2025-03-09@12:07:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1811

«sun kamu da cutar»:

    Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila. Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun. Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin...
    Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar  ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku. Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne...
    Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma kungiyoyin da suke kawance da su da suka da alaka da alkaida, sun kashe fararen hula 745 na Alawi a cikin kwanaki uku da suka gabata, wanda ya haura adadin da aka sanar a lokutan baya. Sai dai Fox News ta buga misali da wata ‘yar Alawiyya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne aka kiyasta an kashe...
    Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya. Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba. Kakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya. Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin shigar da maganin cikin ƙasar akan lokaci, kuma a watan Janairu aka amince da hakan. Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da...
    Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
    Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu. Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati. Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da...
    Senegal ta karbi wasu sansanonin soja na faransa a kasar a wani bangare na janye sojojin faransar daga kasar ta Yammacin Afirka. Ofishin jakadancin Faransa a Dakar ya sanar da cewa an mika wurare da gidaje a yankunan Marechal da Saint-Exupery na Dakar ga hannun gwamnatin Senegal. Sauran kuma “za a mika su ne kamar yadda bangarorin biyu suka amince da jadawalin da suka sanya wa hannu”. A ranar 12 ga Fabrairu Faransa ta sanar cewa ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa da Senegal da zai shirya tsare-tsaren ficewar sojojin Faransa da kuma mika sansanonin zuwa karshen shekarar nan.  “Kwamitin ya kuma kaddamar da aikin yin garen-bawul ga hadakar tsaro,” a cewar sanarwar. A watan Nuwamban 2024 ne Shugaba...
    Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa gomman mutane ne sukayi shahada a sabon rikicin da ya barke a baya baya nan a wasu sassan kasar. Majiyoyin cikin gida na kasar sun tabbatarwa da tashar Al-Mayadeen cewa, a safiyar Asabar an yi ta kashe-kashe a kauyuka da garuruwa da dama a yankunan karkarar Latakia, Tartous da kuma Hama. Majiyar ta yi nuni da cewa an yi wani kisan kiyashi a kauyen Al-Sanobar da ke gundumar Jableh. A cewar wani rahoto na wucin gadi, an kashe mutane 72. An tabbatar da mutuwar wasu mutane 10 a kauyen Harisoun da ke cikin karkarar Baniyas a cikin gundumar Tartous. A sa’i daya kuma, kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Syria (SOHR) ta yi...
    Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna: Muhimmancin sadaka na da yawa baya ga kariya da take yi, sadaka tana hana bambancin da ake yi tsakanin mai kudi da kuma talaka, sadaka tana hada kan al’umma musulmi guri daya, tana taimakawa marayu, masu takaba da manya wadanda suka manyanta wajen nuna musu cewar suma suna da gata, tana kuma kusanto mutum da Allah ta’alla. Wadanda ya kamata a bawa sadaka; Marayu, iyalai masu karamin karfi, masu takaba, ‘yan gudun hijra, dalibai da sauransu. Hanyoyin bada sadaka na da dumbin yawa kamar; bada sadaka ta hanyar bada kudi, yinta ta hanyar dauke abu daga kan hanya wanda zai cutar da dan’Adam, hada kungiya ko kirkirar kungiya ko bada gudunmawa a kungiyar...
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1 BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 1 Sharhi: Shehun malami Ibnu Juzai (Allah ya yi masa rahama) yana bayani a nan game da ma’anar Tafsiri, wanda ke nufin fassara da ƙarin bayani kan ma’anonin ayoyin Alƙur’ani. A bisa wannan magana, ana iya fahimtar cewa: 1. Tafsiri yana nufin bayani da sharhi na Alƙur’ani – Wato fassara da bayanin ma’anar ayoyi domin su fi zama a fili ga masu karatu da sauraro, don su fahimci saƙon da ke cikinsu. 2. Tafsiri yana bayyana ma’anar ayoyi dalla-dalla – Manufarsa ita ce kawar da ruɗani da kuma hana kuskuren fahimta. 3. Hanyoyin bayani a tafsiri suna da matakai daban-daban: Ta lafazin ayar kai tsaye (بِنَصِّهِ) – Wato bayani...
    Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...
    Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara.   “Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara. Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka.   “Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.”   Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da...
