2025-05-17@14:47:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1886
«Kaura»:
Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka ce. Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani. Hajj: Ranar Lahadi za a fara...
Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi wa manona da masunta aƙalla 15 yankan rago a yankin Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kulawa ta Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan na ISWAP sun kutsa yankin ne bayan zagargaza da tarwatsa sojoji suka yi wa maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa. Shaidu sun bayyana cewa a ranar Laraba...
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna,...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kiyaye ci gaba da sarrafa sinadarin yuraniyon da tushen kayan aikin makamashin nukiliya ba abubuwa ba ne da za a tattauna a kansu Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta samar da kwarin gwiwa dangane da ci gaba da zaman...
Asusun kula da kananan yara “UNICEF” na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe yara 45 a Gaza cikin kwanaki biyu kacal Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe kananan yara 45 a Zirin Gaza a cikin kwanaki biyun...
Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fira ministan Netanyahu ya yi sakaci da rayuwar yahudawa a cikin aikinsa don haka hambarar da gwamnatinsa ita ce mafita Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci...

Rikici Tsakanin Faransa Da Aljeriya Ya Shiga Wani Sabon Salo Na Koran ‘Yan Kasashen Juna Daga Kasashensu
An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa ya dawo kan gaba a fagen dakaddamar da ke tsakaninsu. Rikici dai na kara kamari ne tsakanin Aljeriya da Faransa, tun daga rikicin korar ‘yan kasar Aljeriya daga Faransa zuwa...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai 53,119 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023. Adadin ya karu ne sakamakon wasu hare-haren Isra’ila na baya baya nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 93 wayewar...
“Amma sai ku ga cewa daya bayan daya, mun magance yawancin wadannan matsalolin. Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu, amma muna kan samun nasarori.” Da yake jawabi a wajen taron, wakilin AON, Obiora Okonkwo ya yi maraba da wannan sabon ci gaban, inda ya bayyana cewa zai inganta ayyukansu. A cewarsa, “Abin da muke...
Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar ta Iran. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran da kasashen Turan uku Birtaniya da Faransa...
Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu. Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wata rubutaciyar shawara data samu daga Amurka. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya musanta ikirarin samun rubutaccen sako daga Amurka kan yarjejeniyar nukiliya. “Iran ba ta sami wata rubutacciyar shawara daga Amurka ba, kai tsaye ko a kaikaice,” in ji Araghchi a cikin wani sakon da...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar...
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriryar musulunci ta Iran ta sanar da cewa, saboda yadda Amurka take bai wa ‘yan sahayoniya cikakken goyon baya ne, ya sa su cigaba da aikata laifuka na kisan kiyashi akan mutanen Gaza. Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta fitar, ya zo ne saboda tunawa da zagayowar lokacin da aka...
Shugaban hukumar Spain Pedro Sanchez ya bayyana ” Isra’ila” da cewa; “Mai Kisan Kiyashi Ce,” wacce kasarsa ba za yi mu’amala da ita ba. Fira ministan na kasar Spain ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martnni ga wani dan majalisar kasar daga yankin Catalonia, Gabrel Rovian yana wanda ya tuhume shi da cewa,...
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake yammacin kasar. Majiyar tsaron ta Yemen ta ci gaba da cewa; An yi amfani da bama-bamai masu yawa da aka jefa akan wadannan tasoshin jiragen ruwan,kuma fiye da jiragen sama...
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra. Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce. Ita kuwa hukumar kasar ba ta...
Firaminista Li ya nanata cewa, ya kamata dukkan sassan gwamnati da larduna su karfafa tsara manufofi da aiwatar da su, da inganta hadin gwiwa, domin kyautata kuzarin kasuwa da warware matsalolin al’umma yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
A ranar Asabar ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya bisa gayyatar da sabon Fafaroma Leo XIV ya aike masa. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya sanar da cewa, shugaba...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa. An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002. Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin...
Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chikuriwa da ke Ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa...

Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista
“Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.” “Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more...
A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen...
Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata. Wato...
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun...
Jakadan JMI a MDD ya bayyana cewa ranar Nakba ko musiba ga Falasdinawa, abin bakinciki ba karshen musubar ba ce sai faraway ne, don a yau shekaru 77 da suka gabata kenen da musibar da ta faru da Falasdinawa tana ci gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Sa’id Iravani yaana...
Kyaftin Shehu Iyali, tsohon mataimaki na musamman kan sufurin jiragen sama a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, ya rasu. Kyaftin Shehu Iyal ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya yi fama da jinya. Kafin rasuwarsa shi ne shugaban kamfani jiragen sama mai suna Afri Air. Marigayin yakasance jigo a harkar...
Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma. Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar...
Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Imanin Iran Da Tattaunawan Zaman Lafiya Amma Ba Za Ta Amince Da Barazana Ba
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke...

Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Rundunar sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami Rundunar sojin Yemen ta sanar da kaddamar da farmakin soji kan babban filin tashin jiragen saman Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma yin nuna...
A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000. Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna...
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC reshen shiyyar Kaduna ta gurfanar da wani Muhammad Kabir a gaban kotu tare da yanke masa hukunci, wanda ya kasance mai wallafa bidiyo a shafukan TikTok da Instagram. An gurfanar da Muhammad Kabir a gaban mai shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba yaki ba. Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba; Su ne ke haifar da rikici. Muna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar nan da ma makwabtanmu,...
Iran ta bayyana cewa za ta yi zama gobe Juma’a da kasashen nan na turai guda uku da ake kira E3, wato Biritaniya, Jamus da kuma Faransa kan shirinta na nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa, a ranar Juma’a 16 ga watan Mayu ne za a yi shawarwari karo na...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin...
Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai...
Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita. Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da jagoran da ya kafa majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin ya aike masa, yana mai karfafa gwiwar cibiyar da kamfanoni mambobinta, da su samar da sabbin gudummawar raya alakar Sin da Denmark, da kawancen Sin da Turai, kana su zurfafa hadin gwiwa na cimma...
A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini. Dr. Baka’i ya yi ishara...
Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da...
A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar. Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen...
Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za...