2025-05-15@14:07:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1598
«azumin shekara»:
Ƴan majalisar tarayya guda biyu daga jihar Kano, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun sanar da barin jam’iyyar NNPP zuwa APC a yayin zaman majalisar ranar Alhamis, suna mai nuni da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar. Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun ficewarsu a zaman majalisar, inda ya bayyana cewa Usman na wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya, yayin da Sani na wakiltar Karaye/Rogo. Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC Gwamna Yusuf Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Jerin Gidajen Kwankwasiyya, Amana Da Bandirawo Ko da a kwanan baya ma Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da wasu sun fice daga jam’iyyar NNPP, su ma dai sun ce rikicin ne ya fitar da shi. Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje da wasu...
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi. Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau. Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su. A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan jihar Kano da ke niyyar gudanar da aikin hajjin bana. Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu na gari a jihar, su kuma yi addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da hadin kan jihar Kano da Nijeriya baki daya. Ya jaddada kudirin gwamnati na tallafa wa duk maniyyata a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki. Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ya shawarci alhazai da su kwantar da hankulansu, su kuma maida hankali wajen gudanar da ibada. A nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin...
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hukumar kula da manyan makarantu ta jihar Kaduna, ta shekarar 2025, ya zama doka. Dokar dai na da nufin daidaita harkokin gudanar da manyan makarantun sakandire a fadin jihar domin daidaita tsarin ilimin zamani. Da yake jagorantar zaman majalissar, mataimakin kakakin majalisar Mista Henry Magaji Danjuma ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta inganta yadda ake gudanar da manyan makarantun sakandire a jihar. Kudirin dokar ya biyo bayan gabatar da rahoton Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, shugaban kwamitin hadin gwiwa kan ilimi da shari’a, kuma wakilin mazabar birnin Zaria. Ya bayyana cewa dokar ta zama dole ne ta hanyar gyare-gyaren nan a tsarin ilimin Najeriya. “A da, mun gudanar da...
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano, domin bayar da takardar shaidar difloma ga masu amfani da shafukan sada zumunta da ke da hannu wajen tallata manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan a karshen taron yini biyu da aka gudanar a Kano. Kwamared Waiya ya ce horon na da nufin inganta yadda mahalarta taron ke amfani da kafafen sada zumunta wajen musayar bayanai da suka shafi ayyukan gwamnati. “Kwas din diflomasiyyar da aka gabatar zai inganta karfin mahalarta don yin amfani da dandamali na kafofin watsa labarun yadda ya kamata wajen yada bayanai kan manufofi...
A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi. Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje...
Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai. NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai...

Iran Da Kasashen Turai uku wato E3 Zasu Bude Tattaunawa A Tsakaninsu A Birnin Istambul A Gobe Jumma’a
Manya-Manyan Jami’an gwamnatin kasar Iran da tokwarorinsu na kasashen turai uku wadanda ake kira, E3 zasu fara tattaunawa a tsakaninsu dangane da tattaunawa dangane da makamashin nukliya tsakanin Iran da Amurka wanda ke ci gaba a halin yanzu. Kasashen E3 dai sun hhada da Faransa, Jamus da kuma Ingila wadanda suke sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015. Manufar taron ko kuma tuntubar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe uku itace sanyasu a kan hanya kan yadda tattaunawar take tafiya, da kuma yadda ake son a gabatar da sauye-sauye wa yarjeniyar JCPOA, tunda Amurka ta waresu daga wannan tattaunawar. JMI tana ganin idan har an cimma wata yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ba zai bambanta sosai...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB. Domin sauke shirin, latsa nan
“Ofishina ya cika da tarin jama’a suna ta kiraye-kiraye kan wannan mummunan sakamakon da aka samu a jarabawar JAMB ta 2025. “ASUU za ta kalubalanci wannan sakamakon a gaban babbar kotu idan JAMB ta gaza sake duba sakamakon da kuma bai wa dalibai makin da suka cancanta.” In ji shi Ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas da su tashi su kalubalanci abin da ya kira da rashin adalci domin hana dalibai daga shiyyar samun shiga manyan makarantu a kasar nan. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Laraba ya bayyana shirin sake gudanar da jarabawar ga dalibai da suka fito daga jihohin Kudu maso Gabas da Legas. Daga kanmu, magana ta...

