2025-04-12@21:31:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 13
«da ya ɓace»:
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace. Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan. Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin. Sai dai a baya, Danjuma Auta,...
Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda ‘yansandan Nijeriya ke amfani da dokar leken asiri ta yanar gizo ba ta yadda ya dace ba. Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci Sun zargi ‘yansanda da yin amfani da dokar aikata laifuka ta yanar gizo wajen kai hari ga masu fafutukar kare hakkin...
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas. Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun. Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas. Kwankwaso ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa doka kuma barazana ne ga dimokuraɗiyya. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Kwankwaso ya gargaɗi cewa irin wannan matakin na iya kafa mummunan misali da kuma illata dimokuraɗiyya a Najeriya. Kwankwaso, ya ruwaito yadda rikicin siyasa da ya haifar da soke zaɓen 1993, inda ya jaddada cewa ‘yan majalisa su daina ɓata lokacinsu kan abubuwan da ba su dace ba. “Majalisa tana...
Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas? Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar. Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar. Tun bayan ɗaukar wannan mataki,...
Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Similanayi Fubara, ya fice Fadar Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal. Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Fubara ya fice daga Fadar Gwamnatin da safiyar Laraba, a daidai lokacin da sabon Shugaban Riƙn Ƙwarya, Admiral Ekwe Ibas (mai ritaya), ke shirin karɓar ragamar mulki. Ɗan Afirka da yake da ‘ya’ya 104 da jikoki 144 Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Wakilin Aminiya ya ziyarci Fadar Gwamnatin, inda ya lura cewa akwai kwanciyar hankali a yankin, inda aka girke motocin yaƙi guda uku a kofar shiga gidan gwamnatin. Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa an sauya dukkanin jami’an tsaron da ke aiki a Fadar Gwamnatin Jihar. “Gwamna ya fice daga ciki,...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar. ‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’ Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya...
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta soki matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci da kuma cire Gwamna Similanayi Fubara na Jihar Ribas. Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasar ba shi da ikon tsige zaɓaɓɓen gwamna bayan ayyana dokar-ta ɓaci a jiharsa. An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau “Saboda haka duk wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin dimokuraɗiyya wanda kuma ya keta haddin cin gashin kan gwamnatocin jihohi,” in ji shi. A kan haka ne Ƙungiyar Lauyoyin ta buƙaci Majalisar Dokoki ta...
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000. A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram. A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro. Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya. Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’. Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993. “Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin...
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis. Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace. Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235)...