2025-02-23@13:10:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8
«Dokar Kare Hakkin Yara ta»:
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa. Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin....
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa. Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan. Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan. Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto ‘yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil’adama bisa nasarar ceto yaran. Ya ci gaba da cewa ta’addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis. Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...