Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki
Published: 26th, March 2025 GMT
Daraktan Fim ɗin Mai martaba, Prince Daniel (ABOKI), ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa yana fuskantar tsangwama a Kannywwod saboda bambancin addininsa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Aboki ya ce shi ma batun cewa ana nuna masa bambamci a Nollywood saboda ɗan arewa ne ba shi da tushe balle makama.
“Wasu labarai da aka wallafa na nuna cewa wai masana’antar Kannywood ta ƙi amincewa da ni saboda addini na, ita kuma Nollywood saboda ni ɗan Arewa ne.
“Da farko dai ban yi hira da wata jarida ko kafar yaɗa labarai ba dangane da wannan batu. Amma duk da haka bari na ɗan yi ƙarin haske.
“Na halarci wani taron masana’antar Nollywood da Hollywood a birnin Los Angeles na Jihar California da ke Amurka a farkon wannan watan, inda a sashen tambaya da amsa na taron aka tambaye ni ƙalubalen da muka fuskanta lokacin fim ɗin Mai Martaba da gwagwarmayar da muka yi kafin kai wa matakin kambun fina-finan duniya na Oscar.
“Na faɗi abubuwa da dama da suka haɗa da fargabar matsalar tsaro da na masu ɗaukar nauyi kasancewar babu wanda yake son yin kasadar ba mu kuɗinsa, la’akari da cewa ni sabon darakta ne wanda ke aiki tare da sababbin jarumai.
“A wani lokacin ɓangaren masana’antar Kannywood na yi mana kallon ‘yan Nollywood, su ma Nollywood suna kallonmu a matsayin ‘yan Kannywood, saboda kawai ni ɗan Arewa ne.
“Na yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya domin taimaka wa masu sauraro a cikin zauren su fahimci ɓangarorin masana’antar Fina-finai a Najeriya da kuma yadda yake da ƙalubale a gare mu a lokacin.
“Domin fayyace zahiri, masana’antar Kannywood ba ta taɓa nuna min ƙiyayya ba ta ƙabilanci ko addini.
“Hasalima, masana’antar ce babban ginshiƙin goyon bayan da na samu a matsayina na mai shirya fim.
“An nuna min ƙauna a fili ta hanyar babban goyon bayan da muka samu daga masu kallo da sauran al-umma a lokacin da muka nuna fina-finanmu a gidajen kallo, da kuma ƙarfafawa daga ƙwararrun ‘yan masana’antar tsofaffi da sababbin shiga,” in ji shi.
Fim ɗin Mai martaba dai an haska shi ne kimanin watanni takwas da suka gabata, kuma ci gaba ne kan wasan kwaikwayon gidan Rediyon Arewa da ke Kano mai taken ‘Kasar Jallaba”, inda Prince aboki ke aiki a matsayin jagoran sashin shirye-shirye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kannywood masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah
Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai.
Matsalar tsaro
Ko shakka babu lamarin tavarvarewar tsaro ba karamin koma baya ya kawo ba na lamarin zamantakewa tsakanin al’umma abu tun daga wannan unguwa zuwa waccan har,ta kai ga daga wannan babban gari ma zuwa wancan har ta kai ga daga wannan Jiha zuwa waccan.Irin halin da al’umma suka tsinci kansu ke nan lamarin da ya kan yi tafiyar Kura yadda take gaba sai ta koma baya. Arewa ta sassa daban- daban tana fama da matsalar data shafi tsaro tunda kuwa ana yin garkuwa lokaci,anan matafiya wasu Jihohi na sashen Arewa maso yamma kamar Kaduna, Katsina,Zamfara,Sakkwato,da kuma Kebbi,masu ta shi daga Abuja zuwa gida wasu suna kan hanyar tasu ake tsaida su a kwashi mutane kamar Dabbobi ayi cikin daji dasu,kai har ma,ta kai ga mutane ko,a gidajensu suke basu tsira ba ana iya zuwa kowane lokaci ayi awon gaba dasu sai kuma yadda Allah yayi.Yayin da wasu suna dawowa wasu kuwa sun tafi ke nen sai dai aji labarin an kashe su,wasu ko ma an kai kudin fansar ba,za’a sake su ba.Irin hakan ce ta sa wasu yanzu basu zuwa gida Sallah saboda tsoron aukuwar irin hakan,maimakon hakan sai su yi hakuri su rungumi kaddara ta yin rayuwa kamar irin cikin halin,da suka samu kansu.
Tafiya zuwa yawon Sallah daga wannan unguwa zuwa waccan ko daga wannan gari zuwa wancan,halin da ake ciki yanzu hakan bata yiyuwa ba domin komai ba sai saboda tsoron irin abinda ka iya faruwa gare su,maganar gaskiya yanzu lamarin tsaro ya sa mutane da yawa sun,shiga cikin halin tsoro saboda komai yana iya faruwa a lokacin da ba ayi tsammanin hakan ba.Ba ance babu tsaron bane gaba daya amma su wadannan masu tayar,da zaune tsaye ko ina suna iya zuwa saboda ai suna da wadanda suke basu halin da ake ciki da su kan samu na su kason idan an yi sa’ar dauka da kuma garkuwa da mutane aka kuma biya kudin fansar.
Al’umma da dama basa garuruwan su na asali
Mutane da dama yanzu wasu ma ba Jihar su ta asali suke ba,wasu suna wata Jiha,kai akwai ‘yan Nijeriyar da har yanzu suna kasashen Nijar ko kuma Kamaru,idan ma sun yi sa’ar suna Jihar tasu ne,to su kan kasance ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira ne wato wuraren da aka tsugunnar dasu,sanin kowa ne,babu yadda rayuwa za ta yi daidai ga wasu a,irin wadancan wuraren saboda can ma din da akwai nau’oin matsalolin da suke fuskanta a can.Ana iya tunawa shifa sansanin ‘yan gudun hijira wuri ne da aka ware na musamman wanda ake taimakawa nau’oin mutanen da suka fuskanci matsala babu yadda za su iya yi wajen tafiyar da rayuwarsu.Daga karshe sanin kowa ne duk wanda bai garin shi na asali rayuwa Lami yake yin ta domin a matukar takure yake.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp