2025-04-02@13:04:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 17

«tsadar rayuwa»:

    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    “Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    A wani bincike mai kayatarwa da wani rukuni na masana kimiyya na kasar Sin ya gudanar, ya gano wasu tsare-tsaren gudanar da rayuwa, a muhallin halittu mafi zurfi cikin kwarin teku da ake cewa “Mariana Trench”. Wurin da ake ganin shi ne mafi zurfi a sassan tekunan duniyar nan. Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar “journal Cell”, cikin wasu takardun bincike 3, ya bayyana cewa, ta amfani da na’urar nutso a karkashin teku mallakin kasar Sin mai suna Fendouzhe, masu nazarin kimiyyar sun gano tsare-tsaren gudanar rayuwa na musamman, da ma albarkatun dake tattare da kananan halittu dake rayuwa a wurin mai tsananin zurfi, da halittu dangin kaguwa, da dangin kifaye dake wurin. Kazalika, sakamakon binciken ya baiwa bil...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu. Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin gargajiya na kasar na okara granola a intanet, kwanan nan hankali ya koma kansa. Ya rasu a yayin buɗa-baki a Abuja Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna A ranar 8 ga Yuli, ya sanar a shafin sa na sada zumunta na kafar X cewa, matarsa Seira za ta dawo gida bayan ta shafe wata shida tana karatu a kasashen waje kuma za...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa uku daga cikin matan da suka rasu ’yan gida ɗaya ne. Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sai dai wasu fasinjoji uku da suka haɗa da mata biyu da direban motar sun tsallake rijiya da baya, inda a yanzu suke samun kulawa a Babban Asibitin Lapai. Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Gwamna Umar Namadi  ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da  hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa,  ana sa ran ...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu. Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar. Bugu da kari Masar din ta sanar...
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona. A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar. Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda...
۱