Yadda Kanawa suka huce takaicin rashin Hawan Sallah
Published: 6th, April 2025 GMT
Sanannen abu ne cewa irin shagulgulan da ake gudanarwa a lokacin bukukuwan sallah a Kano na samar da nishaɗi da walwala ga mazauna jihar da ma baƙi da ke zuwa kallo daga sassa daban-daban na duniya.
Haye-hayen Sallah da Sarkin Kano da hakimansa da sauran ’yar majalisarsa ke yi na daga cikin abubuwan mafi bankaye da sanya farin ciki da annashuwa a zukatan dubban mutane a yayin shagulgulan.
Rashin gudanar da hawan a bara saboda hanawar da ’yan sanda suka yi sakamakon Dambarwar Sarautar Kano, ta sa umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar ga sarakuna cewa su shirya gudanar da hawa a bana, ya faranta zukatan dubban mutane da ke ta mararin shaida hawan salla ta bana, abin da suka yi matukar kewa bara.
To sai dai kuma, a jajibirin sallah murna ta koma ciki, bayan ’yan sanda suka sake hana gudanar da hawan, saboda irin dalilin da suka bayar a bara.
Wannan sanarwa ta sanyaya gwiwar dubban mutane da suka ci burin halarta, domin yi hawan ko gudanar da harkokin kasuwanci ko kashe kwarkwatan idanunsa, baya ga kashe musu armashin bikin.
Amma duk da haka Kanawa sun gudanar da bukukuwansu na Sallah kamar yadda suka saba, inda suka huce takaici ta wasu hanyoyi, duk kuwa da cewar ba a samu damar fita kallon jerin gwanon dawaki da mahaya da maharba da sauran abubuwan kayatarwa da aka saba gani a Masarautar Kano a lokacin hawan Sallah ba.
A sakamakon haka, wasu mahaya da suka yi shirin yin hawa a Kano sun yi bulaguro domin yin hakan nasu a wasu masarautu a wasu jihohi, wasu hayan dawakan nasu suka bayar a can.
’Yan kasuwa masu cin albarkacin Hawan sallah, musamman masu daukar hoto sun sauya dabara, a yayin da ’yan kallo kuma suka samu wasu wurare don kashe kwarkwatar idanusu ko suka cashe.
Ita dai wannan hana hawan sallar ta samo asali ne daga rikicin Masauratar Kano tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da kuma Sarki Aminu Ado Bayero wadanda kowannensu ke da’awar shi ne halastaccen Sarki, inda a wannan karon kowannensu ya gudanar da sallar idi daban da ta dan uwansa, ya kuma karbi gaisuwar sallar daga hakimansa da jama’ar gari a lokaci guda.
Sarakunan da ke rikicin Sarautar Kano kuma kowannensu fadarsa ta gudanar da wani abudomin mabiyansa da masoya su ji alamar hawa ko fadancin Sallah a fadarsa.
Sallar Idin sarakuna biyuSarki Sanusi ya fita zuwa Filin Idi na Kofar Mata a ƙafa, yadda aka saba a bisa al’ada, yana sanye da fararen kaya da farar alkyabba mai ado da bakin zare, sannan ya jagorancin Sallar Idi da kansa.
Bayan an sauko idi ya hau farin doki riƙe da Bakan Dabo kuma rataye da kwari tare da rakiyar manyan bayin sarki da Sarkin Dogarai kowannensu bisa doki da sauran yaran sarki ’yan ƙasa, suka kama hanyar komawa fadarsa ta Kofar Wambai ana buga tambura da kuge ana ta bushe-bushen algaita da kakaki da kaho, gefen hanya kuma daruruwan jama’a sun fito bakin hanya suna gaisuwa da jinjina ga sarki, shi kuma yana karbar gaisuwa ta dama da hauni.
Rashin hawan hakimaiSai dai kuma, saɓanin yadda aka saba gani, a wannan karon babu hakimi ko daya da ya hau doki domin raka sarki zuwa filin idi.
Wannan ya rage armashin hawan, domin kuwa ’yan kallo ba su ji dadin rashin hawan hakimai ba, wadanda da ma su ke daukar makada da ’yan bori da maroka da sauran masu kade-kade a yayin gudanar da Hawan Sallah.
Haka dai Sarkin ya ci gaba da tafiya har zuwa Gidan Shattima, inda ya gaisa da Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf da sauran mukarraban gwamnati sannan ya karya linzami ya shiga gida.
Sallar Idin Sarki AminuA can Fadar Nassarawa kuma, Sarki Aminu Ado Bayero ya halarci sallar Idi tare da daruruwan masallata.
Sarkin ya yi shiga ta alfarma da alkyabbar da aka yi mata ado da zare mai ruwan zinare.
Bayan idar da Sallah ya karanta jawabinsa na Sallah, sannan hakimansa suka yi ta zuwa suna kawo masa gaisuwa, daga bisani ya koma cikin gida.
Yammacin Ranar sallahSai dai duk da rashin hawan, an ci gaba da wasu al’adun a fadar Kano.
A ranar Sallah da yamma sarakunan biyu sun fito fada inda hakimai da sauran jama’ar gari suka yi tururuwar zuwa gaishe su.