    Yanzu haka adadin matan kasar Sin mamallaka sana’o’i na ta karuwa sannu a hankali, inda ya zuwa yanzu mata ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai inganci a kasar. Wasu alkaluma daga hukumar lura da hada hadar kasuwanni ta kasar sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, adadin kamfanoni da matan kasar Sin suka zuba jari sun haura miliyan 23, adadin da ya kai kaso 41.6 bisa dari cikin jimillar kamfanonin kasar masu zaman kan su. Alkaluman sun nuna adadin hada-hadar kamfanoni masu jarin matan kasar Sin na ta karuwa, da kimanin kaso 9.8 bisa dari a duk shekara tun daga shekarar 2012, a gabar da karin mata ke kafawa, da zuba jari a kamfanoni daban...
    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Nijeriya a ƙarshen makon nan. Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba. Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Kakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya. Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin...
    3- Rubewar hakora 4- Barazanar kiba 5- Barazanar ciwon zuciya da jijiyoyin jini 6. Barazanar ciwon siga (nau’i na biyu) 7- Haddasa kumburin jiki 8- Barazanar ciwon kashi da gabbai (rheumatoid arthritis) 9- Ciwon daji ko kansa da dai sauran makamantansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Asabar ne aka gudanar da zama na biyu na taro na uku, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Zaman da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarta. Albarkacin kasancewar yau ranar bikin mata ta kasa da kasa, a madadin tawagar shugabannin taron, zaman ya mika fatan alheri ga mata daga dukkan kabilu, da dukkan bangarorin kasar Sin, da mata na dukkan kasashen duniya. Bugu da kari, rahoton ayyukan zaunannen kwamitin NPC ya nuna cewa, ana shirin bitar dokoki 34 a shekarar nan ta 2025, wadanda suka hada da samar da wata doka, don inganta hadin...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Ayatullah sayyid Aliyul Kahaminae, ya bayyana cewa tursasawa kasar Iran ta shi tattauna da gwamnatin Amurka ba abin amincewa ba ne, kuma yin hakan ba zai warware matsalolin da ke tsakaninsu ba. Tashar talabijinta Presstv a nan Iran ta nakalto Jagoran ya na fadar haka a yau Asabar a lokacin da yake ganawarsa, da shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan da alkalin al-kalan kasa Muhsen Ejei da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Bakir Qalibof da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar da dama a gidansa. Jagoran ya kara da cewa ba matsalar makamashin Nukliya ne suke bukatar tattaunawa da Iran ba, sai dai suna su tilastawa kasar Iran ra’ayinsu, a cikin dukkan al-amuran...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
    Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma yi kira ga Amurka da Iran su warware wannan matsalar ta ruwan sanyi. Ko hanyar diblomasiyya. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa shirinta na makamashin na zaman lafiya ne. Sannan don haka ne ta amince ta kulla yarjeniyar shirin nukliya ta zaman lafiya  da manya manyan kasashen duniya, a shekara ta 2015 daga ciki har da kasar Amurka. Amma shugaban kasar Amurka na lokacin Donql Trump ta fidda kasar daga yarjeniyar sannan ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni don tursasa mata ta sake zama don sabuwar tattaunawa da ita. Mohammed...
    Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran. Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna da kekyawar kariya daga makamai. Don haka da sauki makiyammu ba zasu cutar da cibiyoyin ba. Ministan ya bayyana haka ne a taron kasashen musulmi na OIC wanda aka gudanar a birnin Jedda na kasar Saudiya a yau Asabar. Ya ce iran zata ci gaba da neman fahintar juna ta hanyar diblomasiyy, Amma idan sun dage zasu yi amfani da karfi to Iran a shirye...
    Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu. Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris. NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa SP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47. Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, wadda shugabanta, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna. Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol NMDPRA ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man ne a jihohin Abia da Delta da kuma Edo. “Za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a Jihar Edo. “Za kuma a buɗe Matatar MB wadda za...
    C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai. 5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa. Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai. Idan ya yi kauri da...
    Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar. “An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya. Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na Maris, zai kuma kunshi karin kaso 100 bisa mai rapeseed, da tunkuza, da waken peas, yayin da kuma albarkatun teku, da naman alade da ake shigarwa Sin daga Canada, aka yi musu karin harajin kaso 25 bisa dari. Mahukuntan kasar Sin sun ce matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da nuna banbanci a hada-hadar cinikayya, wanda ya tabbatar da cewa, matakan da...
    5. Damfara da Alkawurra na Bogi: Wasu na bayar da alkawurran aure da ba su da gaskiya don cimma wasu burika nasu. Yadda Za Ka Kare Kanka • Ka guji aika hotuna na sirri ko bidiyo ga wanda ba ka sani sosai ba. • Kar ka yarda da duk wani alkawari da ba ka tabbatar da gaskiyarsa ba. • Ka duba asalin mutum kafin ka yi amanna dashi da bayanan ka. • Yi taka-tsantsan da sakwannin da kake fitarwa a yanar gizo. • Ka daina amfani da intanet wajen yin mu’amala da wanda ba ka da isasshen sani a kansa. • Idan kana fuskantar barazana, ka sanar da hukuma ko wani da ka yarda da shi. Labari Domin Karfafa Gwiwa...
    “Wadanda aka samu da laifi doka za ta hukunta su. “Ayyukan sun kai ga kwato tarin muggan makamai, haramtattun abubuwa, da abubuwan da ke da alaka da aikata laifuka. Wadannan sun hada da busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi ne, gatari uku da adduna uku, wadanda galibi ake amfani da su wajen aikata munanan laifuka. “Kananan bututu guda shida na manne, bongs din hannu guda biyar, kayan da aka fi hadawa da abubuwan maye, almakashi guda takwas, katunan ID guda biyar, kananan kwantena na filastik da yawa da wasu kwayayen da ake zargin haramun ne. “Rundunar ta kuma kara sanya ido kan gine-ginen da aka yi watsi da su da kuma wuraren da aka gano a matsayin maboyar masu...
    Da yake magana kan aikin, Hundeyin ya bayyana cewa, kungiyoyi masu amfani da dabaru da ke Elemoro ne suka yi kamen, inda suka rufe hanyar Ajah, ciki har da Lekki Phase 1 zuwa Epe. “Tawagarmu ta dabara da ke Elemoro ce ta gudanar da wannan aiki tare da rufe adis na Ajah, kamar Lekki Phase 1 zuwa Epe. Sun gudanar da wannan aiki. Aanu Ayoade, Aminu Abubakar, Olayiwola James, Sahedu Abubakar, Taiwo Fawasi, Muhammed Monsuru, Abdullahi Ibrahim, Uche Achuoye, Samuel Olapade, El-Kamal Ibrahim, Hammed Taofeek, and Jamilu Usman. “Muna da kungiyoyin dabaru a wasu sassan jihar, kuma suma suna da irin wannan na kama masu aikata laifuka tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu,” in ji...
    Daga ƙarshe sanarwar ta ƙara jaddada ingantattun ƙa’idojin karatu a BUK, wanda ta ce ba za ta lamunci satar jarrabawa ko laifuffuka makamantan haka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu kwararru a fannin na aikin noman, sun alakanta samun wannan karuwar, saboda dauki daban-daban da gwamnatin tarayya ta samar ga fannin, musamman wajen kokarinta na rage kalubalen rashin tsaro. Daga cikin wannan daukin na gwamnati, sun hada da kirkiro da shirin jami’an tsaro na sintiri sama da 1,000 da aka tura zuwa kanannan hukumomi 19 a 2024, don bai wa manoma da amfanin noma da aka shuka kariya, inda shirin ya taimaka wajen kara bunkasa aikin noma. A cewar Hukumar ta ‘NBS’, fannin aikin noma ya samar da kashi 25.59 wajen habaka fannin tattalin arzikin kasar, wato ma’ana, a zango na uku na 2023, gudunmawar da fannin ya samar ga tattalin arzikin kasar, ya tsaya ne a kashi 26.11,...
    Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin kiwon dabbobi. Shugaban ya yi fatan nadin Farfesa Jega zai haifar da ci gaba mai ma’ana a fannin kiwo, da kuma kara karfafa ayyukan ci gaban kasa. Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Jega ne ya jagoranci Kwamitin Kiwo na Shugaban Kasa tare da Shugaba Tinubu. Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya bayar da cikakkun shawarwarin da suka tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a fannin kiwon dabbobi, daya daga cikinsu shi ne...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ja hankalin shugabannin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma  da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana domin samun goyon bayan gwamnonin shiyyar. Gwamna Umar Namadi ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada a gidan gwamnati da ke Dutse. Ya ce, Hukumar Raya Arewa maso Yamma, ita ce mafi girma a cikin shiyyoyin kasar nan, a don haka bai kamata a fuskanci wasu matsaloli  ba daga gareta. Namadi ya bukace su da su mai da hankali da jajircewa, tare da yin aiki da abubuwan da gwamnoni suka sa gaba domin samun nasara. Tun da farko, Shugaban Hukumar, Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya ce...
