Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai
Published: 8th, March 2025 GMT
Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC
Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar.
A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar mutane akalla sama da 1,000.
Kwana-kwanan ne, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin fadin jihohi 11 cikin mako shida daga 3 zuwa 9 ga watan Fabrairun 2025, bayan barkewar cutar a 2024, da sama da mutum 4,726 da suka kamu da cutar, inda dama daga cikinsu suka mutu.
Har wa yau, a rahotonta na baya-bayan nan, game da cutar zazzabin Lassa, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar da sun kamu da cutar a jihohi 11 da suka hada da; Ondo, Taraba, Edo, Benuwe, Gombe, Kogi da kuma Ebonyi, inda ta ce; adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da kashi 19.4 cikin 100, daga kashi 17.5 cikin 100, duk dai a cikin shekarar 2024.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, kashi 73 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, sun fito ne daga Jihohin Ondo, Edo da Bauchi, in Ondo ke kan gaba da kashi 34 cikin 100, sai Edo da kashi 21 cikin 100, Bauchi kuma da kashi 18 cikin 100, inda ta bayyana cewa; adadin adadin kananan hukumomi 63 da ke cikin jihohi 11, sun tabbatar da kamuwa da cutar.
Har ila yau, NCDC ta kara da cewa, ba a samu rahoton ko mutum guda cikin ma’aikatan lafiya da ya kamu da cutar a cikin wannan makon ba. Kazalika, jinkirin gabatar da kararraki, ya taimaka wajen karuwar mace-macen da tsadar kudin magani da kuma karancin wayar da kan al’umma.
Matakan Da Aka Dauka
Domin magance barkewar cutar, NCDC ta ce; ta farfado da sakatariyar da ke kula da tsarurrukan da suka shafi wannan cuta ta zazzabin Lassa ta kasa (IMS), domin samun daidaito a ayyukan.
Ta kara da cewa, ta yi hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Bincike ta Kasa da Kasa da wasu Cibiyoyin, don bunkasa hanyoyin gane cutar da kuma magance ta ba tare da wani bata lokaci ba.
Sannan, hukumar ta bukaci ‘yan Nijeriya da su dauki matakan kare kawunansu da suka hada da kula da tsafta, gujewa cudanya da berayen da ke dauke da cutar da kuma neman magani da wuri da zarar an ji alamu kamar na zazzabi, ciwon makogwaro da kuma zubar da jini babu gaira babu dalili.
Hukumar ta NCDC, ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen kamuwa da cutar, musamman ta hanyar adana abincin da aka rufe a cikin kwantena yadda ya kamata, don hana bera shiga. Kazalika, ta karfafi ‘yan Nijeriyan da su rika sanar da su tare kuma da daukar matakan kare kawunansu da sauran ‘yan’uwansu.
Hanyoyin Da Za A Bi Don Kare Kai
A wata hira ta musamman da aka yi da jaridar Blueprint, wani Farfesa a fannin cututtuka masu yaduwa da kwayoyin halitta a sashen nazarin halittu na Jami’ar Adeleke, Oladipo Kolawole ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su inganta tsarin sa ido, domin ganowa da kuma bayar da rahoton bullar wannan cuta ta zazzabin Lassa.
Ya ce, kamata ya yi a tabbatar an samu wadataccen sinadarin ‘ribabirin’, wanda shi ne maganin cutar zazzabin Lassan na farko, wanda hakan zai karfafa tare da taimakawa wajen warkar da masu dauke da cutar.
A cewar Farfesa Kolawole, gwamnatin tarayya karkashin Hukumar NCDC, na taka muhimmiyar rawa wajen daidaitawa tare da sa ido da ganowa da kuma mayar da martani a dukkanin fadin wannan kasa.
Ya kuma jaddada cewa, don gujewa barkewar zazzabin Lassa, ‘yan kasar za su iya daukar matakan kariya da dama, kamar gujewa cudanya da beraye, adana abinci da sarrafa shi yadda ya kamata, kasancewa cikin tsafta, gujewa cudanya da wadanda suka kamu da cutar da kuma wayar wa jama’a kai a koda-yaushe, domin kai kawunansu asibiti da wuri.
