2025-04-07@02:12:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 19

«Fadar Nassarawa»:

    Gwamnatin HKI ta sha mamaki da ganin gwamnatin shugaba Trumo na kasar Amurka ta sanya mata harajin shigowar kayakin HK zuwa kasar Amurka, a yayinda, kafin haka ta bada sanarwan cire dukkan kudaden fito ko haraji ga kayakin Amurka da ke shigowa HK. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta majiyar kafafen yada labarum HKI na fadar haka daga bakin wani jami’an gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa, Amurka ta dorawa HKI kudaden fito na kasha 17% kacal, sai dai ba abinda take tsammani zai faruba, tsammaninta shi ne irin wanda ta yi wato babu kudaden fito. Gwamnatin Amurka dai ta rikita harkokin kasuwanci da dama a duniya saboda kudaden fito da ta karawa kusan kasashen duniya gaba...
    Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su. Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya. Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da motocin Sarkin ke wucewa. Duba hotunan hawan a ƙasa: Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing. Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau Talata, inda ya ce daukacin mahalarta taron na karawa juna sani sun yi imanin cewa, a halin da ake ciki, ya kamata a karfafa ayyukan MDD, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kuma tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta a duniya. Kazalika, mahalarta taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ta taka...
    Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule. Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar. Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su, domin tabbatar da sahihanci da ingancin aikin jarida. Da yake ƙarin bayani, ya ce gwamnatin Abdullahi Sule ta kawo sauye-sauye masu amfani, musamman wajen inganta harkar haƙar ma’adinai a jihar. Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ce ke kan gaba a Naieriya wajen samar da ma’adinan Lithium, wanda ke amfani ga ci gaban tattalin arziƙi. A nasa jawabin, Shugaban ‘Yan Jarida na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju,...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu. Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari. Wani ganau da ya buƙaci a sakaya...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Ana sa ran waɗannan sabbin jarin za su samar da ayyuka 3,940 a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar. Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira. Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Kano yayin rabon kayan tallafi da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon. Kabiru Dahiru Sule, ya bayar. Ya zargi wasu mutane na amfani da zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa don cimma muradun kansu da kuma haddasa rikici a Kano. “Muna kira ga...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ya hori Kiristoci masu niyyar ziyarar su zama jakadu na gari tare dayin addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba idan sun isa can.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bankwana da masu ziyarar su 162 da zasu tashi zuwa Isra’ila.   Gwamnan ya jaddada muhimmancin da’a a yayin tafiyar tasu, inda ya bayyana cewa su dauka su Allah ya nufa da wannan ziyarar a bana.   Ya kuma tabbatar wa maziyartan jihar cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwarsu, tare da samar da matsuguni da abinci kyauta a tsawon tafiyarsu.   Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin hukumar kula da masu ziyarar kiristoci ta jihar Nasarawa, Davide Ayiwa, wanda ya yabawa...
    Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da DSS sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Ƙofar Nasarawa da ke Jihar Kano. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun yi dandazo a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa, lamarin da jami’an tsaron suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan Kawo yanzu dai ba a gano dalilin gudanar da zanga-zangar ba, sai dai tuni jami’an tsaro suka sanya shamaki a hanyoyin da ke daura da zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
    Kakakin Majalisan ya amince da kudirin dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana kuma shugaban Kwamitin Majalisar kan Muhalli, Hon. Muhammed Adamu Omadefu, wanda ya bukaci dakatarwar a yayin tantance kwamishinan a zauren Majalisar da ke Lafiya, babban birnin jihar.   Hon. Jatau ya ce, Majalisar za ta sake duba batun tantance shi ne kawai idan ya aika da wasikar neman uzuri mai karfi ga Majalisar kan aikata laifi da rashin biyayya da ya yi lokacin da yake Kwamishina.   Ya ce, Majalisar ba za ta bari wani jami’in gwamnati ya zubar da darajar Majalisar ba.
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
    Wani ɗalibi a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya da ke Jihar Nasarawa ya yi wa abokin karatunsa kisan gilla ta hanyar amfani da wuƙa da gatari. Rundunar ’Yan Sanda Jihar Nasarawa ta ce ɗalibin da ya yi kisan gillar ɗan ajin ND2 a Fannin Aikin Banki da Hadahadar Kuɗaɗe ne a Kwalejin kuma yana hannunta, yana amsa tambayoyi. Ta bayyana cewa ya amsa laifin tare da shaida wa masu bincike cewa ya yi amfani da wuƙa da kuma gatari wajen halaka abokin nasa a gidan da suke haya bayan wata hatsaniya a tsakaninsu. Kakakin rundunar, Rahman Nansel, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kai ɗauki ne bayan matar da ɗaliban ke haya a gidanta, Mercy-Bassey, ta sanar da rundunar...
    Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki kan hanyoyin da za su yaki ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya ta hanyar amfani da darussan da aka koya a wajen wani bada horo da ya gudana a Sakkwato.   Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana haka a Sokoto a wajen wani taron karawa juna sani da nufin tattauna sabbin dabarun murkushe ‘yan bindiga da sauran ayyukan tada kayar baya a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Runduna ta 8 ta Sojojin Najeriya dake Sokoto.   Wanda ya samu wakilcin babban hafsa Manjo Janar Olusegun Samson Abai, ya ce ziyarar wayar da kan ta taso ne domin inganta aikin da ake yi ta hanyar...
    Wani Jami’in Ɗansanda Ya Bindige Kansa Har Lahira A Jihar Nasarawa
    Kamfanin hakar ma’adinai na Jiuling Lithium, na kasar Sin, na shirin zuba jarin sama da dala miliyan 200 a domin haƙar lithium a Endo da ke jihar Nasarawa. A ziyarar da gwamna Abdullahi Sule ya kai, shugaban kamfanin, Mista Xiong Jin, ya jaddada aniyarsu ta gina daya daga cikin manyan masana’antar samar da lithium a jihar. Ya kuma bayyana cewa ma’aikatan da aka dauka aiki a wurin za su sami mafi karancin albashi na N500,000. Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa Gwamna Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwar Nasarawa, Ya Sauke Sakataren Gwamnati Gwamna Sule ya bukaci matasa da su rungumi sana’o’in hannu domin cin gajiyar guraben ayyukan yi a fannin hakar ma’adinai. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar...
    Wani Jami’in Ɗan Sanda da ke aiki a ofishin ’yan sanda na yankin Mada a Jihar Nasarawa, ya harbe kansa da bindiga har lahira. An gano ɗan sandan, mai suna Dogara Akolo-Moses, yana aiki ne a Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon lokacin da ya kawo ƙarshen rayuwarsa. ’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Shaidu sun bayyana cewar ya shiga wani ɗaki sannan ya harbe kansa da bindiga. Sautin harbin bindigar ne ya jawo hankalin abokan aikinsa, waɗanda suka garzaya zuwa ɗakin, inda suka same shi kwance cikin jini da bindiga a gefensa. Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya hallaka kansa ba. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar...
۱