    “Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun. Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane. Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi. Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo. Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya...
    Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla. Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus. Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin. Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci...
    Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar. Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.6. “Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya. Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin...
    Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin zaman lafiya a yankin da kuma kara tunzura Isra’ila. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na nuna damuwa kan rashin tsaro, tashe-tashen hankula, zubar da jini da cutar da al’ummar Siriya da basu ji basu gani ba. Ita ma ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta bayyana matukar damuwarta kan halin da ake ciki a makwabciyarta Syria, tana mai jaddada cewa...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta rufe wani shagon da ake yin caca na zamani, wanda aka fi sani da “betting. Mataimakin kwamandan hukumar a Kano, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano. Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95  Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bisa dokokin Jihar Kano, kuma hukumar ta kai samame wajen kafin ta rufe shagon gaba ɗaya. Aminudeen ya nuna damuwa kan yadda wasu Musulmai ke shiga harkar caca, musamman a lokacin azumin watan Ramadan. A watannin baya hukumar ta haramta yin cacar “betting” lamarin da ya sanya ta fara farautar wuraren...
    Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar. A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar mutane akalla sama da 1,000. Haka nan kuma, a shekarar 2018 an sake samun bullar cutar a kasar, inda mutane sama da 1,500 suka kamu da cutar, sannan adadin wadanda suka kamun sun doshi kashi 20 cikin 100. Kwana-kwanan ne, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin fadin jihohi 11 cikin mako...
    “Bisa ga ajandar sabunta fata na Shugaba Tinubu, mun himmatu wajen tabbatar da manufofi da ka’idojin da suka jagoranci hukumar tsawon shekaru. “Ina kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya, musamman maniyyatan da suka yi niyyar zuwa aikin hajjin 2025, za su gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da NAHCON bisa sakamakon aikin hajjin 2025. “Shugaban kasa yana tsayawa kan Magana daya. Yana ba mu dukkan goyon bayan da ya kamata. Ba za mu ci amanarsa ba. Ba za mu sauka daga kan manufarmu ba. “A kan wannan, dole ne mu gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima bisa yadda suka ba mu amanar tafiyar da harkokin aikin hajji. “Hukumar ta samu wasu nasarorin da suka shahara...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
    Rikicin ya fara ne tun bayan tsige Obasa a ranar 13 ga Janairu, 2025, a matsayin shugaban majalisar. ‘Yan majalisa 33 a zaman da aka yi a wannan rana suka tsige Obasa tare da ayyana tsohowar mataimakiyar shugaban majalisar, Merand a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar Legas. Ko da yake ’yan majalisar sun yi nuni da cewa yana cin zarafin mukami da karkatar da kudade da kuma rashin da’a a matsayin wani bangare na dalilan tsige Obasa, matakin ya nuna asalin rikicin da ya barke a majalisar ta 10 a jihar. ‘Yan majalisar dai sun tsige Obasa ne a lokacin da yake kasar Amurka. Bayan dawowarsa Legas a ranar 25 ga Janairu, 2025, ya kalubalanci cire shi. Duk da tsoma...
    Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori. Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a wannan Juma’a a gefen taron gaggawa karo na 20 na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah. A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan matsayin dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma masarautar Saudiyya, tare da jaddada aniyar kasashen biyu na ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakaninsu. Bangarorin biyu sun kuma yi nazari...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin Mashawarci kuma Mai Kula da Shirin Gyaran Noma da Kiwo na Shugaban Ƙasa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da naɗin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a Kebbi Zan sasanta Akpabio da Natasha — Ministar Harkokin Mata Shugaba Tinubu na fatan wannan naɗi zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da ƙarfafa yunƙurin raya ƙasa. Farfesa Jega, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne, ya kasance mataimakin shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Noma da Kiwo tare da Shugaba Tinubu. Kwamitin ya gabatar da shawarwari masu...
    Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila. A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da  Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi. Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan harkokin satar ma’adinai. A cewar gwamnatin, cikin wadanda aka kama 320, kusan mutum 150 a halin yanzu suna fuskantar shari’a kuma wasu guda tara an dauresu, inda su kuma mutum hudu ‘yan kasar wajen aka dauresu a gidan yari. Ministan bunkasa albarkatun kasa, Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartarwa na tarayya...
