2025-05-04@07:50:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3419

«duban wata»:

    Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba. A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga...
    Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa 52,495 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a jiya Asabar 3 ga watan Mayu, shekara ta 2025 cewa: Falasdinawa 77 ne da suka yi shahada da suka hada da gawarwakin mutane 7 da aka...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar. A cikin wata...
    Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta miƙawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON kuɗi sama da Naira biliyan 6 a matsayin kuɗin jigilar maniyyatan jihar na 2025 na zuwa Saudiyya. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Labbo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a...
    Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas. Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar. ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe  An kama masu garkuwa...
    A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.   Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da...
    ’Yan ta’addan Boko Haram da suka kai hari kan rundunar soji ta 27 da ke Buni Yadi a jihar Yobe, sun kashe akalla sojoji hudu tare da lalata kayan aiki da dama na soji. An kai harin ne kafin wayewar garin Asabar, jim kaɗan bayan da Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta gana a Damaturu...
    Ƙungiyar mayaƙan ISWAP sun mamaye garin Buni Gari a daren Juma’a da ƙarfe 12:00 na dare, mahaifar Gwamna Buni da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe inda suka kai wani harin ba zata a garin da kuma barikin soja ta 27 da ke garin. Wata majiya mai tushe daga garin ta tabbatar da cewa, lamarin ya...
    Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon. Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba. A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa...
     Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Manufar HKI akan Syria a fili take ba a boye ba.” Baka’i ya ci gaba da cewa; Manufar HKI  ita ce rusa duk wani karfi da Syria take da shi na yaki, da kuma lalata tattalin arzikinta, domin share fagen shimfida iko...
    Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450. Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin. Gwajin makamin na...
    Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga HKI da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa kasar Syria,jim kadan bayan da sojojin HKI su ka sanar da cewa; a karon farko jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniya ya sauka a Suwaidah.  A daren jiya Juma’a ne dai HKI ta kwana tana luguden wuta...
    Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sashen tawagarta masu tattara bayanan sirri (IRT), ta kuɓutar da wasu ’yan ƙasar Ghana biyu da aka yi garkuwa da su tare da damƙe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a kan iyakokin ƙasashen duniya. Rundunar ’yan sandan a ranar Juma’ar  ta ce hakan...
    “Ka san idan za ka yi la’akari da sauran jihohin da suke barin jam’iyyarsu su shiga wata jam’iyya ni a tunanina tsoro ne karawa da babban jam’iyyar adawar da ke jihar ba, yanzu misali a Jihar Delta shi gwamnan jihar ya san daker ya ci zabe a 2023 sannan kuma yana da yakinin idan bai...
    A daya bangaren kuma, sashen sufurin jiragen kasa na Sin, ya gudanar da zirga-zirga kusan miliyan 23.12, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka nuna.   Har ila yau, idan an kwatanta da tafiye-tafiye masu cin gajeren zango da Sinawa suka fi...
    Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su. An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin. ’Yan...
    Ta ce: “Zargin da aka yi na cewa na shirya ficewar matan daga bikin Uwargidan Gwamna a ranar 2 ga Mayu 2025, karya ce kawai. Ba ni da hannu a cikin wannan lamirin kuma wannan ƙarya ce ta masu tada hankali.   “Na kasance na mai da hankali ne kan karatuna na digiri na uku...
    Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau.   Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da...
    Wasu daga cikin manoman a wadanan yankuna sun bayyana cewa, sun koma neman wasu gonakin da za su yi shuka ko dai a cikin jihar ko kuma a wasu guraren daban, musamman duba da cewa; sun dogara ne a kan wadannan sana’o’i na noma da kamun Kifi. Koda-yake dai, gwamnatin tarayya ta yi wani gini...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri. An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata. Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an...
    Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙwato dazuzzuka da sauran yankuna a Arewa-Maso-Yamma da sauran sassan Nijeriya, yayin da yake jawabi a wata liyafa da tsofaffin shugabannin Katsina suka shirya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar sa ido don yaƙar ta’addanci da ƴan fashi. A cewar sanarwar kakakin shugaban ƙasa, Tinubu...
    Wadanda ake tuhumar dai sun tabbatar wa kansu aikata laifin ba tare da kara yin wata shaida ba. Duk da haka, a kokarin janye ikirari nasu, sun yarda cewa abokai ne kuma suna zaune tare a wurin da suka aikata laifin, kuma aka kama su tare. Tawagar masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Zainab...
    Cibiyar samar da kyakyawan yanayin yin kasuwanci na Fadar Shugaban Kasa da hadaka da NPA ne, suka shirya taron kaddamarwar,   “Ana sa ran a zangon farko na 2026, aikin na NSWP zai fara fara aiki wanda tuni, Fadar Shugaban Kasa ta amince da kwangilar domin a wanzar da aikin,” Inji Dantsoho.   Ya kuma...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean (Euro-Med) ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani jirgin ruwan Freedom Flotilla da ke dauke da kayan agaji zuwa zirin Gaza da aka yi wa kawanya. An kai harin ne a ruwan kasa da kasa...
    “Manchester United ce fa kowane dan wasa na hankoron taka wasa a cikinta kuma idan kuka duba kungiyar a yanzu, kamar akwai matsaloli, ciki har da sauya koci da aka yi amma duk da haka muna da masaniyar abin da ya kamata, kuma abu ne mai sauki a ganar da dan wasa” in ji Amorim,...
    Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron...
    A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a...
    Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar...
    A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce...
    Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya soki mummunar rawar da Faransa ke takawa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki kasar Faransa saboda abin da ya bayyana a matsayin gurgunta rawar da take takawa a kokarin diflomasiyya kan matsayin Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. A wani rubutu da ya yi a...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da kai hare-haren da sojojin Amurka suka kai cikin sa’o’i 24 da suka gabata kan yankuna daban-daban na lardin...
    Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka...
      Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa...
    Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar.   Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa...
    Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere,  ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana...
    Gwamnatin HKI ta kai farmaki kan tawaga masu rajin kare hakkin bil’adama dauke da kayakin agaji a cikin jirgin ruwa dauke da kayakin agaji zuwa zirin Gaza wacce ta hana shigar abinci cikinsa kimani watanni biyu da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin tsibirin Malta na cewa HKI...
    Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen...
    Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar sannan da kokarin fasa korinsu zuwa wajen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an lama manjo polo ne da makamai wadanda suka hada da MK-47...
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan...
    “Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya...
    Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato motocin sata guda 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi. Kwamishinan ’Yan sanda CP Ajoa Saka Adewale, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar...
    Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana.   A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau...