Aminiya:
2025-04-24@13:07:27 GMT

Ya isa haka: Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su kawo ƙarshen kashe-kashe

Published: 24th, April 2025 GMT

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya  ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara.

Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa.

“Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da tsaro ke ciki.

Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci

Ribadu ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin amfani da sabbin dabaru don magance matsalolin rashin tsaro.

Ya ce, shugaban ƙasar “ya ba mu damar zuwa mu sake yi masa bayani. Ya ɗauki lokaci mai tsawo muna masa cikakken kan abin da ke faruwa.

“Ko da ya yi tafiya ƙasar waje yana yawan tuntuba, yana ba da umarni kuma yana bin diddigin abubuwan da ke faruwa. A yau kuma mun sami damar sake yi masa bayani na tsawon awanni.

“Mun saurara, kuma mun karɓi sabbin umarni daga gare shi. Gaskiya, ya nace cewa mu yi aiki tuƙuru don maido da tsaro a ƙasa.

“Mun yi masa bayani kan abin da ya faru kuma muka tabbatar masa da jajircewarmu.

“Mun aiwatar da umarninsa, mun je wuraren da ake fama da rashin tsaro, kamar jihohin Filato da Binuwai da Borno, kuma mun ba shi ra’ayinmu saboda ya ba mu umarni mu je mu gana da hukumomin siyasa a can,” in ji shi.

Ribadu ya ce Tinubu ya jaddada buƙatar ƙara shigar da ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi wajen magance al’amuran rashin tsaro.

“Matsalar rashin tsaro sau da yawa ba ta tsaya ga manyan matakai kawai ba. Ta ƙunshi ƙananan hukumomi. Su ne ke tare da mutane kai tsaye, musamman ma idan wasu ƙalubalen sun shafi matsalolin al’umma.

“Muna buƙatar yin aiki da al’ummomi  da ƙananan hukumomi da kuma gwamnoni. Shugaban Ƙasa ya ba da umarni cewa mu ƙara yin aiki da gwamnoni,” in ji shi.

Ribadu ya ce Shugaban Ƙasa ya “damu sosai” a taron kuma ya ce “abin ya isa haka.”

Ribadu ya ce maharan galibi suna kai hari ne kan ’yan ƙasa marasa galihu ta hanyar dasa bama-bamai da kuma kai hari kan wuraren da ba su da gwamnati.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tsaro shugabannin tsaro Shugaban Ƙasa Ribadu ya ce rashin tsaro ba da umarni

এছাড়াও পড়ুন:

Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna

Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake yi a birnin. A cewar gwamnan, an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke napep a tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe. Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati, ranar Talata. Ya ce, amma dokar ta kebe cibiyoyi da hukumomin kiwon lafiya. Ya bayyana cewa, sabon matakin na da nufin dakile matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a babban birnin jihar. Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta rungume hannu ba, yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Ya kuma umurci gundumomi, ƙauye, da masu unguwanni da su sanya ido kan duk wadanda ke zaune a yankunan su. Ya kuma yi gargadin cewa, duk gidan da aka samu yana dauke da masu aikata laifuka ko masu safarar miyagun kwayoyi za a ruguza shi. A baya-bayan nan dai garin Minna ya sake samun koma-baya na ‘yan daba, da hare-hare, da kashe-kashe, lamarin da ke janyo firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sakataren PDP: Damagum ya amince da matsayar gwamnoni
  • Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Abuja
  • Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Tsaro Da Ribadu Kan Kashe-kashen Rayuka
  • Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
  • Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai