Uganda ta sanar da aikewa da sojojinta zuwa birnin birnin kasar Sudan Ta Kudu, Juba saboda ba shi kariya. Sai dai har yanzu gwamnatin Sudan din ba ta  tabbatar da hakan ba.  Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Uganda Janar Muhoozi Kainerugaba ya bayyana cewa; Rundunar musamman ta Ugandan ta shiga cikin birnin Juba, domin ba shi kariya. Janar Muhoozi Kainerugaba ya kuma ce: “ Za mu kare dukkanin kasar Sudan  Ta Kudu, kamar yadda za mu kare kasarmu. A wurinmu Salva Kiir ne mu ka aminta da cewa halartaccen shugaban kasar Sudan  Ta Kudu,don haka duk wanda zai shelanta yaki akansa, ya shelanta yaki ne akan Uganda.” Har ila yau janar din na Uganda ya kuma ce; “  Wadanda...
    Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da  sauran dangoginsa da sun kai  ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta  EFCC ta bayyana cewa,  ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar  “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke. Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu. Ya...
    Duk da haka, kungiyar za ta ci gaba da amfani da Old Trafford har sai an kammala sabon filin wasan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
    UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza. Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen  zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka. “Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin...
    An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana. ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ An hana tashe bana a Kano — Nalako Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
    Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
    Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran. A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...