2025-03-25@21:28:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9

«shiga Kannywood»:

    Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
    Masana’antar Kannywood ta dade tana nishaɗantar da al’umma, musamman Hausawa da sauran kabilun Arewacin Najeriya. A makon jiya Aminiya ta ruwaito a cewa kasuwancin fina-finan ya samu koma-baya matuƙa, wanda hakan ya sa wasu suke nuna yatsa ga furodusohin yanzu kan gaza shirya fim ɗin da za a iya haskawa a Netflix da sauran manyan hanyoyin nuna fina-finai da za su samar wa masana’antar kuɗin shiga. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza Wannan ya sa Aminiya ta yi waiwayen wasu furodusohin da aka daina jin ɗuriyarsu a masana’antar. Salisu Galadanchi – Shi ne Daraktan Fim din Turmin Danya, fim na farko a Kannywood, ya...
    Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma don neman daukaka ya kara da cewa. A ci gaba da hirar Sadik ya amsa tambayar da aka yi mashi a kan fina-finan da yayi da kuma wadanda yake kallo a matsayin wanda yafi so a cikinsu, inda ya ce daga cikin fina-finan da ya fito wadanda kuma yafi so, akwai Mati Da Lado sai kuma wani fim mai suna Dan Marayan Zaki. Abinda ya...
    Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...
    Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai muka tuna da fim dinsu na Badakala (wanda wani jarumi Bashir Mudi Yakasai ya shirya), inda suka yi fim mai dauke da rawa da waka na farko a cikin fina-finan Hausa,wato a shekarar 1997 wannan fim ya daga abinda yanzu ake kira Hausa Afropop, domin shi ne wakar fina-finan Hausa ta farko da aka kai wa Rabi’u BK a kasuwar Kofar Wambai domin sayar da...
    Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai. “Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa...
    A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar. Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina; na daga cikin fina-finan da ke kan gaba a ‘YouTube’, harkokin fina-finan Kannywood, sun koma wannan kafar ne; tun bayan da tattalin arzikin masana’antar ya tabarbare sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa ‘YouTube’ din zai inganta kasuwancin masana’antar kamar yadda yake a baya. An dade ana shirya fina-finan Hausa masu dogon zango, amma fim din Izzar So, na Lawan Ahmad; na cikin wadanda...
    A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam. “Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan...
    Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba. Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu. A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a...
۱