2025-05-28@17:48:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4229

«shan ruwa»:

    Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin...
    Matakin na FCTA ya kara jaddada daukar tsauraran matakai kan wadanda suka saba ka’idojin amfani da filaye a babban birnin kasar.   Jami’an sun ce, rufewar za ta ci gaba da aiki har sai an warware basussukan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa, ta kama nau’in ƙwayar Tiramol katan 491,000, tare da miƙa su ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC). An ƙiyasta kuɗin magungunan da aka kama sama da Naira miliyan 150, kuma an gano su a cikin wata mota ƙirar Lexus SUV, a hanyar Gumel zuwa...
    Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.”   Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin...
    Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA), ta rufe hedikwatar jam’iyyar PDP da ke unguwar Wuse a Abuja. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:05 na ranar Litinin. Wike ya rufe ofishin FIRS da Bankin Access kan rashin biyan haraji Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Jami’an FCTA sun isa ginin...
    Hukumar Kula da Babban Birnin (FCTA) Tarayya ta rufe ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma ginin Bankin Access kan rashin biyan haraji na sama da shekaru 25. Daraktan Kula da Filaye na Hukumar FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya bayyana cewa hukumar bin ginin da bankin Access yake bashin harajin shekara 35, ofishin FIRS...
    Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara...
    Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne. Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya...
    Kasar Uganda ta dakatar da aikin hadin giuwa na soje dake tsakanin kasashen biyu, saboda sukan da jakadan kasar Jamus yayiwa dan shugaban kasar yake kuma goyon bayan wata jam’iyyar adawar kasar. Shafin yanar gizo na labarai Afirka News ya nakalto jami’iyyar shugaban kasar Uganda People’s Defence Forces (UPDF) tana bada rahoton cewa Jakada Schauer...
    Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne...
    05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) na HKI. Inda faduwar makaman ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama a tashar.  Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Yahyah...
    Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a...
    Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da furucin ministan harkokin wajen kasarsa da ya shafi batunci ga Iran. Muhammad Tanhaye wanda shi ne mai kula da bangaren kasashen turai a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran,  ya bukaci Karin bayani...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da...
    Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar  Falasdinawa 57 Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.”  Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin...
    Jaridar ” Up Isra’el” ta buga labarin cewa; shugaban cibiyar Ayyukan Agaji A Gaza” wacce ke karkashin Amurka da Isra’ila”  ya yi murabus saboda abinda ya kira rashin gaskiya da ‘yanci a cikin Shirin. Jaridar ta ambato  Jake Wood yana cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a aiwatar da Shirin agaji a Gaza, sannan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda...
    An shiga ruɗani a unguwar CBN Quarters da ke cikin birnin Sakkwato, inda wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu mai suna Ayman Abubakar, ya ɓace, amma daga bisani aka gano gawarsa a cikin ramin sokawe. Ana zargin wani maƙwabcin iyayen yaron da wata mata da aikata wannan ɗanyen aiki. An kashe matashi yayin rikici a...
    Daga Bello Wakili Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa: Suna yin aiki ne bisa maslahar kasa, kuma ba su yarda da karbar umarni daga waje ba Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, ya ce Iran tana dogara ne kan manufofinta na kasa da kuma manufofinta na koli, kuma ba zata yarda wasu kasashen...
    Mene ne dalilin da ya sa Amurka da Isra’ila suke barazanar jefa bama-baman nukiliya a Gaza? Masanin siyasa kuma mai sharhi Abdel Bari Atwan ya rubuta labarin game da barazanar da Amurka ta yi na kai wa Gaza hari da makamin nukiliya, yana mai cewa; “Domin dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican Randy Fein ya...
    ‘Yar majalisar dokokin Ireland ta yi kakkausar suka kan shugabannin Turai tare da neman afuwa daga Falasdinawa Tana jaddada cewa: Muggan makaman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da lakume rayukan fararen hula a zirin Gaza. Sannan a wani sabon kisan kiyashi, an kashe Falasdinawa 7 a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka...
    Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa: Sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, bakar siyasa ce ta nemen bata mata suna A cikin wata sanarwa da gwamnatin Sudan ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba mata sabbin takunkumai, tana mai bayyana hakan a matsayin maimaita kura-kurai irin na baya...
    Rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa a ƙauyukan Faruruwa da Tarandai da ke Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano, inda aka kashe wani matashin har lahira. Rikicin ya faru ne a ranar cin kasuwa kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka ƙone rumfunan kasuwar. Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana...
    George Iniobong ɗan shekara ashirin da biyu daga tawagar Jihar Binuwai ya samu kyautar azurfa a gasar maza ta Judo mai nauyin kilo 60 a yau Lahadi, yayinda ake cigaba da gasar wasanni ta ƙasa karo na 22 (NSF) da ke gudana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Nasarar da George ya samu ya sa...
    An kaddamar da wani sabon babban filin wasa a birnin N’Djamena na kasar Chadi, wanda kasar Sin ta gina wa kasar kyauta. Yayin bikin kaddamarwar da ya gudana ranar Juma’a, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby, ya buga kwallon kafa da kansa, a matsayin alamar fara amfani da babban filin wasan. Cikin jawabin da ya...
    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba. Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba. Gwamnatin Gombe za ta...
    Gwamnatin Jihar Gombe, na shirin taimaka wa wata yarinya ’yar shekara 14 da aka tilasta yi mata auren dole a Jihar Taraba. Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwala, Asma’u Iganus, ta ce yarinyar ta nemi taimako bayan da kakanta ya ɗaura mata aure da wani mutum a matsayin mata ta huɗu. An kama Hakimi kan zargin...
    Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa.   Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan...
    Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.   A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai...
    “Kuma taron zai baiwa jama’a damar yi wa gwamna tambayoyi kai tsaye, kuma su sami bayani kan ayyukan gwamnati.” “Wannan shi ne ci gaba a siyasance, kuma ba sabon abu bane a duniya, amma a jihar Yobe, wannan wani sabon salo ne. Mataki ne na sauke nauyi, gaskiyar da jama’a suka baiwa gwamnati, samun hadin...
    Jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama hakimin ƙauyen Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja. Hakimin mai suna Garba Mohammed ana zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga wajen aikata ta’addanci a yankin. Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai Halin da fasinjoji ke...
    Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu...
    A jiya Asabar ce kasashen Rasha da Ukraine suka yi musayar Fursinoni a tsakanin, karon farko irinsa tun bayan fara yaki a tsakaninsu fiye da shekaru 3 da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai Arabs News ya bayyana cewa an yi musayar furisnonin ne a jiya Asabar kuma ko wace kasa ta sake fursinonin...
    Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati. Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a...
    Shugaban Wanda Alhaji Ahmed Aliyu Zarma ya wakilta ya kara da cewa, wannan cibiya ba itace ta farko ba da shugaban ya fara ginawa ba, a cewarsa ya gina irinsu a sassa daban-daban a fadin kasar nan. Yana Mai Cewa, baya ga cibiyoyin koyar da addinin musulunci ya samar da makarantu a majami’un addnin kirista...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ce, Amurka ta bayyana cewa, MDD ta ki aiki tare da kamfanonin Amurka da na Isra’ila domin raba kayan agaji a Gaza. Majiyar ta HKI ta kuma kara da cewa; An jinkirta aiwatar da Shirin na raba kayan agajin saboda wasu dalilai na kayan aiki. Wuraren hudu ne dai aka...
    Ofishin watsa labaru na hukuma a Gaza ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin jin kai, da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na doka da kyawawan halaye, su tsoma baki domin ceto da fararen hula a Gaza. Ofishin watsa labarun na hukuma a Gaza ya  kuma...
     Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da...
    Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa. Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki...
    Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya...
    Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda...
    City ta ba da sanarwa a gabanin fafatawar cewa ta shirya wani babban kyalle mai dauke da sunansa tare da sanya wa wata hanya sunan De Bruyne a makarantar horarwa ta kungiyar, Guardiola yana girmama De Bruyne sosai har ya bayyana dan kasar Belgium din a matsayin dan wasan da ya fi iya kwallo a...
    A yau Asabar ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sauka a birnin Jakarta domin ziyarar aiki a kasar Indonesia bisa gayyatar da shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya yi masa. Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indonesia sun bayar da misali kan yadda manyan kasashe masu tasowa suke aiki tare don kara karfi...
    Majiyoyin tsaro sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida kafin sanar da tsagaita bude wuta a ranar Larabar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...