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan. Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan. “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya. “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.” Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
Kasafin kudi na birnin tarayya Abuja (FCT) na shekarar 2025, kimanin naira tiriliyan 1.78 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisa, ya tsallake karatu na biyu. Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin FCT na 2025 ta wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da kudirin domin saukaka aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a babban birnin kasar. Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte Da yake karanta wasikar a zauren majalisar a ranar Laraba a Abuja, Akpabio ya bayyana cewa, gabatar da takardar ya yi daidai da sashe na 299...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Bukatar Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza. Ya yi kira da a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta tare da baiwa Falasdinawa ‘yan gudun hijira ‘yancin komawa kasarsu ta gado. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu. ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts. Ya ce...
Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025. Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar. UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale. Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da...
Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko yau aka yi zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara. Oshiomhole wanda shi ne mai wakiltar shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a safiyar wannan Larabar. DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Majalisar Dattawa ta buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa Borno da Yobe Tsohon gwamnan na Jihar Edo ya faɗi hakan a lokacin da yake tsokaci kan sauya sheƙar da Sanatocin Kebbi uku suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Ya ce, Tinubu ya ɗauki ƙwararan matakai domin daidaita Nijeriya, yana mai cewa kafin gwamnatinsa manoma a wasu sassan ƙasar...
Wannan matsala, in ji bankin, na shafar samar da abinci da kuma ƙara hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa. Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ta ɗauka tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, musamman cire tallafin man fetur da yunƙurin ƙarfafa darajar Naira. Amma bankin ya nuna cewa duk da irin waɗannan gyare-gyare, talakawa na fuskantar matsin rayuwa saboda tashin gwauron zabi da hauhawar farashin kayayyaki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan matsala, in ji bankin, na shafar samar da abinci da kuma ƙara hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa. Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ta ɗauka tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, musamman cire tallafin man fetur da yunƙurin ƙarfafa darajar Naira. Amma bankin ya nuna cewa duk da irin waɗannan gyare-gyare, talakawa na fuskantar matsin rayuwa saboda tashin gwauron zabi da hauhawar farashin kayayyaki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni ta yadda shugabanci zai riƙa kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa. Domin sauke shirin, latsa nan
Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta baiwa mutane 311 tallafi a karkashin shirin tallafa wa mata da matasa kan harkokin noma da nufin bunkasa dogaro da kai da ’yancin tattalin arziki a fadin jihar. Da take jawabi a yayin kaddamar da gagarumin bikin a Gusau, babban birnin jihar, Hajiya Huriyya ta jaddada kudirinta na gwamnati na bunkasa sabbin manoma, ‘yan kasuwa, da matasa da suka samar da su don kawo sauyi a fannin noma. Ta bayyana cewa daga cikin 311 da suka ci gajiyar tallafin, 201 mata ne yayin da 110 kuma samari ne, wadanda dukkansu za su samu cikakken goyon baya a karkashin shirin. “Kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu jarin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya wadanda suka hana da nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa. An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ya ce, “Samar da motocin aiki ga jami’an tsaron zai bayar da ci gaba wajen sawwaƙa masu zirga-zirga, kai ɗauki a kan lokaci da ƙara ƙarfafa masu gwiwa wajen samar da tsaro da bin doka da oda. “Wannan taro na yau, wani ci gaba ne na ƙoƙarin gwamnatina wajen ƙarfagawa, tare da inganta ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a duk faɗin jihar. “Wannan kuma yana ɗamfare ne da alƙawuran da muka yi, tare da jajircewar mu wajen samar da duk abin da za mu iya don tunkarar dukkan nau’o’in rashin tsaro, samar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar mu. “Wannan ƙoƙari namu yana ƙara nuna hobbasan gwamnatin mu wajen ƙarfafa wa jami’an tsaron mu don...
Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...
Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman. Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan dake addabar al’umma masu karamin karfi. Ya ce, “tun lokacin da cibiyar ta fara ayyukan jinkai don yaki da cutar makanta a Nijeriya, cikin watan Oktobar 2019, KSrelief ta gudanar da gwaje-gwajen idanu sama da 218,000, da gudanar da tiyatar idanu sama da 21,000, kuma da bayar da tallafin tabarau sama da 45,000 ga al’umma. “KSrelief ta samu karbuwa a matsayin daya daga...