Kazalika, don rage barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohi kamar su Edo, Ebonyi, Ondo da kuma Bauchi, Farfesan ya bayyana cewa, za a iya daukar matakai da dama da suka hada da karfafa tsarin sa ido da shigo da al’umma ciki, domin samun hadin kai da kuma kokarin daukar matakan kariya.
Wadane Matakai Ya Dace Gwamnati Ta Dauka
Wani likita mazaunin Birtaniya, a makarantar Chebening, wanda kuma ya kafa gidauniyar kiwon lafiya ta yara, Dakta Christian Inya Oko, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara zuba kudade tare da aiwatar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen shawo kan wannan cuta ta zazzabin Lassa yadda ya kamata. Ya ce, ya rasa abokansa likitoci da dama sanadiyyar wannan cuta, baya ga sauran ‘yan Nijeriya da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya ce, “Bayan mutuwar abokaina likitoci uku tare da wasu ‘yan Nijeriya sama da 800 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, na kadu matuka da jin rahoton NCDC na baya-bayan nan. A rahoton shekara ta 2024, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bayar da rahoton kusan mutum 1300 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, kashi 16.3 cikin 100 na mace-mace, wato mutum 214 da suka mutu a jihohi 28.
Jihohin Edo, Ondo da Bauchi ne ke kan gaba a jerin sunayen, yayin da Taraba, Ebonyi, Enugu da Filato, su ma suka bayar da rahotanni marasa dadi. A cikin mako na shida na 2025, an samu mutuwar mutum 80 cikin mutum 413 da suka kamu da cutar a jihohi 28 tare da karin mutuwar mutum 10 a cikin wannan makon.
“Idan aka yi la’akari da wannan kididdigar, akwai bukatar kara ingancin matakan da ake amfani da su wajen kokarin dakile wannan cuta ta zazzabin Lassa. Zazzabin Lassa, wani muhimmin al’amari ne da ya shafi lafiyar al’umma a Nijeriya da ake fama da shi”, in ji shi.
Dakta Oko ya yi nuni da cewa, ya kamata a samar da hanyoyin horar da ma’aikatan kiwon lafiya a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da na sauran manyan makarantu, don ganowa da magancewa da kuma kaucewa ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka. Marasa lafiyan da aka gano suna dauke da cutar, ya kamata a ba su kulawa ta musamman, ta hanyar ba su magunguna da sauran abubuwan da suka dace, har sai sun warke.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wannan cuta ta zazzabin Lassa da suka kamu da cutar cutar zazzabin Lassa sun kamu da cutar bayar da rahoton kamu da cutar A kamu da cutar a da aka tabbatar barkewar cutar mutuwar mutum yan Nijeriya bayyana cewa Nijeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
Masana Kimiyya Na Sin Sun Gano Tsare-Tsaren Rayuwa A Muhallin Halittu Mafi Zurfi A Teku
A wani bincike mai kayatarwa da wani rukuni na masana kimiyya na kasar Sin ya gudanar, ya gano wasu tsare-tsaren gudanar da rayuwa, a muhallin halittu mafi zurfi cikin kwarin teku da ake cewa “Mariana Trench”. Wurin da ake ganin shi ne mafi zurfi a sassan tekunan duniyar nan.
Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar “journal Cell”, cikin wasu takardun bincike 3, ya bayyana cewa, ta amfani da na’urar nutso a karkashin teku mallakin kasar Sin mai suna Fendouzhe, masu nazarin kimiyyar sun gano tsare-tsaren gudanar rayuwa na musamman, da ma albarkatun dake tattare da kananan halittu dake rayuwa a wurin mai tsananin zurfi, da halittu dangin kaguwa, da dangin kifaye dake wurin.
Kazalika, sakamakon binciken ya baiwa bil adama damar kara fahimtar yanayin rayuwar halittu a muhallin karkashin teku da zurfinsa ya kai mita 10,000, yayin da nau’o’in kwayoyin halittu, da yanayinsu, da tasirin rayuwarsu, ka iya baiwa masu bincike damar gudanar da nazari bisa sabbin kirkire-kirkire, ta yadda za a kai ga magance tarin kalubale masu nasaba da albarkatun halittu masu rai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp