2025-02-20@09:12:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6

«Ƙaramar Hukumar»:

    Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani  da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina. Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana. Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar. Wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa...
    Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa idan ba tare da cikakken tantance kudi ba, babban bankin ba zai iya bude sabbin asusu ga kananan hukumomin ba.
    Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar. Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su. Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba...
    Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, inda ake fuskantar ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma zargin sayen ƙuri’u a wasu rumfunan zabe. Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da NSCDC, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga tare da tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro. A garin Tsani, rahotanni sun nuna cewa mutum biyu kacal aka gani a rumfar zabe, yayin da aka hango motar sintiri da APC na jami’an tsaro. Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga A rumfar Birchi ta Kudu, inda aka yi rajistar masu zabe 808, kaɗan daga cikinsu ne...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
    Kazalika gwamnan ya amince da naɗa Sunday Alex daga Ƙaramar Hukumar Bassa, da Joyce Ramnap daga Langtang ta Kudu, da Sylvanus Dongtoe daga Shendam, da kuma Nicholas Baamlong daga Qua’an Pam, sai Cornelius Doeyok daga Ƙaramar Hukumar Qua’an domin maye gurbin waɗanda ya sallama.   Idan ba a manta ba a baya ma gwamnan ya dakatar da Dawam da Jamila na watanni uku bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba, wanda a yanzu majiyoyi ke cewa sallmar tasu na da alaƙa da rashin aiki yadda ya kamata a shekarar da ta gabata.   Wannan ya janyo cece-kuce a cikin harkokin siyasa, inda masana ke hasashen yiwuwar sauya wasu mukamai da kuma tasirin sauyin a harkokin gwamnati.
۱