    Jami’an tsaro da ’yan sa-kai sun kashe shugaban ’yan ta’addan Lakurawa, Maigemu, a Jihar Kebbi. Daraktan Tsaro na Jihar Kebbi, AbdulRahman Usman Zagga ne, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa an kashe Maigemu a ranar Alhamis. PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja Ya ce an kashe shi ne yayin musayar wuta da jami’an tsaro a garin Kuncin Baba da ke Ƙaramar Hukumar Arewa. Mutuwarsa ta zo ne mako guda bayan da Gwamna Nasir Idris ya kai ziyarar jaje ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade, inda ’yan ta’adda suka kashe mutum shida. “Ƙoƙarin gwamna ya haifar da ɗa mai ido, domin yanzu...
    Ya bayyana cewa samun damar karɓar baƙuncin wannan babban taro wata gagarumar nasara ce ga Nijeriya, kasancewar ita ce ƙasar Afirka ta biyu da za ta karɓi baƙuncin taron.   Ya ce: “Wannan babban cigaba ne ga Nijeriya kuma yana da alaƙa da manufofin gwamnatin mu na inganta martabar ƙasar a idon duniya. A daidai lokacin da muke aiwatar da muhimman sauye-sauye da ƙarfafa matsayar mu a duniya, karɓar baƙuncin WPRF wata alama ce cewa duniya tana kallon Nijeriya.   “Gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da nasarar wannan taro.”   Ya kuma bayyana wata muhimmiyar nasara, inda ya ce Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin Cibiyar UNESCO ta Mataki na Biyu kan Ilimin Kafofin Watsa...
    Ana sa ran shirin zai inganta samar da abinci, rage rikice-rikicen Makiyaya da Manoma, da kuma samar da damarmaki ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke dogaro da kiwo a matsayin sana’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, zuwa karshen watan Fabarairun shekarar nan ta 2025, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin, ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2272, adadin da ya karu da dalar Amurka biliyan 18.2, sama da na karshen watan Janairu, wato karuwar kaso 0.57 cikin dari. Wani jami’i mai aiki a hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai inganci, da fa’ida mai yawa, da juriya mai karfi, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka  wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da  Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...
    Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai. A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani. Alake ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta karfafa aikin hadin gwiwa a tsakaninta da gwamnatin jihohi a yankunan da ake hakar ma’adinai domin dakile ayyukan masu haka ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da cewa kasar na morar albartun da Allah ya huwace mata. Da yake magana kan takardar da ya gabatar a gaban majalisar, ministan ya ce takardar ta tsara yadda za a shawo kan...
    Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio. Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu “Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP. Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa....
    Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio. Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu “Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP. Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa....
    Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom. Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu. A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani a baya bayan nan, wadda ta shafi matakan kasar na shawo kan bazuwar sinadarai dangin fentanyl a kasar Sin.  Yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma’ar nan, kakakin ma’aikatar cinikayya ta Sin, ya ce takardar ta fiyyace daukacin matakai, da gabatarwa mai zurfi game da matsayar kasar Sin, da tasirin matakanta na shawo kan bazuwar sinadarai dangin fentanyl ga kasashen duniya. Gwamna Dauda Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Zamfara Da Sakatarori 12 Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara Ya ce takardar ta yi cikakken bayani game da yadda Amurka ta kakaba harajin...
    “NNPC na amfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje domin yin gogayya da matatar Dangote, a maimakon ta dukufa amfani da matatunta na mai da suke cikin kasar nan. Wannan lamarin na shafan dorewar musayar kasuwanci kuma zai kara janyo damuwowi ne kawai ga tattalin arzikin kasar nan,” Iledare ya shaida. Wani masanin makamashi kuma shugaban NES, Farfesa Adeola Adenikinju, ya ce akwai bukatar hukumomi su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da wadatar mai da kuma saukinsa a kasuwanni. Ya kuma lura da cewa akwai bukatar magance dakile gasar rashin adalci domin a samu yin ciniki sosai a tsakanin masu mai. Mataimakin shugaban IPMAN, Hammed Fashola, ya nuna farin ciki da rage farashin litar...
    A wani bincike mai kayatarwa da wani rukuni na masana kimiyya na kasar Sin ya gudanar, ya gano wasu tsare-tsaren gudanar da rayuwa, a muhallin halittu mafi zurfi cikin kwarin teku da ake cewa “Mariana Trench”. Wurin da ake ganin shi ne mafi zurfi a sassan tekunan duniyar nan. Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar “journal Cell”, cikin wasu takardun bincike 3, ya bayyana cewa, ta amfani da na’urar nutso a karkashin teku mallakin kasar Sin mai suna Fendouzhe, masu nazarin kimiyyar sun gano tsare-tsaren gudanar rayuwa na musamman, da ma albarkatun dake tattare da kananan halittu dake rayuwa a wurin mai tsananin zurfi, da halittu dangin kaguwa, da dangin kifaye dake wurin. Kazalika, sakamakon binciken ya baiwa bil...
    Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci ta Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi tofin Allah tsine da kashe Rabaran Fada Sylɓester Okechukwu na Gundumar Katolika da ke Kafanchan, inda ta jingina haka ga taɓarɓarewar harkokin tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da Shugaban SKCLA,  Dakta Emmanuel Nuhu Kure ya fitar a ranar Jumma’a ya miƙa ta’aziyyarsu ga Gundumar Katolika ta Kafanchan, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin. Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna “Wannan mummunar aiki babbar asara ce ga Coci da matuƙar tayar da hankali da damuwa game da ci gaba da kai hare-hare...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
    Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.” Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa. Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar...
    Ministar Harkokin Mata, Imaan Suleiman Ibrahim, ta yi alƙawarin sasanta Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida bayan kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a ya same ta da laifin karya dokokin majalisar. Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC Yayin da ta ke magana da manema labarai bayan taron bikin Ranar Mata ta Duniya, ministar ta bayyana takaicinta kan dakatarwar da aka yi wa Natasha. Ta ce, “Abin takaici ne kuma bai kamata ya faru ba. A majalisa ta baya, muna da mata Sanatoci guda tara, amma yanzu huɗu...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da matakan da suka wajaba na cimma nasarar tsare-tsare masu inganci, na bunkasa rundunar sojin kasar Sin na shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojin kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne a Juma’ar nan, yayin da yake halartar taron rukuni na tawagar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin PLA, da rundunar ‘yan sandan kasar, a wani bangare na taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    A yau Juma’ar farko ta watan Ramadan an kiyasta cewa adadin Falasdinawan da su ka halarci sallar juma’a  a masallacin Kudus, sun kai 90,000,duk da cewa sojojin HKI sun hana wasu falasdinawan masu yawa isa masallacin. “Yan sandan Sahayoniya sun rufe dukkanin hanyoyin da suke isa cikin masallacin, domin bincika takardun masu wucewa, saboda su hana samari da matasa majiya karfi shiga cikin masallacin.
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon fashewar wata tankar mai da ta tashi a Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata filayen noma a cikin unguwanni. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƙaramin Rami da ke ƙaramar hukumar Mashegu da misalin ƙarfe 6:30 na yamma. An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya afku ne lokacin da wata motar ɗaukar kaya ta yi yunƙurin kaucewa wasu munanan hanyoyi. Waɗanda fashewar ɗin ta rutsa da su sun haɗa da: Rafiatu Sahabi da Ramlat Shehu da Rashida Abdullahi da Raliya Abdulrahman...
    Hukumar da take yaki da yi wa tattalin arzikin kasar  Najeriya zagon kasa, ta yi wa tsohuwar ministar harkokin mata Uju Kennedy,tambayoyi masu alaka da zargin da ake yi mata akan aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da wasu kudade da sun kai Naira miliyan 138.4 a karkashin kasafin kudin ma’aikatar tata a 2023. Da safiyar jiya Alhamis da misali 11: na safe ne tsohuwar ministar ta isa babbar shalkwarar hukumar ta EFCC dake birnin Abuja,inda ta amsa tambayoyin da aka yi mata. Majiyar hukumar ta EFCC ta ce da akwai wasu kudade da aka bai wa ma’aikatar a karkashin shirin nan na p-Bat cares, amma sai aka karkata su zuwa asusun tsohuwar ministar. Uju tana cikin minsitocin da ...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata masu dogaro da Amurka su kwana da sanin cewa, haka makomarsu za ta kasance, domin haka halayyar girman kai take.” Haka nan kuma limamin na Tehran ya ce; tare da cewa jagoran juyin musulunci na Iran ya sha jaddada cewa, babu aiki da tunani a cikin tattaunawa da Amurka, kuma ba abu ne na girma ba, sai dai kuma da akwai wadanda ba su nuna...
    Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Damuwar IMF akan kalubalen tattalin arzikin Najeriya yaudara ne – Farfesa Yushau AngoWani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango, ya ce damuwar da asusun lamuni na duniya IMF ke yi kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu yaudara ce.   Farfesa Yushau Ango ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Kaduna. Ya kuma jaddada bukatar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF ta gabatar da shawarwari masu inganci don magance kalubalen da ke haifar da cire tallafin man fetur, wanda manufofinsa suka yi tasiri.   Masanin harkokin kudi ya bayyana raguwar farashin kayan abinci a matsayin na wucin gadi sai dai idan ba a samar wa manoman kasar...
    An Bukaci ‘yan fansho suyi gangami ganin jinkirin da ake samu wajen biyan su kudaden su. An shawarci kungiyar ’yan fansho ta tarayya da ta zaburar da mambobinta kan jinkirin rage basussukan da gwamnatin tarayya ta amince da su. Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ’yan fansho na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Alhaji Muhammad Mamman, ya bayar da wannan shawarar a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa an dakatar da zanga-zangar da ake shirin yi kan lamarin, biyo bayan rokon da PTAD ta yi na a ba da damar tattaunawa. Alhaji Muhammad Mamman wanda ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawa da wa’adin makonni hudu da hukumar NIPOST reshen kungiyar ‘yan fansho ta kasa ta bayar ya ba da shawarar...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna. An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar...
    Wasu alkaluma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN sun suna cewa, a 2024, Asusun ajiyar Nijeriya rufe ne a kan Dala biliyan 40.877. Wani masani a fannin tattalin arziki da ke da zama a jihar Legas Ibukun Omoyeni, a wani hasashe da ya yi kan shekarar 2025 ya bayyana cewa, Nijeriya ta fuskanci wasu bin ka’dojin yarjejeniyar karbar bashi, inda ya kara da cewa, baya ga batun kafin a shiga shekarar 2026, akwai wasu basussuka na waje Nijeriya ta ciwo wandanda kuma, ba su riga sun gama nuna ba, wanda akalla zai iya kai wa Dala biliyan 1.33 a duk shekara ko kuma sama da haka wadanda suka hada da biyan kudin ruwa na rancen, inda mai yuwa,...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi kira ga masu dafa abincin buda baki a karamar hukumar Kafin Hausa da su kasance masu gaskiya da adalci wajen ciyar da masu azumi a wannan watan na Ramadan. Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Abdulkadir Bala T.O yayi wannan kiran yayin da yake duba cibiyoyin ciyar da masu azumi na Dan Modi a cikin garin Kafin Hausa. Alhaji Abdulkadir Bala T.O ya yaba da kokarin wasu daga cikin masu dafa abincin, yayin da ya nuna rashin jin daɗi kan yadda wasu suka karya yarjejeniyar da aka gindaya masu. A nasa jawabin, Shugaban karamar hukumar Kafin Hausa, Alhaji Abdullahi Sa’idu Nalayi, ya tabbatar da cewar, Karamar hukumar za ta...
    Bugu da kari,a kasuwar an yi hada-hadar Naira kan 1,960, inda kuma Fam na kasar Birtaniya, ya fadi, wanda aka sayar kan Fam 1, sabanin a kwana daya da aka sayar da Naira kan 1,950 aka kuma sayar da Fam kan, Fam 1. Hakazalika, Dalar Kanada, ta yi asara a kasuwar, inda aka sayar da Naira kan 1,200, aka kuma sayar da ta kan CA1, sabanin yadda a kwana daya aka sayar da Naira kan 1,150, aka kuma sayar da CA kan CA1. An yi hada-hadar Naira, kan Naira 5, sabanin takardar Euro da aka yi hada-hadarta kan Naira 1,590, inda takardar ta Euro aka sayar da ita, kan Euro 1, sabanin kwana daya baya, da aka sayar da Naira...