Sarki Sanusi II ya fito a kan doki cikin kwalliya sanye da malafa, masu buga tambura na biye da shi a kan rakuma suna buga masa tambari.
Wannan ya kayatar da waɗanda suka zo gaisuwar domin kuwa aƙalla sun ji tambari da akan yi lokacin hawa.
A Fadar Nassarawa ma an buga tambura da suke alamta mulki da sarauta ga Sarki Aminu Ado Bayero.
Fitattun mawaƙa irin su Aminu Ladan Alan Waka kuma sun cashe a Fadar Nassarawa domin nishaɗantar da jama’a sakamakon rashin gudanar da Hawan Sallah.
Ranar Hawan DausheAn ci gaba da gudanar da shagulgulan Sallah a washegarin ranar Sallah yayin da mutane suka ci gaba da gaishe-gaishen ’yan uwa da abokan arziki.
Bisa al’ada, washegarin Sallah rana ce da ake gudanar da Hawan Daushe, wadda a wannan karo ba a samu damar gudanarwa ba.
To amma sarakunan biyu sun sami zarafin karbar gaisuwa daga hakimai da dagatai da sauran jama’ar gari
A yammacin ranar ce kuma Sarki Sanusi II ya hau mota domin zuwa ya gaishe da mahaifiyarsa a gidansa da ke titin Ibrahim Dabo tare da rakiyar hakimansa.
Ranar Hawan NassarawaA rana ta uku ga Sallah watau ranar Talata, ranar da ake gudanar da Hawan Nassarawa a bisa al’ada, Sarki Sanusi II ya tafi gidan Gwamnati a cikin jerin gwanon motoci da ’yan bindiga da ’yan baka da sauran ’yan fada domin taya Gwamna Abba Kabir Yusuf barka da Sallah.
Sarkin ya sami kyakkyawar tarba daga Gwamna Abba, wanda a cikin jawabinsa ya zayyana irin aikace-aikacen da gwamnatinsa take aiwatarwa domin ci-gaban Jihar Kano.
A yayin da ake wancan biki a gidan gwamnati, can ma Fadar Nassarawa Sarki Aminu Ado Bayero a daidai lokacin ya fito ana gunadar da bikin karbar gaisuwa daga kungiyoyi da sauran bangarorin jama’a.
Rashin hawa ya rage wa bikin Sallah armashi
To yaya mutane suka ji game da rashin gudanar da Hawan Sallar bana?
Wani matashi mai suna Yusuf Abdullahi ya ce, “duk mutumin Kano ko’ina yake idan ba Kano ya zo Sallah ba, to ba ya jin dadi saboda yadda haye-hayen Sallah ke kara armashi ga bukukuwan Sallah, amma rashin gudanar da hawan ya sa Sallah ta kusa zama lami.
“Duk Nijeriya mutumin Kano ba ya Sallah Sai a Kano saboda kasaitar Hawan Sarki.
“Babu inda ya kai Kano tsara Hawan Sallah. Hatta tambura da irin busar algaitar Kano daban suke.
“To ga shi rigimar masarauta da gudun tashin hankali ko fitina ya sa an hana hawan gaba daya.
“Muna fatan Allah Ya Kawo mana hanyar da za a warware rikicin domin a dawo mana da al’adar hawan da muka saba,” in ji shi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan rashin hawan, wani magindanci mai suna Adamu Aminu Fagge ya ce, “Bayan Sallar Idi da cin tuwon sallah, kwanciyata na yi na yi barci domin na san ba wani abin yi.
“Rashin gudanar da Hawan Sallah ya rage wa bikin karsashi da nishaɗi duk kuwa da cewa a ganina dalilan tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka suka sanya aka hana hawan.”
Yadda Kanawa suka huce takaiciMahaya dawaki su suka fi takaicin rashin hawan, domin kuwa yawancinsu sun riga sun tanadi kayan ado da dawakai na hawa da shirin kure adaka da kuma fita kunyar ’yan kallo.
Rashin gudanar da hawan ya sa wasunsu yin bulaguro zuwa masarautun Dutse da ta Kazaure da Daura da ke makwabtaka da Jihar Kano domin gudanar da hawan a can domin su huce takaici.
Wasu mahayan kuma dawakan nasu suka bayar haya domin a yi hawa da wasu a masauratun da ke makwabtaka da Kano.
A gefe guda kuma, iyayen yara kanana maza da mata sun yi tururuwa zuwa Gidan Zoo wanda ya yi cikar kwari, domin samun nishadi da kallon mamun daji.
Masu gudanar da wasanni iri-iri kuma sun yi amfani da wannan damar wajen gudanar da wasanninsu na barkwanci da sauransu a cikin gidan zoo, inda suke karbar ’yan kudade a hannun masu kallon.
Wani wurin da ya iyaye da yara ’yan yawon Sallah suka yi dafifi shi ne filin wasan yara da ke Ado Bayero Mall, inda suke rububin biya kudin shiga su yi wasa a kan lilo da motocin wasa iri-iri.
