2025-04-01@11:18:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6
«yawon bude ido»:
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmaanci. Kamfanin dillancin labarum “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunis ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Lrabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude...
Bisa ga yadda wasu fina-finan kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa, ciki har da fim din “Ne Zha 2”, a yau Litinin an kaddamar da bikin “Tafiya a kasar Sin bisa fina-finan kasar” a gidan tarihi na fina-finai na kasar Sin dake nan birnin Beijing, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) suka shirya, kuma gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin (CGTN) da cibiyar shirye-shirye ta tashar fina-finai suka karbi bakuncinsa. Bikin wanda ya fi mayar da hankali kan gudanar da ayyukan tallata fina-finai da yawon shakatawa ta hanyar nuna fina-finan kasar Sin a ketare, da shirya bikin nune-nunen fina-finan kasar...
Wani kifi jinsin Shark da mamallakin Kamfanin Airbnb da ya shahara a duniya mai tsawon kafa 25 ya fusata, inda ya fito daga rufin gidan da yake saboda matakin da aka ɗauka na tilasta rufe gidan da aka ajiye shi. Mamallakin Kamfanin wanda yake mazaunin Birtaniya ne, mai suna Dakta Magnus Hanson-Heine ya rasa wani shirin neman alfarma daga Karamar Hukumar Oxford na hana shi amfani da wurin zama na ɗan gajeren lokaci na cikin kadarorinsa da aka fi sani da Shark House (wato inda yake kiwon kifin). Mazabar Tsanyawa/Kunchi ta shafe shekara guda ba tare da wakilci ba Yadda za a yaƙi talauci a Arewa maso Gabas — Shettima Ya yi iƙirarin cewa bai samu ƙorafi ko ɗaya daga...
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take. Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro. Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai DSP Buhari ya kara da cewa rundunar za...
Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis. Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, kakaba karin haraji da Amurka ta yi ita kadai, ta yi matukar saba wa ka’idojin kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO, wanda ke nuni baro-baro a fili da ra’ayi na kashin kai da gicciye kariyar ciniki. Don haka, a cewar jami’ar ma’aikatar, yunkurin na Amurka ya yi matukar kawo cikas ga tsarin gudanar da ciniki a tsakanin bangarori daban-daban,...