    Bayan da Amurka ta sanar da sanya karin haraji, kasashen Canada da Mexico da ma Sin dukkan sun dauki matakan ramuwar gayya. A ranar 4 ga wata, bi da bi ne ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ma kwamitin kula da dokokin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar sun sanar da jerin matakai na tinkarar matakan haraji na Amurka. Kakakin ma’aikatar wajen kasar Sin ya kuma jaddada cewa, nuna fin karfi ba shi da amfani da kasar Sin, kuma matsawa da barazana ba hanya ce ta cudanya da kasar. Hakikanin abubuwan da suka faru a shekarun baya ma sun shaida yadda kasar Sin ke mai da matsawa da aka yi mata a matsayin karfin da ke sa ci gabanta, bisa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A lokacin ganawar ta su, Dantsoho ya shedawa Daraktar yin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ta Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa. Da take mayar da jawabi Daraktar Janar ta Cibiyar ta bayyana tawagar ta NPA shawarar ta kan yadda za a kara inganta ayyukan NPA, musamman a bangaren samar da saukin yin kasuwanci, domin a kara habaka gasar yin kasuwanci da kuma kara tara kudaden shiga. Kazalika, Hukumomin biyu, sun bayyana fatan kan hadakar a tsakaninsu, domin a samar da sauye-sauyen da a za su samar da sakamako mai kyau. Hukumar ta NPA, ita ce aka dorawa nauyin tafiyarwa da kuma tafiyar da ayyukan Tashoshin Jirgen Ruwan Kasar. Ana sa ran wannan hadakar a tsakanin NPA da PEBEC, za...
    Majalisar Wakilai na shirin kafa wata sabuwar hukuma da za ta karɓi ikon yin rajistar jam’iyyun siyasa daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta gabatar da wani sabon ƙudiri kan batun. Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, tare da Hon. Marcus Onobun daga Jihar Edo ne, suka gabatar da ƙudirin. Ƙudirin na neman kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta riƙa yi wa jam’iyyu rajista, kula da dokokinsu, da kuma tallafa musu. Har ila yau, ƙudirin na neman a kafa wata kotu ta musamman da za ta duba ƙorafe-ƙorafen da...
    Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu. Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci...
    Ya zama wajibi a tarihance cewa, a duk sa’adda aka tasamma furta asalin samuwar kunshin “yan majalisun taraiya a wannan kasa, a faro daga Jihar Legas, wadda ake yi wa take da “cunkus dakin tsumma, makarinki sai an dawo”. Kasantuwar, daga can ne suka samo asali. Mai karatu ya fahimta cewa, wannan rubutu da alama zai ja zarensa ne har zuwa wani lokaci, cikin gabatar da mabanbantan bayanai game da “yan majalisunmu na Kasa, hada da na jihohi. Fede irin karfin iko da tsarin mulkin Kasa ya ba su, tare da yin jinjina ga wasu cikin cokali daga cikinsu, sai kuma fyadar “ya”yan kadanya ga asarinsu, duba da irin burus da suka yi da kwamacalar shugabanni (shugaban kasa da gwamnoni)...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci. An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu. Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan. Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba. Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za...
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    Yansanda a birnin Lagos na kudancin kasar sun kama wasu yan kasar Pakistan biyu wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin aikin kamawa don neman kudaden fansa daga hannun wani dan kasar ta Pakistan dan shekara 48 a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran sun nakalto daga kafafen yada labaran kasar wadanda suka ji kakakin yansan na jihar Lagos Chief Superintendent Benjamin Hundeyin yana cewa, yan kasar Pakisatn da suka kama a wani dauki da suka wanda aka sace don neman kudaden fansa sun kama a ranar 5 ga watan maris akwia Roman Gull dan shekara 19 da kuma Aftab Ahmed dan shekarera 28 a duniya kuma yan asalin kasar Pakistan ne, wadanda suka hada kansu da wasu...
    Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...
    An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar. Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a. SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a. Ta kuma kara da cewa. a bakin ruwan garin Jabbeh kusa da lardin lardin lantaki mutane 48 aka kashe. Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a...
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan. Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto Stephane Dujarric kakakin babban sakataren MDD yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, wakilan Majalisar a yankun sun bada rahoton yadda sojojin HKI suka kutsa a cikin sansanin yan gudun hijira na al-Arroub wanda yake cikin yankin Shuyukh al-Arrub, inda suka daki wani matsayi da kasar bindiga har suka fasa masa bakinsa suka kuma karya masa kafa. Har’ila yau rahoton ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da...
    LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa. Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe. A makon da ya gabata, jaridar ta ce ta kara samun wani matsayi na musamman a bikin na bana, wanda kuma ke bikin cika shekaru 20 da kafa kamfanin, ta hanyar baje kolin abin da ke tafe a jaridar Financial Times, babbar jaridar kasuwanci da hada-hadar kudi ta duniya. Gangamin wanda aka fara a makon farko na watan Fabrairu, zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Maris, wanda...
    Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada. A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”...