2025-04-16@15:57:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 710
«ya kammala karatu»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau. Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin wasannin gargajiya na wannan yankin na Afirka. Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen shekara. Janar...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...