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu. Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya ‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram...
Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja. Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka...

Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi. “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri. “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141. “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Idan aka ga tana da tasiri, ana iya tsawaita ko kuma daidaita matakin. Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan ci gaba zai iya taimakawa wajen farfaɗo da cinikayya tsakanin manyan ƙasashen biyu, kuma zai taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke dogara da su wajen kasuwanci da kayan masarufi. Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ya fara ne tun daga 2018 lokacin da kowanne ɓangare ke ƙara haraji a kan kayayyakin juna, lamarin da ya haifar da hauhawar farashi da rikicin masana’antu a duniya. Matakin rage harajin da suka ɗauka yanzu na iya zama sabon shafi na fahimtar juna da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ƙasashen biyu na duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna. Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol. ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano Galibin waɗanda ake zargi sun harbu da cutar an killace su a cibiyoyin lafiya a matakin farko daban-daban da kuma Asibitin Cottage inda suke samun kulawar gaggawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Bokkos, Mista Amalau Samuel Amalau wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna aiki tare da mahukuntan asibitin domin daƙile ƙalubalen A cewarsa,...
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu ta hanyar yin shawarwari da tuntuba bisa daidaito, tare da aza tubali da samar da yanayi na kara dinke baraka da zurfafa hadin gwiwa. Daga bangarenta kuwa, Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a jiya Lahadi ta bayyana cewa, ta yi farin cikin ganin an samu sakamako mai kyau yayin taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. A cikin...
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...
Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon nazari da aka yi kan mutane 2,500 a fadin kasashe 10 na Latin Amurka. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, masu bayar da amsa sun amince da manufa da nasarorin da aka cimma na zamanantar da kasar Sin, tare da gamsuwa da dangantakar Sin da kasashen Latin Amurka. Al’ummar Sin da Latin Amurka mai makoma ta bai daya na kara samun goyon baya daga mutanen yankin...

Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Bayan Taron Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun...
Sojojin sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyar da sauran makaman yaki daga a yayin artabun. Majiyoyin sojin sun bayyana cewa, farmakin wani sabon shiri ne na sake tarwatsa shirin ‘yan ta’addan da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen kai muggan hare-hare a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita. Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi. Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba. Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu. Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo. Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi. Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake...
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu. Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar. Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar. Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi. Gwamnan ya yi addu’ar...
Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan. Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara...
Lamido a ranar Lahadi ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle ta rabu gida biyu, saboda tana rungumar mutane masu tunani daban-daban. “Na fadi haka, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida, duk wadanda suka koma APC za su dawo, kuma PDP za ta farfado da karfi don kwace mulki a 2027.” A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin ta hannun sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yi watsi da ikirarin da cewa, hakan ba zai yi wu ba. Ganduje ya ce maimakon ya koma PDP, Lamido...
’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar. Wani jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ne ta wata ƙofa da ke bayan katangar makarantar. “Sun mamaye harabar makarantar sanye da cikakkun kayan ’yan sanda, da hula da takalman roba. Sun yi amfani da kofar da ke bayan katangar wajen shiga da kuma guduwa bayan harin,” in ji shi. Rahotanni sun nuna...
Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare. Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da walwala, aminci da jin daɗin alhazan Jihar Zamfara. “Gwamnatin Jihar Zamfara, a madadin al’ummarmu, ta ba ku kwarin gwiwa sosai wajen ganin an aiwatar da kowane fanni na aikin Hajjin 2025 cikin inganci, mutunci, da gaskiya. “Ina kira gare ku da ku ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙa da Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, da hukumomin Tarayyar da abin ya shafa, da...
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi. Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
“Bisa ga al’adarta hukumar, INEC za ta sanar da ranar da za ta fara sabunta katunan masu zabe a lokacin da ya dace, wanda kuma za a raba cikakkun bayanai ta shafukan sada zumunta na hukuma,” in ji Oyekanmi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona. Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona. Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama. Barça,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya. Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa. A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a...
Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI dake birnin NewYork ya kara da cewa, abin mamaki da kamfanin dilancin laraban reuters, shi ne ba wannan ne karo na farko yake yada labaran karya a duniya wanda wai yake samu daga wasu wadanda basa son a bayyana sunansu. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa bata bayan wani bangare daga cikin bangarori biyu da suke fafatawa a kasar Ukraine. Don haka bata...
