2025-04-19@07:12:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12

«a rayuwarsu»:

    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
    Rasuwar Sheikh Dakta Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi rasuwa ce da ta jijjiga al’ummar Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare, bisa la’akari da irin faɗakarwarsa da karantarwarsa da gwagwarmayarsa. Hakan ya jawo dandazon al’ummar Musulmi suka halarci sallar jana’izarsa kuma fitattun mutane da malamai suka yi ta yin ta’aziyyar rasuwarsa. Lokacin da Malamin yake raye kusan a kulum sai ya gabatar da huɗuba ko darasi na wayar da kan al’umma ko kuma ilmantar da su kan wani abu mai muhimmanci a masallacinsa da makarantarsa. A ’yan shekarun nan Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya, wanda a sanadiyyar haka ya xauki tsawon lokaci ba a ji huɗubarsa ko karantarwarsa ba da suke xaukar hankalin dubban masu sauraro a faɗin Afirka, lamarin...
    Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi. Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    “Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona. A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar. Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda...
۱