2025-02-21@14:22:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1113
«Rundunar Tsaron Kano»:
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba. Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu. Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA...
daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga. “A baya...
Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu. Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar. An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida...
Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhafa barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masi muhimmanci a wannan makon wadanda suka hada da wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro na sauransu, da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu...
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan...

Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta...
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta...
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar. Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin...

Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar...
Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya....
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta nesanta hannunsa da kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch, Dele Giwa. An kashe Dele Giwa wanda fitaccen mai sukar gwamnatin Babangida ne, ta hanyar wasikar bom a gidansa da ke Legas a ranar 19 ga watan Oktoban 1986. Kwana biyu kafin...
Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe. “Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,”...
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...

Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma. Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance...
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da...
Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya, wato Muslim Charity For United Kingdom a turance. Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon ilimi na zamani, da sauransu. A cewar daraktan...
An Bude Cibiyar Horar Da Malaman Harshen Sinanci A Ghana
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da shirin Da’awah na mata a hukumance, domin karfafawa mata ilimin addinin musulunci, da karfafa alakar iyali, da kyautata rayuwa a tsakanin. Da yake jawabi a wajen bikin a Dutse, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tsara tarbiyar al’umma da kyawawan dabi’u....
Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi. Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga...
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin...
Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da...
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man. “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma...
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai...
Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar. Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP,...
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha,...
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza. Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito. Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin...
Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya...
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar...
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan...
Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu. Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. NNPP ta rasa Ɗan Majalisa...
Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta...
Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993. Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban. Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara...
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga...
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
“Wannan mataki yana cikin shirin Hisbah na tabbatar da cewa al’ummar Katsina na tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u,” in ji shi.
Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram. An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis. ’Yan bindiga sun...
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6...