A jawabinsa a wajen tarbar Jirgin Ruwan na na yankin Asia Jim Stewart, ya bayyana jin dadinsa ga Hukumar ta NPA, bisa goyon bayan da ta bayar wajen samar da kyakyawan yanayi a babban wajen da Jiragen Runwan na Tashar Onne suke tsayawa. “Muna da kyakaywar dangantakar gudanar da ayyuka da Manajan Tashar ta Onne Mista Abdulrahmon Hussain da kuma sauran ‘yan tawagar Hukumar ta NPA, “Inji Stewart. Ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancin shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, wanda kuma kashin bayan duk wata nasara da muka zamu. “Sake farfado da babban wajen tsayawar Jiragen Ruwan a Tashar Onne, hakan ya kara mana kwarin Guiwa”. A cewar Stewart. Kazalika, Stewart ya yi kira ga Gwamnatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Asabar ne kasashen Sin da Amurka suka fara wani babban taron tattalin arziki da cinikayya na matakin koli a birnin Geneva na kasar Switzerland. A matsayin shugaban tawagar kasar Sin kan harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, He Lifeng, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, ya halarci taron tare da jagoran tawagar Amurka, babban sakataren baitul-malin kasar, Scott Bessent. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya. “Na bayar da umarnin haramta sayar da da man...
Farfesa Lawan Abubakar tsohon jagora na ASUU shiyyar Bauchi shi, ya wakilci wanda ya kira taron, ya ce yadda aka yi zaben wadanda suka cancanci samun tallafin kuma an yi amfani da adalci tsakanin jinsin mace da namiji, suma wadanda suke da bukata ta musamman, saboda a taimaka masu wajen bunkasa iiminsu. Ya ce a shekaru biyu da suka gabata kungiyar ASUU ta kashe fiye da Naira milyan 164.kudaden bada tallafin karatu ga wadanda ba su da halin biyan kudin a Jami’oin da ake da su a fadin tarayyar Nijeriya. Ya ce“Kungiyarmu ta ci gaba da amfani da kuma kula da lamarin bayar da tallafin karatu na Gani Fawehinmi,tsawon shekrun da suka gabata.Ba kawai mun tsaya bane sai kawai ta...
12.Malaman makaranta suna nuna yadda muhimmnci ilimi yake. Malaman makaranta suna zama abin yin koyi musamman ma saboda lamarin ilimin da al’umma suke karuwa da shi daga gare su.Yada suka maida hankalinsu kan koyon darussan da za su koyar, hakan ya sa daliban abin ya basu sha’awa har abin ya burge su suka fara gane karfi da darajar ilimi, a rayuwa ta yau da kullum.A aji kana iya bada wani labara wanda ya shafi al’amarin iliminka, matsaloli da kuma ci gaban da ka samu ka ,bugu da kari kuma sai ka hada darussa da irin yadda abin yake a duniya, hakanan ka yi bayani kan irin ayyukan da za a iya samu ta bangaren ilimi. 13.Malaman makaranta suna...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...
A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin. Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu. Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa. Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna...

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba. Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa. A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da...
Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata. Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu. Amma duk da haka an dakatar da karatun wasu daga cikinsu zuwa wani lokaci nan gaba. Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar...
Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun. Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar...
Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni. A gun gudanar da ayyukan jinyar kyauta, kwararrun likitocin kasar Sin daga bangaren aikin tiyata na gama-gari, da aikin kasusuwa, da aikin kula da mata da na sauran sassa sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da gano cututtuka da kuma ba da jinya cikin tsari a wurin bayar da jinya na wucin gadi da rarraba magunguna kyauta, tare da ba da cikakken jagora kan yadda...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, ta yi kakkausar suka kan rufe makarantu guda 6 na MDD da Isra’ila ta yi a yammacin gabar kogin Jordan, tare da bayyana hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa ranar Alhamis 8 ga watan Mayu, Hamas ta bayyana cewa harin da aka kai kan makarantun hukumar agaji ta MDD UNRWA da ke birnin Quds da aka mamaye, da kuma rufe su da aka yi bayan korar dalibai da malamai da aka yi, ya zama harin kai tsaye ga daukacin tsarin MDD da cibiyoyinta. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, irin wadannan matakai na aikata laifuka wani bangare ne na yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi da wanzuwar Falasdinu da kuma asalinsu. Don...
Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan...
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci Mista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar. Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. Wani kwararre a kan sha’anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin...
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. An kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da...
Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya. Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu. Idan bai samu dama ba sai ya yi bayan Arfa kafin ya bar Makka. Bayan ya dawo garinsu, sai ya yi sauran azumin kwana bakwai. Jimillar azumin kwana 10 ne yake madadin hadayar da bai yi ba. Amma kuma kar ya zama Alhaji...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana tare da manema labarai bayan tattaunawa a fadar Kremlin dake birnin Moscow. Inda Xi ya jaddada cewa, a yayin da yanayin kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye da hargitsi, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su yi riko da ruhin kyakkyawar makwaftaka kuma na dindindin, da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da hadin gwiwar samun moriyar juna da nasara tare, da habaka girma, fadi da juriyar dangantakar Sin da Rasha daga dukkan fannoni, da sanya karin kwanciyar hankali ga zaman lafiya da tsaro a duniya, da samar da kuzari ga ci gaban duniya da wadata. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga...
Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal. Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya. An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Egbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa...

Aragchi: Muna Bukatar Rage Zaman Daradar Da Kuma Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Pakisatan Da Indiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni. Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar....
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...
Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka...
Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ta tokwaransa na kasar China Xi Jinping sun tattauna a birnin Mosco a yau Alhamis, inda kasashen biyu suka kara dankon zuminci a tsakaninsu, da fatan zasu bukasa harkokin kasuwanci da ci gaba a tsakaninsu nan da shekara ta 2030. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Xi Jinping ya je birnin Mosco ne don halattan bikin nasara da kasar Rasha ta samu kan sojojin Nazi a yankin duniya na biyu shekaru 80 da suka gabata. Haduwar shugabannin kasashen biyu yana zuwa ne a dai-dai lojkacinda ake kara tada jijiyoyin wuta tsakanin su da kasashen yamma musamman Amurka. Shuwagabannin biyu sun kara jaddada manufar su da samar da duniya mai kudubobi...
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar. Yace karamar hukumar ta gamsu matuka bisa yadda aikin ya gudana cikin kyakkyawan tsari mafi dacewa. Alhaji Builder Muhammad Uba ya kuma yabawa hukumar asusun adashen gata na fansho kan yadda take biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya akan lokaci ta hanyar basu hakkokin su. Shima a nasa jawabin, Daraktan kudi da mulki na karamar hukumar, Malam Haruna Ibrahim Kwaimawa ya godewa Karamar Hukumar bisa karamci data nuna a...
Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana. A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki yayi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki. Yana mai cewar, hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya-shiyya da jami’an su dukkanin kayayyakin maniyyata da dukkan sauran muhimman abubuwa daya dace. Game da...
Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA. Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi. “Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara,...
Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne. Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar. Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo. Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Kyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar...
Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje. Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito. Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin. Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani kan Houthis tare da kai hare-hare kan filin jirgin sama na babban birnin Sana’a da ke hannun ‘yan tawayen da kuma tashoshin wutar lantarki a kewayen birnin. Amurka da Houthis sun cimma yarjejeniyar sasantawa, kamar yadda Oman ta sanar a ranar Talata, inda ta ce yarjejeniyar za ta tabbatar da ” ‘yancin kewayawa” a cikin bahar maliya, inda ‘yan tawayen suke kai hare-hare kan jiragen...
An gabatar da shirin talabijin na kasa da kasa mai taken “Kalaman Magabata dake Jan Hankalin Xi Jinping” jiya Laraba a kasar Rasha, yayin da shugaban Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow domin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. Sama da mutane 200 daga Sin da Rasha ne suka halarci bikin kaddamar da shirin a Moscow. Da yake bayyana kaddamar da shirin a matsayin irinsa na 4 da aka yi a Rasha, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce shirin na wannan karo ba amfani da dadaddun labarai wajen gabatar da falsafar shugabanci na gari na Xi Jinping da dabi’un dan adam ga duniya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp