2025-04-01@02:54:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 115

«gwamnatin wariya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
    Alkaluma daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin sun nuna cewa, kudin shigar kamfanoni mallakin gwamnatin Sin ya karu da kaso 1.3 a shekarar 2024. A cewar ma’aikatar, kamfanonin sun samu karuwar yuan triliyan 84.72, kwatankwacin dala triliyan 11.7 na kudin shiga a 2024. Jimilar ribar da suka samu a shekarar 2024 kuma, ta karu da kaso 0.4 zuwa triliyan 4.35 a kan na shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.” Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba. Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.” Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza.  Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba. A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin amaryar. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya Ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’idar Musulunci kuma ba za a yarda da irin wannan lamarin ya ci gaba da faruwa a Kano ba. “Muna sanar da cewa mun kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don kama abokansu da duk wanda...
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Kungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta tabbatar da ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar a hukumance. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS ɗin ta fitar, tana mai cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ga waɗannan ƙasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake komawa. Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce za a ci gaba da mutunta fasfon jama’ar waɗannan ƙasashen uku da ke ɗauke da tambarin ECOWAS, haɗi da katinsu na shaidar ɗan kasa. Kazalika, ƙungiyar ta ce za a ci gaba da kallon waɗannan ƙasashe tamkar mambobinta,...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
    Rundunar ƴansandan Abuja, ta bayyana cewa rashin samun labarin lamarin da wuri ne ya kawo jinkirin ɗaukar mataki. Mun Fara Bincike – Ƴansanda Kakakin rundunar ƴansandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni suka fara bincike domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. Ta ce: “Ƙarfe 1 na dare muka samu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga sun kai hari Chikakore. Nan take muka tura ƴansanda zuwa yankin. Bincike ya nuna cewa maharan guda bakwai ne, sun yaudari mai gidan har ya buɗe musu ƙofa.” Ta kuma ce wata maƙwabciyarsu da ta yi ƙoƙarin taimaka musu ta ji rauni, kuma tana karɓar magani a asibiti. Rundunar ta buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare...
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
      Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa.   Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin.   A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa.   Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje.   Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...