Matasa, samari da ’yan mata kuma sun yi ta turuwar zuwa gidajen daukar hoto cikin kwalliyarsu ta Sallah domin daukar hotuna.
Wani saurayi, Salim Khalid, ya ce saboda ajiye tarihi yake zuwa ya dauki hoton Sallah a lokacin da ya yi adon Sallah.
Wani mai sana’ar daukar hoto, Malam Nasiru Darki, ya ce lokacin bukuwan Hawan Sallah na ba su damar samun kudi ta hanyar daukar hoton mahaya wadanda ke yin kwalliyar ta musamman.
Kazalika ’yan kallon kan biya a dauke su hoto a wurin hawan Sallah, don hana hawan ya kawo musu koma baya ta wani bangaren, shi ya sa ma suke dogaro da masu zuwa shagon daukar hoto a yi musu hoton su koma gidajensu.
Wasu kuwa sun shirya wasannin kwaikwayo da raye-raye a wurare na musamman inda ’yan kallo kan biya kudi su shiga.
Daga cikin irin wadannan wurare akwai gidan tarihi na Makama Museum.
Yadda sallah ta gudana a kauyukan KanoShugaban Kungiyar Ci-gaban Kasar Bichi, Injiniya Bello Gambo Bichi, ya shaida wa wakilinmu cewa mutane sun gudanar da bikin Sallah ba tare more kallon Hawan Sallah a Bichi ba kamar yadda ya gudana a ’yan shekarun baya saboda rushe masarautar.
Ya ce an yi sallar idi tare da sadar da zumunta da gaishe-gaishe, amma rashin Hawan ya sa bikin bai yi armashi sosai ba.
Mazauna kauyuka sun gudanar da bikin Sallah kamar yadda aka saba inda bayan saukowa daga Sallah Idi, suka koma gidajensu domin cin tuwon Sallah, yayin da yara ke zuwa gidajen ’yan uwa rabon abinci da kuma sada zumunci.
Khadija Ibrahim, wata mazauniyar Garin Rimin Gado ta shaida wa Aminiyya cewar, “Babu wani abu da aka gudanar a garin tun bayan da aka sauko daga Sallar Idi, illa kowa ya koma gida yana zaune.”
Haka abin yake a Makoda da Danbatta, inda jama’a manya da yara suka fita zuwa Sallar Idi cikin sabbin tufafi.
Wani mazaunin garin, Sani Ibrahim ya shaida wa wakilinmu cewa “babu wasu shagulgula da aka gudanar bayan saukowa idi, illa ziyarce-ziyarcen ’yan uwa da sada zumunci.”
A Masarautar Karaye ma dai bikin Sallah ya gudana ne ba tare da hawa ko shagali ba.
Abdullahi Dantani, wani matashi da ke zaune a garin, ya ce babu wasu wasannin Sallah da aka gudanar a garin bayan gabatar da Sallar Idi.
Haka lamarin yake a garuruwan Bebeji da Wudil da Garko da sauran kauyuka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hawan Sallah Jihar Kano Masarautar Kano Sarki Aminu Ado Bayero Sarki Muhammadu Sanusi II Rashin gudanar da Hawan rashin gudanar da Hawan Rashin gudanar da hawan rashin gudanar da hawan Sarki Aminu Ado Bayero Fadar Nassarawa Sarki Aminu A Hawan sallah Hawan Sallah rashin Hawan Rashin hawan hawan Sallah Sarki Sanusi rashin hawan daukar hoto Rashin hawa
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Yada Hutunan Bidiyo Wadanda Suka Nuna Yadda Sojojin Amurka Suka Kashe Mutanen Yemen Wadanda Suke Bukukuwan Salla Karama
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yada wasu hutunan bidiyo wanda yayi kama da na jiragen yakin kasar ne kan kasar Yemen, inda suka yi ruwan boma bomai a kan su a matsayin yan ta’ada wadanda suke shirin yakar Amurka, amma daya baya shaidu sun ta tabbatar da cewa taron ta yan kasar ta Yemen ne a birnin Hudaida wadanda suke bukin sallah karamar da ta gabata a ranar 4 ga watan Afrilun da muke ciki.
Labarin ya kara da cewa wannan aikin na sojojin Amurka ya na iya zama laifin yaki wanda ana iya gurfanar da gwamnatin Amurka kan laifukan yakin da ta ke aikatawa a yake-yakenta na kasashen waje.
Wannan zargin yana cewa ne bayan da sojojin Amurka suka fara kaiwa kasar Yemen hare-hare a cikin watan Maris da ya gabata, kuma ya zuwa yanzu sun kai mata hare-hare har fiye da 200.
Manufar gwamnatin kasar Amurka a yakin da take kaiwa kasar Yemen itace, raunan kasar ta Yemen a hare-haren da take kaiwa HKI, da kuma harba makamai kan jiragen ruwan kasuwanci na HKI wadanda suke wucewa ta tekub red sea.
A wani sakon X daga kasar Yemen da wani a Yemen ya mayarwa Trump. Y ace masa. Taron wata kabila ce daga kabilun lardin Hudaida, kuma ka kasa yin kome da kasar Yemen sai ka koma kashe fararen hula wadanda ba ruwansu da jiragen ku.